Nijeriya ta shirya karɓar baƙuncin Taron Hulɗar Jama’a na Duniya – Idris

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin ta na karɓar baƙuncin Taron Hulɗar Jama’a na Duniya na shekarar 2026 (WPRF), wanda ake sa ran wakilai daga ƙasashe sama da 126 za su halarta daga ranar 15 zuwa 22 ga Nuwamba a Abuja.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin wani taron manema labarai a Abuja, inda ya ce taron zai ba Nijeriya damar nuna ƙwarewar ta da kuma ƙarfafa matsayin ta a fagen sadarwa na duniya.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, shi ne zai zama babban mai masaukin baƙi a taron, wanda zai gudana tare da babban taron ƙungiyar Hulɗar Jama’a ta Afrika karo na 37 (APRA).

Idris ya ce Nijeriya ce ƙasa ta farko a Yammacin Afrika, kuma ta biyu a nahiyar, da za ta karɓi baƙuncin WPRF. 

Ya bayyana taron a matsayin wata dama ta ƙarfafa dangantakar ƙasar nan da sauran ƙasashe, tare da ba da gudunmawa ga tattaunawar duniya kan harkokin sadarwa.

Da yake tsokaci kan taken taron mai cewa, “Sadarwa Mai Haƙƙi: Muryar Duniya”, ministan ya buƙaci ƙwararrun masu hulɗar jama’a da su riƙa kiyaye gaskiya, sahihancin bayanai, bayyana gaskiya da ƙa’idojin sana’a, musamman a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan yaɗuwar bayanan ƙarya da raguwar amincewar jama’a.

Ya ce: “Dole ne ƙwararrun masu hulɗar jama’a su fahimci cewa nauyin da ke kan su ya wuce kula da martabar mutane ko inganta muradun cibiyoyi. Suna da haƙƙin tabbatar da gaskiya, sahihancin bayanai, bayyana gaskiya, bin ƙa’idojin sana’a da kuma kare muradun jama’a.”

Ministan ya bayyana goyon bayan Gwamnatin Tarayya ga yunƙurin kafa Cibiyar ƙasa da ƙasa ta UNESCO mai mataki na biyu kan Ilimin Kafafen Yaɗa Labarai da Bayanai (wato IMILI) a Abuja, yana mai cewa cibiyar za ta taimaka wa ’yan ƙasa, musamman matasa, wajen gane bayanan da za su iya yaudarar su da kuma amfani da kafafen zamani yadda ya kamata.

Idris ya ƙara da cewa ya kamata sadarwar gwamnati ta ƙunshi sauraron jama’a, magance matsalolin su da kuma samar musu da sahihan bayanai domin su yanke shawara bisa cikakken sani.

Shugaban Cibiyar Hulɗar Jama’a ta Nijeriya (NIPR), Dakta Ike Neliaku, ya yaba wa Idris bisa goyon bayan da ya bayar wajen neman damar karɓar baƙuncin taron a Nijeriya.

Shi kuwa Sakatare-Janar na ƙungiyar Hulɗar Jama’a ta Afrika (APRA), Dakta Omoniyi P. Ibietan, ya bayyana haɗa taron WPRF da babban taron APRA karo na 37 a matsayin wata dama ga Afrika ta ƙarfafa muryar ta da tasirin ta a fagen sadarwa na duniya.

Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa na ƙungiyar Hulɗar Jama’a da Sadarwa ta Duniya, Farfesa Justin Green, ya bayyana cewa ana sa ran wakilan Majalisar ɗinkin Duniya, Bankin Duniya, Tarayyar Afrika da Hukumar Tarayyar Turai za su halarci taron.

By ukarofi

Leave a Reply