Yunƙurin sulhu a ACF ya ci tura

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rikicin shugabanci da ke ci gaba da girgiza ƙungiyar Tuntuɓa da Kare Muradun Arewa ta Arewa Consultative Forum (ACF) ya ƙara tsananta, bayan wani taron sirri da aka gudanar domin shawo kan saɓanin da ke tsakanin shugabannin ƙungiyar ya tashi ba tare da cimma matsaya ba.

Taron, wanda ya haɗa mambobin kwamitin amintattu (BoT), kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) da wasu manyan sarakunan gargajiya daga Arewacin Nijeriya, ya ƙare ne cikin abin da wasu majiyoyi suka bayyana a matsayin rashin cimma matsaya.

An rawaito cewa an gudanar da taron ne a ranar Talata a gida mai zaman kansa na Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar na III, da ke Maitama, Abuja. Taron ya ɗauki tsawon sa’o’i biyu, daga ƙarfe 5:00 zuwa 7:00 na yamma, ba tare da samun wata sahihiyar mafita kan rikicin ba.

Daga cikin sarakunan gargajiyar da suka halarci taron akwai Sarkin Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, da Aku Uka na Wukari, Dakta Manu Ishaku Adda Ali. Sai dai rahotanni sun nuna cewa Sarkin Musulmi bai halarci taron ba, saboda wasu muhimman ayyukan ƙasa da ya ke gudanarwa a wani wuri.

Ko da yake ba a samu cikakken bayani kan abubuwan da suka gudana a taron ba, wanda aka shirya bisa yunƙurin Sarkin Musulmi, wasu majiyoyi da ke da masaniya kan harkokin cikin gida na ACF sun shaida cewa an fi mayar da hankali ne kan yadda za a kawo ƙarshen rarrabuwar kawuna da ke ƙara ta’azzara a shugabancin ƙungiyar.

Wata majiya ta ce Sarkin Nupe da Aku Uka sun nuna matuƙar damuwa kan yadda kwamitin amintattu da kwamitin zartarwa suka kasa samun matsaya ta bai ɗaya da za ta ba su damar haza kai wajen nemo mafita ga matsalolin tsaro da tattalin arzikin da ke addabar Arewa. An fahimci cewa tun farkon shekarar 2026, Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, tare da goyon bayan Sarkin Lafia, Mai Shari’a Sidi Dauda Bage Muhammad, da sauran sarakunan Arewa, suka fara tattaunawa da shugabannin ACF domin shawo kan rikicin. Wannan ya biyo bayan saɓanin da ya ɓarke tsakanin kwamitin amintattu da kwamitin zartarwa, inda ɓangarorin biyu suka riƙa zargin juna da haddasa matsalar.

A wani sabon lamari da ya nuna yadda rikicin ke ƙara ƙamari, jami’an ’yan sanda sun rufe sakatariyar ƙungiyar ACF da ke Kaduna a ranar Litinin. Sai dai an samu saɓanin bayanai kan ainihin abin da ya haddasa rufe sakatariyar.

Shugaban kwamitin zartarwa na ƙasa, Mamman Mike Osuman, ya shigar da ƙara ga Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, kan zargin cewa wasu mutane sun kutsa cikin sakatariyar ƙasa ta ACF da ke Kaduna ba bisa ƙa’ida ba. A cikin ƙarar da ya rubuta ranar 9 ga Nuwamban 2026, Osuman ya zargi Munir Mustapha da Bukar Zarma da kutsawa cikin hedikwatar ƙungiyar da ƙarfi tare da kwashe wasu muhimman kayayyaki. Sai dai, Gwamnatin Jihar Kaduna ta musanta zargin cewa tana da hannu a rufe sakatariyar ƙasa ta ƙungiyar ACF da ke Kaduna.

By ukarofi

Leave a Reply