Kamfanonin DisCos sun nemi afuwar ’yan Nijeriya bayan makonni a duhu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanonin rarraba hasken lantarki a Nijeriya (DisCos) sun nemi afuwar al’ummar ƙasar bisa ci gaba da fuskantar ƙarancin wutar lantarki, lamarin da ya jefa gidaje da harkokin kasuwanci cikin mawuyacin hali sakamakon shafe makonni ana fama da ɗaukewar wuta. Neman afuwar na zuwa ne daidai lokacin da fushin al’umma ke ƙara ƙamari sakamakon ƙarancin lantarkin, inda masu amfani da shi ke fama da matsanancin rashin tabbas kan lokacin da haske zai dawo yadda ya kamata.

Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na ƙungiyar Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki ta Nijeriya (ANED), Sunday Oduntan, ne ya nemi afuwar a ranar Litinin, yayin wata tattaunawa da ya yi a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels. Oduntan ya amince cewa al’ummar Nijeriya sun sha wahala matuƙa a cikin makonnin baya-bayan nan, sakamakon matsalolin wutar lantarki da suka addabi ƙasar. Ya ce, “Da farko, ina son na fara da ba ’yan Nijeriya haƙuri. Yin hakan ya zama wajibi, domin al’ummar ƙasar sun shiga cikin wannan matsala tsawon makonni da dama.”

Haka kuma, ya nuna damuwarsa kan abin da ya kira sake dawo da al’adar ɗora wa juna laifin matsalolin da suka dabaibaye ɓangaren samar da wutar lantarki, yana mai tunatar da cewa irin wannan sa-in-sa tsakanin masu ruwa da tsaki ya taɓa kawo cikas ga harkar wutar lantarki tsakanin shekarun 2016 zuwa 2019. Ya bayyana cewa a wancan lokaci, kamfanonin rarraba wutar lantarki, masu kula da layukan isar da wuta, kamfanonin samar da wutar lantarki da masu samar da iskar gas sun mayar da hankali wajen zargin juna, maimakon haɗa kai domin magance matsalolin da suka haddasa ƙarancin wutar.

Oduntan ya ce, “Babbar matsalarmu ita ce mun sake komawa kan mummunar hanyar da muka bi tsakanin shekarun 2016 zuwa 2019. Wace hanya ce kuwa? Ita ce ɗora wa juna laifi. Abin da ya faru a wancan lokaci shi ne, wasu za su zargi kamfanonin rarraba wutar lantarki, su kuma su zargi Kamfanin Isar da Wutar Lantarki ta Nijeriya (TCN). Shi kuma TCN ya zargi kamfanonin samar da wutar lantarki, su kuma su zargi masu samar da iskar gas, daga ƙarshe masu samar da iskar gas su ɗora alhakin matsalar kan rashin biyan kuɗaɗensu. Yanzu mun sake komawa kan wannan hali, kuma ina ganin akwai buƙatar dakatar da shi cikin gaggawa.”

Shugaban na ANED ya kuma nuna shakku kan bayanan baya-bayan nan da Kamfanin Kula da Tsarin Samarwa da Rarraba Wutar Lantarki Mai Zaman Kansa na Nijeriya (NISO) da Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPC Limited) suka fitar dangane da musabbabin matsalar ƙarancin wutar lantarki. A cewarsa, NISO ya danganta matsalar samar da wutar lantarki da ƙarancin ruwan da ake samu a madatsun ruwa da kuma ƙarancin iskar gas, yayin da daga baya NNPC ya fitar da sanarwa da ke nuna cewa iskar gas tana nan akwai ta.

Sai dai Oduntan ya soki bayanin kamfanin man fetur ɗin, yana mai cewa ya kamata ya yi ƙarin haske kan ko akwai matsalar bashin kuɗaɗen da ake bin kamfanonin samar da wutar lantarki, wanda ka iya shafar samar musu da iskar gas. Ya ce, “Daga bayanin da NNPC ta fitar, a bayyane yake cewa ba ta faɗa mana cikakken gaskiya ba. Abin da nake sa ran kamfanin ya yi shi ne ya yi mana bayanin ko akwai matsalar biyan kuɗi. Muna buƙatar sanin ko an biya kuɗin iskar gas ɗin da aka samar, wa ya biya, wa bai biya ba, da kuma ko an kai iskar gas ɗin ga waɗanda ake buƙatar su yi amfani da ita.”

Ya buƙaci Ministan Makamashi da Wutar Lantarki da ya jagoranci ƙoƙarin warware saɓanin da ke tsakanin masu ruwa da tsaki, ta hanyar kiran dukkan hukumomi da kamfanonin da abin ya shafa zuwa teburin tattaunawa domin gano ainihin musabbabin matsalar. Oduntan ya ce, “Wannan kai-komo na ɗora wa juna laifi tsakanin masu samar da iskar gas, NNPC, da kuma Kamfanin Isar da Wutar Lantarki (TCN) ko NISO, ina ganin ya kamata Ministan Makamashi da Wutar Lantarki ya karɓi ragamar jagoranci. Akwai buƙatar shugabanci mai ƙarfi, domin ƙarshe dole ne a kira dukkan waɗannan ɓangarori wuri guda domin tattauna matsalar tare da nemo mafita.”

Matsalar ƙarancin wutar lantarki ta kuma sake haifar da tambayoyi kan ingancin tsarin rarraba masu amfani da wutar lantarki zuwa rukunan A, B da C, wanda ke ƙayyade kuɗin da kwastomomi za su biya bisa mafi ƙarancin awannin wutar lantarki da ake tsammanin za su samu a kowace rana.

Abin damuwa shine, hatta masu amfani da wutar lantarki a rukuni na A, waɗanda ake tsammanin za su samu wuta na aƙalla awanni 20 a kullum, na ci gaba da kokawa kan rashin isasshiyar wutar lantarki. Wannan ya sanya jama’a ke ƙara shakkar ingancin hidimar da ake karɓar kuɗaɗe masu tsoka a kanta.

By ukarofi

Leave a Reply