Bayan shafe shekaru biyar ana shari’a, kotu ta wanke mutumin da ake zargi da kashe matarsa a Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 11, da ke yankin Bompai a cikin birnin Kano, ta sallami tare da wanke Yusuf Nadabo Kawule, wanda ake tuhuma da laifin kashe matarsa.

Rahoton News Point Nigeria ya ce kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Nasir Saminu, ta wanke wanda ake tuhuma bayan ta yanke hukuncin cewa masu gabatar da ƙara ba su gabatar da isassun hujjojin da za su tabbatar da zargin kisan kai a kansa ba.

Masu gabatar da ƙara sun tuhumi Kawule da laifin kisan kai bisa tanadin sashe na 221 na dokar Penal Code, amma ya musanta aikata laifin.

A yayin shari’ar, masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidu, yayin da wanda ake tuhuma shi ma ya tsaya a gaban kotu domin bayar da bayaninsa kan zargin da ake masa.

Lamarin da ya kai ga shari’ar ya faru ne a shekarar 2021 a ƙauyen Kogo da ke ƙaramar Hukumar Takai ta Jihar Kano.

An zargi Kawule da ɗaukar matarsa a kan babur domin zuwa neman mata gida a wani ƙauye, amma sun yi haɗarin mota wanda ya yi sanadin mutuwar matar.

Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro sun kama shi, daga bisani aka gurfanar da shi a gaban kotu domin amsa tuhumar da ake masa.

Sai dai kotun ta sallame shi tare da wanke shi, bisa dalilin cewa ba a gabatar da isassun hujjojin da za su tabbatar da laifin da ake tuhumarsa da shi ba.

By ukarofi

Leave a Reply