Gurbin AFCON: Super Eagles ta doke Madagascar bayan farfaɗowa a wasan farko

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta fara wasanninta na neman gurbi a gasar Kofin ƙasashen nahiyar Afirka (AFCON) na 2027 da ƙafar dama bayan doke Madagascar da ci 2 da 1 a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo a Jihar Akwa-Ibom.

Super Eagles tana cikin rukunin L ne, wanda ƙasa ɗaya ce take da damar shiga gasar saboda bai wa Tanzaniya gurbi kai-tsaye a matsayinta na mai masaukin baƙi.

A wasan na daren Asabar, Madagascar ce ta fara zura ƙwallo a minti 16 a lokacin ɗan wasa Charly Couturier ya samu damar fasa ‘yan wasan bayan Super Eagles.

Nijeriya ta samu damar mayar da martani ne a minti na 46 ta hannun ɗan wasa George Ilenikhena, lamarin da ya mayar da wasan 1 da1. Ɗan wasa Moses Usor ne ya zura wa Super Eagles ƙwallo ta biyu ana minti na 65, wanda ya taimaka wa Nijeriya samun nasara a wasan duk da matsi daga Madagascar ana gab da tashi.

An dai buga wasan ne ba tare da zakaran ɗan wasan gaba ba, Victor Osimhen acikin ‘yan Super Eagles ɗin sakamakon rauni da yake fama da shi da ya samu a wasannin ƙungiyarsa ta Galatasaray.

By Babaji

Leave a Reply