“Tun tana ƙaramar idan ana zaluntar wani yaro, takan shiga tsakani tana faɗin ta ɗauki faɗan a kanta”
Daga AISHA ASAS
A duk lokacin da ake magana kan gwagwarmayar mata a Arewacin Najeriya, akan ambaci sunaye da dama. Amma akwai suna guda da ya tsaya daban, saboda ba a gina shi da mulki ko arziki ba, sai da sadaukarwa, ƙalubale da kuma jajircewar da ba ta san ja da baya ba. Wannan suna shi ne na Hajiya Gambo Sawaba.
A wani zamani da aka ɗauki siyasa a matsayin fagen maza, kuma aka ɗora wa mata nauyin zama masu sauraro kawai, Gambo Sawaba ta fito ta rusa wannan tunani. Ta yi magana lokacin da wasu suka zaɓi yin shiru, ta tsaya kan abin da ta yi aminta da shi lokacin da hakan ke iya kai ta gidan yari, kuma ta ci gaba da gwagwarmaya duk da cin zarafi, matsin lamba da tsare-tsaren da aka yi mata domin a raunana ta. Duk da haka, ba ta daina fafutukar ganin mace ta samu ilimi, ta shiga siyasa, ta yi zaɓe kuma ta kasance cikakkiyar ‘yar ƙasa ba.
Shekaru da dama bayan rasuwarta, ana ci gaba da ambaton Gambo Sawaba a matsayin ɗaya daga cikin fitattun matan da suka shimfiɗa tubalin gwagwarmayar ‘yancin mata a Arewacin Najeriya. Tarihinta ya nuna cewa sauyi ba ya zuwa cikin sauƙi; sau da yawa yana neman wanda zai yarda ya ɗauki wahala domin wasu su amfana a nan gaba.
Shin wace ce Hajiya Gambo Sawaba?
An haifi Hajiya Gambo Sawaba, wadda aka sa wa suna Hajaratu Amarteifio, a ranar 15 ga Fabrairu, 1933. Mahaifinta, Isa Amarteifio, ɗan asalin Ghana ne da ya zo Najeriya aiki a Hukumar Jiragen ƙasa, inda daga bisani ya karɓi Musulunci. Mahaifiyarta kuma, Fatima, ‘yar ƙabilar Nupe ce daga yankin da yanzu yake cikin Jihar Neja. A al’adar Hausawa, an raɗa mata suna “Gambo” saboda an haife ta bayan haihuwar tagwaye.
Ta taso ne a Sabon Gari da ke Zariya cikin rayuwar da ba ta cika da walwala ba. Duk da cewa ta fara karatun firamare a makarantar Natiɓe Authority da ke Tudun Wada, mutuwar mahaifinta tana da shekara goma, sannan rasuwar mahaifiyarta bayan shekaru uku, suka katse karatunta tare da sauya alƙiblar rayuwarta. A cikin ƙanƙanin lokaci ta tsinci kanta tana fuskantar nauyin rayuwa tun tana yarinya.
Tun tana ƙaramar yarinya, an ce idan ta ga ana zaluntar wani yaro, ba ta wuceww ta yi shiru. Maimakon haka, takan shiga tsakani tana faɗin cewa ta ɗauki wannan faɗa a kanta, sannan ta tsaya ta kare wanda ake zalunta. Wannan hali na ƙin amincewa da zalunci ya kasance tare da ita tun ƙuruciya, kuma shi ne ya zame mata tubalin rayuwar gwagwarmaya da ta yi daga baya.
Ba da jimawa ba aka yi mata aure tana da shekara goma sha uku, kamar yadda al’adar lokacin ta tanada. Auren bai daɗe da kawo mata kwanciyar hankali ba, domin mijinta ya bar ta tana ɗauke da ciki. Wannan ɗanɗanar rayuwa ta sa ta fahimci irin nauyin da mata ke ɗauka a cikin al’umma, abin da daga baya ya ƙara ƙarfafa mata gwiwar yaƙi da auren yara da kuma neman ilimi da damar rayuwa mai inganci ga mata.
Shigarta gwagwarmayar siyasa da yadda ta zama “Sawaba”:
Rayuwar Hajiya Gambo Sawaba ta sauya alƙibla ne a lokacin da ta fara hulɗa da masu fafutukar neman sauyi a Arewacin Najeriya. A wancan lokaci, siyasa ta kasance tamkar fili ne da aka killace wa maza. Ba kasafai ake ganin mace ta fito fili tana halartar taruka, balle ta yi jawabi ko ta jagoranci gangamin siyasa ba. Duk da haka, Gambo ba ta bari wannan tunani ya hana ta shiga fafutukar da ta yi imanin za ta amfani talakawa ba.
A lokacin da ta shiga jam’iyyar Northern Elements Progressiɓe Union (NEPU), ba ta je neman suna ko muƙami ba. Abin da ya ja hankalinta shi ne manufofin jam’iyyar na yaƙi da zalunci, kare haƙƙin talakawa da kuma ƙoƙarin gina al’umma mai adalci. Wannan ne ya sa ta rungumi siyasa a matsayin wata hanya ta kawo sauyi, ba kawai hanyar neman mulki ba. Aminu Kano ya hango irin ƙarfin hali da jajircewar da ke tattare da ita tun farkon shigarta, abin da ya sa ya kasance ɗaya daga cikin manyan mutanen da suka ba ta damar taka rawa a cikin gwagwarmayar siyasar Arewa.
A hankali sunanta ya fara bazuwa a tsakanin jama’a. Tana zagayawa unguwanni da ƙauyuka tana wayar da kan mata da talakawa kan muhimmancin ilimi, adalci da kuma shiga cikin harkokin siyasa. A lokacin da wasu mata ke jin tsoron fitowa fili saboda tsangwama ko tsoron abin da al’umma za ta ce, ita kuwa Gambo ta ɗauki hakan a matsayin nauyin da dole ne ta sauke.
Jajircewarta ta burge shugabannin NEPU matuƙa. A sakamakon haka ne aka ba ta laƙabin “Sawaba”, kalmar Hausa da ke nufin ‘yanci ko kuɓuta. Laƙabin bai zo ne saboda shahara ba, ya samo asali ne daga irin gudunmawar da take bayarwa wajen fafutukar ganin talakawa sun samu ‘yanci daga zalunci da danniya. Daga wannan lokaci, sunan “Gambo Sawaba” ya mamaye sunanta na haihuwa, har ya zama sunan da tarihi ya adana.
Sai dai shigarta siyasa ba ta zo da sauƙi ba. A lokacin, wasu sun ɗauki fitowarta a matsayin karya al’ada. An yi mata suka, an yi mata barazana, an kuma yi ƙoƙarin dakatar da ita ta hanyoyi daban-daban. Amma maimakon hakan ya sa ta ja da baya, sai ya ƙara mata ƙwarin gwiwa. Ta yi imanin cewa idan mace ta yi shiru saboda tsoro, to waɗanda za su zo bayanta za su tarar da ƙofofi a rufe.
A cikin jawabanta, ta fi mayar da hankali kan matsalolin da suka shafi talakawa, musamman mata. Ta yi kira da a bai wa ‘ya’ya mata damar zuwa makaranta, ta yi adawa da auren yara, sannan ta nuna cewa ci gaban al’umma ba zai tabbata ba muddin rabin al’ummar ƙasa, wato mata, ba su samu damar ba da gudubmawarsu ba. Waɗannan saƙonni sun fara samun karɓuwa a tsakanin jama’a, amma kuma sun ƙara jefa ta cikin dagga da masu adawa da sauyi.
Daga wannan lokaci ne rayuwar Gambo Sawaba ta shiga wani sabon babi; babin gwagwarmaya da ya haɗa da ƙyama, tsarewa, cin zarafi da kuma gwada ƙarfin zuciyarta fiye da yadda ta taɓa tsammani. Duk da haka, ba ta taɓa yin nadamar hanyar da ta zaɓa ba, domin a ganinta, mutuncin al’umma ya fi jin daɗin mutum guda muhimmanci.
Kalubalen da Hajiya Gambo Sawaba ta fuskanta:
1. Rasuwar iyaye tun tana da ƙuruciya
Rayuwar Hajiya Gambo Sawaba ta fara ne da ƙalubalen da ba kowane yaro ke iya jurewa ba. Tun tana da shekara goma ta rasa mahaifinta, Isa Amarteifio, wanda shi ne ginshiƙin rayuwar iyalinsu. Kafin ta gama sabawa da wannan rashi, sai kuma rasuwar mahaifiyarta, Fatima, bayan shekaru kaɗan. Wannan ya sa rayuwarta ta sauya gaba ɗaya, domin ta taso ba tare da kulawar iyayen da za su jagorance ta ba. Rashin iyayen ya kuma katse karatunta tun tana ƙaramar yarinya, abin da ya hana ta samun cikakkiyar damar ilimin boko kamar sauran takwarorinta.
2. Auren ƙuruciya da mutuwar aurenta
A lokacin da yawancin yara mata ke ci gaba da karatu da wasa, an yi wa Gambo aure tana da shekara goma sha uku. Wannan ya kasance cikin al’adun da suka mamaye al’umma a wancan lokaci. Sai dai auren bai daɗe ba, domin mijinta ya rabu da ita tana ɗauke da ciki. Wannan ƙwarewar rayuwa ta sa ta fahimci irin nauyin da mata da ‘yan mata ke ɗauka a cikin al’umma, musamman waɗanda ba su da damar yanke hukunci kan makomarsu.
3. ɗauri da cin zarafi saboda gwagwarmaya
Shigarta siyasa ya buɗe wani sabon babi na ƙalubale. Saboda ƙin yin shiru kan abin da ta ɗauka a matsayin zalunci, an kama ta aka tsare ta sau da dama. Rahotanni sun nuna cewa ta shiga gidan yari sau goma sha shida a lokuta daban-daban saboda ayyukan siyasa da gwagwarmayar da take yi. A wasu lokutan kuma ta sha duka da cin zarafi yayin tsarewarta, amma hakan bai sa ta janye daga fafutukar da ta fara ba. A maimakon haka, duk lokacin da aka sake ta, sai ta koma cikin al’umma tana ci gaba da wayar da kan jama’a da kuma kare haƙƙin talakawa.
4. Suka da tsangwama daga al’umma
Ba gwamnati kaɗai ta fuskanta ba. A cikin al’umma ma akwai waɗanda ba su amince da fitowar mace tana jawaban siyasa ba. Wasu sun ɗauki abin a matsayin saba wa al’ada, wasu kuma suna ganin wurin mace shi ne gida. Wannan ya jefa ta cikin suka, zarge-zarge da ƙoƙarin dakatar da ita. Duk da haka, ta ci gaba da tafiyarta ba tare da ta bari matsin lamba ya hana ta faɗin abin da ta yarda da shi ba.
5. Rayuwar sadaukarwa ba tare da neman abin duniya ba
Duk da shaharar da ta samu, rayuwar Gambo Sawaba ba ta kasance ta wadata ba. Ta shafe yawancin rayuwarta tana fafutuka ne saboda abin da ta yi imani zai amfani al’umma, ba tare da neman tara dukiya ko amfani da siyasa wajen bunƙasa kanta ba. Wannan ya sa ta ci gaba da rayuwa cikin sauƙi, duk da irin girman sunan da ta samu a tarihin Najeriya.
Nasarorin da Hajiya Gambo Sawaba ta samu:
Ko da yake tarihin Hajiya Gambo Sawaba ya cika da wahalhalu, hakan bai hana ta barin gado mai ɗorewa ba. A zahiri ma, irin ƙalubalen da ta sha ne suka ƙara bayyana girman nasarorin da ta cimma, domin ta yi tasiri a lokacin da mata ba su da isasshen damar shiga harkokin jama’a.
aya daga cikin manyan nasarorinta shi ne karya shingen da ya hana mata shiga siyasa a Arewacin Najeriya. A lokacin da aka ɗauki siyasa a matsayin abin da ya shafi maza kaɗai, ta fito ta nuna cewa mace ma na da damar tsayawa a gaban jama’a, ta bayyana ra’ayinta kuma ta taka rawa wajen tsara makomar al’umma. Wannan jajircewa ta ba mata da dama ƙarfin gwiwar fitowa daga inuwa, suka fara ganin cewa shiga harkokin jama’a ba laifi ba ne, kuma ba abin da ya takaita ga maza kawai.
Haka kuma, ta taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan mata kan muhimmancin ilimi. Ta yi imanin cewa ilimi shi ne ginshiƙin ‘yanci da ci gaban mace, kuma ba za a iya gina al’umma mai ɗorewa ba idan aka ci gaba da hana ‘ya’ya mata damar zuwa makaranta. Ta riƙa amfani da tarurruka da gangamin wayar da kai wajen ƙarfafa iyaye su bai wa ‘ya’yansu mata damar yin karatu, tana mai nuna cewa ilimin mace ba amfaninta kaɗai ba ne, har ma amfanin iyali da al’umma baki ɗaya.
Gambo Sawaba ta kuma kasance cikin waɗanda suka ɗaga murya kan matsalolin da mata ke fuskanta, musamman auren yara da kuma tauye musu damar yanke hukunci kan rayuwarsu. A lokacin da irin waɗannan batutuwa ba kasafai ake tattauna su a bainar jama’a ba, ita ta dage cewa ci gaban al’umma ba zai tabbata ba muddin ana ci gaba da ɗaukar mace a matsayin wadda ba ta da haƙƙin bayyana ra’ayinta ko ba ta da rawar da za ta taka wajen gina ƙasa.
Anan za mu tsaya, a sati na gaba da yardar Allah za mu ƙaro wasu nasarorin da Hajiya Gambo Sawaba ta samu, kafin mu ɗora da wasu bayanai da muke hasashen za ku ƙaru da su dangane da tarihinta.
