Daga AISHA ASAS
*Shin suna shiga domin wakiltar muradun jama’a ko kansu?
A shekarun baya, sunayen fitattun jaruman Kannywood sun fi yawan bayyana ne a fagen fina-finai, waƙoƙi da nishaɗantar da jama’a. Kyamarori, hasken fage da kuɗin shirya fina-finai ne suka fi zama abubuwan da ake danganta su da wannan masana’anta.
Amma a yau, wannan hoton ya fara sauyawa. Wasu daga cikin fitattun jarumai, mawaƙa da masu shirya fina-finai sun koma wani babban dandali da za mu iya cewa saɓa wa sanannen abubuwan da suke fassara masana’antar, wato fagen siyasa.
Daga halartar gangamin jam’iyyu, zama masu taimaka wa ‘yan takara, riƙe mukamai a gwamnati, zuwa tsayawa takarar zaɓe, ‘yan Kannywood sun shiga siyasa ba tare da shakka ba. Abin da a baya ake kallonsa a matsayin wani abu na nesa da masana’antar fina-finai, yanzu ya zama wani muhimmin ɓangare na rayuwar wasu daga cikinsu.
Sai dai wannan sauyi ya haifar da tambayoyi masu yawa; me ya sa ‘yan Kannywood suka ƙara karkata zuwa siyasa? Shin shaharar da suka samu a masana’antar nishaɗi ce ta ba su damar shiga fagen mulki? Shin suna zuwa siyasa ne domin wakiltar muradun jama’a, ko kuma domin neman damar da za ta amfani rayuwarsu ta kansu?
Wannan shi ne babban abin da shafin Taurari na wannan makon zai tattauna kansa.
Kannywood ta kasance wata babbar hanya da ta ba wasu matasa damar samun suna da tasiri a tsakanin al’umma. Ta hanyar fina-finai da waƙoƙi, jarumai sun samu miliyoyin masoya waɗanda suke bin ayyukansu da kuma ra’ayoyinsu.
Wannan shahara ita ce ɗaya daga cikin abubuwan da suka sa siyasa ta fara kallon masana’antar a matsayin wani wuri mai muhimmanci wajen samun goyon bayan jama’a.
A siyasar zamani, sanin jama’a ya zama babban jari. ɗan siyasa ko jam’iyyar siyasa na buƙatar mutanen da za su iya isa ga zukatan jama’a cikin sauƙi. A nan ne wasu daga cikin ‘yan Kannywood suka samu kansu a matsayin mutane masu daraja a idon ‘yan siyasa.
Saboda haka, ba abin mamaki ba ne ganin yadda wasu jam’iyyu ke neman kusantar jarumai da mawaƙa domin amfani da tasirinsu wajen yaƙin neman zaɓe ko isar da saƙon siyasa.
Amma ga wasu ‘yan Kannywood, wannan ba wai kawai damar taimaka wa ‘yan siyasa ba ce; suna ganin siyasa a matsayin wata hanya ta shiga inda ake yanke hukuncin da ya shafi rayuwar jama’a.
Me ya sa suke komawa siyasa?
Dalilan da ke sa ‘yan Kannywood shiga siyasa sun bambanta daga mutum zuwa mutum.
Ga wasu, shiga siyasa wata dama ce ta amfani da shahararsu wajen kawo sauyi a cikin al’umma. Suna ganin cewa bayan shekaru suna sadar da saƙonni ta fina-finai da waƙoƙi, lokaci ya yi da za su shiga inda ake tsara manufofi da yanke shawara.
Wasu kuma suna ganin siyasa hanya ce ta samun damar yin aiki kai tsaye ga jama’a fiye da yadda masana’antar nishaɗi ke ba su dama.
A gefe guda kuma, akwai masu sukar wannan tafiya da ke ganin cewa wasu na shiga siyasa ne saboda damar da take tattare da ita; kamar samun mukami, kusanci da masu iko, ko kuma faɗaɗa matsayinsu na kuɗi da zamantakewa. Wannan kuwa shi ne wanda kaso mai yawa na jama’a suka yi amanna da shi. Hakan kuwa ba ƙaramin rage ƙimar fitattun mutanen suke yi ba ga masoyansu.
Wannan ne ya sa ake yawan tambayar ko shigar ‘yan Kannywood siyasa wata hidima ce ga jama’a ko kuma wata hanya ta biyan bukatun kansu?
A fagen siyasa, suna da tasiri wani babban makami ne. Dan siyasa na iya kashe kuɗi mai yawa wajen yaɗa saƙonsa, amma wani fitaccen jarumi ko mawaƙi na iya isa ga zukatan jama’a cikin ɗan lokaci saboda amincewar da ya riga ya samu daga masoya.
Wannan ne ya sa aka fara ganin kusancin da ke tsakanin ‘yan siyasa da ‘yan Kannywood yana ƙaruwa.
Jaruman fina-finai ba kawai masu nishaɗantar da jama’a ba ne; wasu daga cikinsu sun zama mutane masu tasiri da ke iya sauya ra’ayin magoya bayansu. Kalmar da wani shahararren jarumi ya faɗa, hoton da ya ɗora, ko goyon bayan da ya nuna wa wani ɗan takara na iya samun tasiri a tsakanin dubban ko miliyoyin masu bibiyarsa.
A nan ne wasu masana siyasa ke ganin cewa shigar ‘yan Kannywood cikin harkokin siyasa ba wani sabon abu ba ne, domin a tsarin dimokuraɗiyya, duk wanda yake da tasiri a cikin al’umma na iya amfani da wannan tasiri wajen shiga harkokin mulki.
Sai dai tambayar da ta rage ita ce: shin wannan tasirin ana amfani da shi ne domin ciyar da jama’a gaba, ko kuma kawai domin taimaka wa wasu ‘yan siyasa samun nasara?
Arewacin Najeriya, musamman yankin da ake magana da Hausa, Kannywood tana da matuƙar tasiri. Fina-finanta, waƙoƙinta da jarumanta sun shiga gidajen jama’a har ma da ƙauyuka inda wasu kafafen yaɗa labarai ba sa samun irin wannan kusanci.
Saboda haka, wasu ‘yan siyasa suna ganin jaruman Kannywood a matsayin wata gada da za ta haɗa su da jama’a kai tsaye.
A lokutan yaƙin neman zaɓe, ana iya ganin fitattun jarumai suna bayyana a wuraren tarukan siyasa, suna yin waƙoƙin kamfen, suna tallata manufofin jam’iyyu ko kuma bayyana goyon bayansu ga wani ɗan takara.
Ga wasu, wannan wata hanya ce ta amfani da fasaha wajen wayar da kan jama’a. Suna ganin kamar yadda ake amfani da mawaƙa ko masu wasan kwaikwayo wajen isar da saƙonni kan lafiya, ilimi ko zaman lafiya, haka za a iya amfani da su wajen isar da saƙonnin siyasa.
Amma masu suka suna tambayar ko wannan rawar ba ta mayar da wasu daga cikin jaruman zuwa kayan yaƙin neman zaɓe kawai ba?
Baya ga tallafa wa ‘yan takara, wasu daga cikin ‘yan Kannywood sun yanke shawarar shiga siyasar kai tsaye. Sun bar matsayin masu goyon baya suka koma masu neman mukami ko masu riƙe da ofisoshi a gwamnati.
Wannan sauyi ya nuna cewa masana’antar ba ta tsaya a matsayin wurin nishaɗi kawai ba; ta zama wata hanya da wasu ke amfani da ita wajen gina tasirin da zai iya kai mutum zuwa fagen mulki.
Ga wasu jarumai, shigar siyasa wani mataki ne na amfani da farin jini wajen yin abin da suka yi imanin zai amfani jama’a. Suna cewa kasancewarsu a cikin gwamnati ko kusa da masu yanke shawara zai ba su damar magance matsalolin da suke ganin sun shafi al’umma.
Misali, wani jarumi da ya shahara a fina-finai na iya amfani da muryarsa wajen magana kan matsalar tsaro, talauci, rashin aikin yi, ilimi ko matsalolin matasa. Abin da ake tambaya shi ne: shin bayan magana, akwai wani aiki da aka yi domin magance matsalar?
A nan ne bambanci yake tsakanin amfani da suna kawai wajen samun karɓuwa da kuma amfani da suna wajen kawo sauyi.
ɗaya daga cikin manyan muhawarorin da ke tattare da shigar ‘yan Kannywood siyasa ita ce ko manufarsu ita ce hidimar jama’a ko kuma neman anfani na kansu.
Masu goyon bayan wannan tafiya suna cewa bai kamata a hana wani ɗan ƙasa amfani da basirarsa ko shahararsa wajen shiga siyasa ba. A ganinsu, idan mutum yana da ilimi, hangen nesa da sha’awar yi wa jama’a hidima, sana’ar da ya fito daga ciki ba ta hana shi zama shugaba nagari.
A gefe guda kuma, masu suka suna cewa wasu lokuta shaharar mutum ba ta nufin yana da kwarewar jagoranci ko fahimtar matsalolin mulki.
Suna tambayar ko kasancewa fitaccen jarumi ya isa mutum ya zama mai iya tsara manufofi, kula da albarkatun jama’a ko warware matsalolin da suka shafi al’umma.
Wannan muhawara ba ta shafi Kannywood kaɗai ba; a duniya akwai mawaƙa, ‘yan wasa da fitattun mutane daga masana’antar nishaɗi da suka shiga siyasa. Amma abin da ke tantance darajarsu shi ne abin da suka iya yi bayan sun samu dama.
Lokacin da murya ta zama wakilci: Shin ‘yan Kannywood suna isar da koken al’umma ne?
ɗaya daga cikin manyan dalilan da wasu ‘yan Kannywood ke bayarwa na shiga siyasa shi ne cewa suna son amfani da damar da suka samu wajen zama muryar waɗanda ba sa samun damar bayyana damuwarsu.
A matsayinsu na mutane da suka yi suna a cikin al’umma, wasu daga cikinsu suna ganin cewa sun fi kusa da jama’a fiye da wasu masu riƙe da muƙaman siyasa. Sun san matsalolin da mutane ke fuskanta saboda sun shafe shekaru suna mu’amala da jama’a ta hanyar fina-finai, waƙoƙi da kafafen sada zumunta.
Wasu na amfani da wannan matsayi wajen magana kan matsalolin matasa, rashin aikin yi, tsadar rayuwa, ilimi, ko kuma matsalolin da suka shafi masana’antar nishaɗi kanta, da uwa uba matsalar tsaro da ta adabe Najeriya, musamman yankin Arewa.
A wasu lokuta, ana ganin yadda fitattun mutane ke amfani da shafukansu na sada zumunta wajen jawo hankalin gwamnati ko masu ruwa da tsaki kan wani batu da ya shafi jama’a.
Wannan ya nuna cewa tasirin da suka samu daga Kannywood ba lallai ne ya tsaya a kan nishaɗi kawai ba; yana iya zama wata hanya ta isar da saƙo ga waɗanda ke da ikon ɗaukar mataki.
Sai dai akwai tambayar da ke ci gaba da jan hankali: shin yin magana kawai ya isa, ko kuwa ana buƙatar a ga sakamakon wannan magana?
Domin a siyasance, darajar wakili ba ta tsaya ne kawai a iya magana ba; tana cikin iya sauya magana zuwa aiki.
A duk lokacin da wani fitaccen jarumi ya shiga siyasa, ana samun manyan tsammani daga magoya bayansa. Mutanen da suka saba ganinsa a matsayin gwarzo a fina-finai kan yi fatan zai zama gwarzo a rayuwa ta zahiri.
Amma siyasa ba ta da sauƙi kamar yadda ake nuna labari a fim.
A cikin masana’antar fina-finai, jarumi na iya warware matsala cikin sa’o’i biyu na fim. Amma a rayuwar siyasa, matsaloli na buƙatar tsari, lokaci, haɗin gwiwa da kuma ikon yanke shawara.
Wannan ne ya sa wasu ‘yan Kannywood da suka shiga siyasa suka fuskanci suka daga wasu magoya bayansu. Wasu na cewa shaharar da suka samu a fina-finai ba ta wadatar da su wajen magance matsalolin al’umma.
Wasu kuma suna ganin ya kamata a ba su dama domin su nuna abin da za su iya yi, domin siyasa ba ta bambanta da sauran fannoni ba; kwarewa tana zuwa ne da lokaci da gogewa.
Shin siyasa ta amfanar da Kannywood?
Baya ga tambayar ko ‘yan Kannywood sun amfanar da siyasa, akwai wata tambaya mai muhimmanci: shin siyasa ta amfanar da Kannywood?
Wasu na ganin shiga siyasa ya ba masana’antar damar samun ƙarin kulawa daga gwamnati da masu ruwa da tsaki.
A baya, Kannywood ta sha fuskantar matsaloli da suka haɗa da rashin isasshen jari, ƙarancin tsare-tsare, matsalolin dokoki da kuma rashin cikakken tsarin tallafa wa masana’antar.
Saboda haka, wasu na ganin cewa kasancewar mutanen masana’antar a cikin harkokin gwamnati na iya zama wata dama ta tunkarar waɗannan matsaloli daga ciki.
Amma akwai masu ganin cewa kusancin da ake samu da siyasa wani lokaci na iya kawo barazana ga ‘yancin masana’antar.
A ganinsu, idan masu shirya fina-finai ko jarumai suka yi kusanci sosai da wasu ɓangarorin siyasa, hakan na iya sa a samu tsoron cewa wasu batutuwa ba za a iya magana a kansu cikin ‘yanci ba saboda la’akari da muradun siyasa.
Babban abin da ya bambanta shahararren mutum da talaka a siyasa shi ne tasirin da yake da shi tun kafin ya shiga. Amma wannan tasiri yana zuwa da wani nauyi.
Idan jarumi ya yi amfani da farin jininsa wajen neman kuɗi, matsayi ko kariya kawai, jama’a na iya kallon hakan a matsayin cin moriyar suna da ya samu.
Amma idan ya yi amfani da wannan damar wajen tallafa wa jama’a, magana kan matsalolinsu, da kuma neman mafita, zai iya zama misali na yadda shahara za ta iya zama kayan ci gaban al’umma.
Saboda haka, ba shigarsu siyasa kaɗai ce ke da muhimmanci ba; abin da ya fi muhimmanci shi ne abin da suke yi bayan sun shiga.
Za mu ci gaba.
