Ma’aikatar lafiya ta Nasarawa ta amince da tsarin daidaituwar lafiya domin magance sauyin yanayi kan lafiyar al’umma

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Ma’aikatar lafiya ta jihar Nasarawa ta amince da tsarin daidaitawa na lafiya na gwamnatin tarayya na 2025-2030 domin magance tasirin sauyin yanayi kan tsarin lafiyar al’ummar jihar.

An bayyana amincewar ne a wajen taron bitar masu ruwa da tsaki na kwana ɗaya domin tantance tsarin daidaitawa na lafiya na jihar ta Nasarawa wadda aka gudanar a ranar Juma’a a Lafia babban birnin jihar.

Tsarin daidaitawar lafiyar na ƙasa wani tsari ne na haɗa daidaitawa da sauyin yanayi a cikin manufofin lafiya da shirye-shirye da kuma gina ababen more rayuwa a faɗin ƙasar nan.

Da yake jawabi a wajen taron, jami’in dake kula da sauyin yanayi da lafiya na jihar Dakta Godwin Ewuga yace sauyin yanayi ya haifar da ƙalubalen lafiya da dama.

Yace sauyin yanayin a yanzu haka yana shafar lafiya ta hanyar kawo cikas ga ayyukan kiwon lafiya da kuma raunuka da mace-mace dake tattare da ambaliyar ruwa da sauran bala’o’i.

Ewuga ya kuma ce sauyin yanayi na taimakawa wajen yaɗuwar cututtuka masu yaɗuwa ta ruwa da ta abinci da kuma ta sauro ciki har da zazzaɓin cizon sauron.

Ya ƙara da cewa mutanen dake da wasu cututtuka masu tsanani kamar hawan jini da cututtukan zuciya da ƙoda da kuma asma na iya samun damuwa mai zafi dake fitowa daga ƙaruwar zafi.

Yace za a aiwatar da takardar idan gwamnatin jihar ta amince da ita.

Ewuga ya kuma yaba da gudunmawar masu ruwa da tsaki daga ma’aikatu da sassa da hukumomi daban-daban waɗanda suka halarci tantance takardar.

Yace takardar za ta samu kulawa idan gwamna ya amince da ita.

A nasa ɓangaren babban sakatare na ma’aikatar lafiya ta Jihar Nasarawa Dakta Ibrahim Alhassan yace an shafe kimanin watanni 20 ana shirya takardar.

Alhassan yace aikin tantancewar ya haɗa da wakilai daga ma’aikatun lafiya da kasafin kudi da tsare-tsare da kiwon dabbobi da noma da cigaban ɗan Adam da kuma hukumar kula da yanayi ta Najeriya da hukumar makamashi mai sabuntawa da kuma Red Cross da sauran su.

“Muna nan yau don tantance wata takarda da aka daɗe ana shiryawa. Don haka a gare ni wannan bikin aiki ne tuƙuru wato bikin jajircewa ne. Kuma zan ce muna godiya ga jami’in da ya amince ya ɗauki wannan aiki mai wahala. Muna kuma godiya ga dukkan masu ruwa da tsaki saboda gudunmawar da suka bayar wajen ganin wannan takarda ta yi nasara,” in ji shi.

Tun farko da yake jawabi daraktan lafiyar jama’a na jihar Dakta Peter Attah yace jihar Nasarawa na daga cikin jihohi 15 na farko a ƙasar nan da suka ƙirƙiro tsarin daidaitawa na lafiyar jihohin su.

Yace a shirye takardar take don amincewa daga gwamna kuma ma’aikatar za ta aiwatar da ita idan ta samu amincewar da ta dace ba tare da ɓata lokaci ba.

By ukarofi

Leave a Reply