Dangote ya zuba Dala miliyan 800 don ƙarfafa kamfanin simintinsa na Ogun

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanin Dangote ya rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna ta Dala miliyan 800 da kamfanin Sinoma International Engineering Company Limited na ƙasar Chana, domin faɗaɗa matatar simintinsa da ke Itori a Jihar Ogun daga ƙarfin samar da tan miliyan shida zuwa tan miliyan 12 a shekara.

Ana sa ran wannan shiri zai ƙara ƙarfin Nijeriya wajen fitar da siminti zuwa ƙasashen waje tare da ƙarfafa matsayinta a matsayin ƙasa mafi girma wajen samar da siminti a nahiyar Afirka.

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, da Shugaban Kamfanin Sinoma, Lin Zhong, ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar, wadda ke nuna ci gaba da haɗin gwiwar da kamfanonin biyu suka daɗe suna yi wajen bunƙasa masana’antu a Afirka.

Ana sa ran faɗaɗa matatar zai ƙara ƙarfin samar da siminti na Kamfanin Dangote, wanda zai ba shi damar biyan buƙatar cikin gida da ke ƙaruwa, tare da faɗaɗa kasuwancinsa a ƙasashen Afirka da sauran sassan duniya ta hanyar ƙara fitar da siminti.

Da yake jawabi yayin bikin sanya hannu kan yarjejeniyar, Dangote ya bayyana cewa wannan jarin wani muhimmin ɓangare ne na dabarun bunƙasa kamfaninsa na dogon lokaci, kuma alama ce ta yadda yake da cikakken ƙwarin gwiwa kan tattalin arzikin Nijeriya.

Ya ce an yanke shawarar faɗaɗa matatar Itori ne sakamakon sabon salon da Gwamnatin Tarayya ke ɗauka na amfani da siminti wajen gina tituna, da kuma yadda buƙatar siminti ke ci gaba da ƙaruwa a kasuwannin Afirka.

Dangote ya ce, shirin kuma yana daga cikin manufofin Vision 2030 na Kamfanin Dangote Cement, wanda ke da burin samar da tsakanin tan miliyan 90 zuwa miliyan 100 na siminti a duk shekara.

A cewarsa, wannan faɗaɗawa za ta ƙara kuɗaɗen shiga na musayar kuɗaɗen ƙasashen waje da Nijeriya ke samu, ta samar da ayyukan yi ga dubban mutane, tare da ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce, “Wannan jarin dala miliyan 800 wani sabon gagarumin mataki ne na ƙarfafa masana’antun Nijeriya da kuma tabbatar da jagorancinmu a masana’antar siminti ta Afirka.”

Ya ƙara da cewa, faɗaɗa matatar daga tan miliyan shida zuwa miliyan 12 a shekara ba wai kawai zai biya buƙatar cikin gida ba ne, har ma zai ninka ƙarfin kamfanin wajen fitar da siminti zuwa ƙasashen waje, wanda zai ƙara wa Nijeriya kuɗaɗen shiga na musayar kuɗaɗen ƙasashen waje.

Dangote ya kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa samar da yanayin da ya dace ga masu zuba jari, yana mai cewa ƙoƙarin gwamnati wajen bunƙasa ababen more rayuwa ya ƙarfafa masu masana’antu su ci gaba da zuba jari a ƙasar.

Ya kuma yabawa Kamfanin Sinoma, yana mai cewa ya kasance amintaccen abokin hulɗa wajen gina matatun siminti na zamani a faɗin Afirka, tare da bayyana tabbacin cewa sabon aikin zai ƙara bunƙasa masana’antun Nijeriya.

A nasa jawabin, Shugaban Kamfanin Sinoma International Engineering Company Limited, Lin Zhong, ya ce yarjejeniyar wani sabon babban ci gaba ne a dangantakar da ke tsakanin kamfanonin biyu.

Ya ce faɗaɗa matatar zai ƙara wa Kamfanin simintin Dangote ƙarfin gogayya a kasuwa, tare da mayar da Nijeriya cibiyar samar da siminti da fitar da shi zuwa ƙasashen duniya.

Lin Zhong ya ce kamfaninsa zai yi amfani da ƙwarewar injiniyoyi, fasahohin zamani da gogewarsa ta duniya domin tabbatar da nasarar aikin, yana mai cewa wannan saka hannun jari wata alama ce ta yadda masu zuba jari na ƙasashen waje ke ci gaba da amincewa da ɓangaren masana’antun Nijeriya.

Da zarar an kammala aikin, ana sa ran matatar Itori za ta zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin samar da siminti da fitar da shi zuwa kasuwannin cikin gida da na ƙasashen waje, tare da taimakawa ƙoaarin bunƙasa masana’antu da kasuwancin Nijeriya a yankin Afirka

By ukarofi

Leave a Reply