2027: Tinubu, Atiku da Obi sun bayyana ƙudirorinsu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Yayin da Nijeriya ke tunkarar babban zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027, manyan ’yan siyasar ƙasar sun fara bayyana irin manufofi da tsare-tsaren da suke son aiwatarwa idan suka samu damar jagorantar ƙasar. A wannan karon, batutuwan da suka fi ɗaukar hankalin al’umma sun haɗa da matsalar tsaro, hauhawar farashin kayayyaki, rashin aikin yi, matsalar wutar lantarki, koma bayan tattalin arziki da kuma yadda za a inganta rayuwar talakawa.

Shugaban ƙasa mai ci, Bola Ahmed Tinubu, tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan Jihar Anambara, Peter Obi, na daga cikin manyan ’yan siyasar da suka fara bayyana manufofinsu gabanin zaɓen mai zuwa.

Tinubu, wanda ke neman sake samun wa’adin mulki na biyu a ƙarƙashin jam’iyyar APC, ya gabatar da kundin manufofin jam’iyyarsa na shekarar 2027 zuwa 2031 mai taken; ‘From Reform to Prosperity Agenda’, wato daga sauye-sauyen tattalin arziki zuwa wadata.

A nasa ɓangaren, Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, ya bayyana wani shiri da ya kira na ceto Nijeriya daga matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro, yayin da Peter Obi na jam’iyyar NDC ya fi mayar da hankali kan haɗin kan ƙasa, kare rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma samar da shugabanci mai sauraron al’umma.

Duk da bambancin hanyoyin da suka gabatar, abin da ya haɗa waɗannan ’yan siyasa shi ne amincewarsu cewa Nijeriya na buƙatar manyan sauye-sauye domin fitar da al’ummar ƙasar daga halin ƙuncin rayuwa da suke ciki.

Sai dai mene ne ainihin abin da kowannensu ya yi alƙawarin yi? A waɗanne fannoni ne suka yi kama, kuma a ina ne manufofinsu suka bambanta?

Tsaro: Babban ƙalubalen da ke gaban kowace gwamnati

Babu shakka, matsalar tsaro na daga cikin manyan ƙalubalen da suka addabi Nijeriya, musamman matsalar ’yan bindiga, ta’addanci, garkuwa da mutane, rikice-rikicen al’umma da sauran laifuffukan da ke barazana ga rayukan jama’a. A cikin kundin manufofinsa, Tinubu ya yi alƙawarin ƙarfafa rundunonin tsaro ta hanyar ɗaukar ƙarin sojoji 28,000 da ’yan sanda 50,000, domin ƙara ƙarfin yaƙi da ta’addanci, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Baya ga haka, ya yi alƙawarin ɗaukar ƙarin jami’ai 30,150 a Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Nijeriya (NSCDC), domin su karɓi wasu ayyukan tsaron wurare da cibiyoyi da a halin yanzu ke ƙara wa ’yan sanda nauyi.

Shirin na APC ya kuma ƙunshi kammala gina sabbin rundunonin soji guda huɗu a Makurɗi, Ilorin, Jalingo da Benin City, tare da samar musu da kayan aikin da suka dace. Haka kuma, Tinubu ya yi alƙawarin kawo sauye-sauye a rundunar ’yan sanda ta hanyar amfani da kyamarorin da jami’ai za su riƙa sanyawa a jikinsu, na’urorin adana bayanai, taswirar wuraren ayyuka da ingantattun hanyoyin binciken laifuffuka.

Atiku kuwa, a cikin manufofinsa, ya bayyana cewa zai ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa ta hanyar ɗaukar ƙarin jami’an tsaro, inganta walwalarsu da yaƙi da cin hanci da rashawa a cikin hukumomin tsaro. Ya kuma yi alƙawarin amfani da fasahar zamani wajen tattara bayanan sirri da gudanar da ayyukan tsaro, tare da samar da cikakken goyon bayan siyasa domin yaƙi da ta’addanci, ’yan bindiga da manyan laifuffuka. Wani muhimmin ɓangare na shirin Atiku shi ne ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da ƙasashen da ke maƙwabtaka da Nijeriya, domin tunkarar matsalolin tsaron da ke ƙetare iyakokin ƙasa.

Peter Obi kuwa ya mayar da hankali ne kan tabbatar da cewa kare rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne babban nauyin kowace gwamnati. Ya ce babban burinsa shi ne ganin cewa babu wata uwa da za ta ci gaba da zubar da hawaye saboda rasa ɗanta, babu matar da za ta rasa mijinta sakamakon tashin hankali, sannan babu wani uba da zai sha azabar rasa iyalinsa saboda rashin tsaro. Obi ya kuma yi magana kan matsalar ’yan gudun hijira da ke zaune a sansanonin wucin gadi, inda ya bayyana cewa kasancewar ko mutum ɗaya a sansanin ’yan gudun hijira alama ce ta gazawar gwamnati wajen kare rayukan jama’a da samar musu da yanayin da za su zauna lafiya. Ya yi alƙawarin ganin an dawo da waɗannan mutane zuwa gidajensu da garuruwansu cikin aminci.

Yayin da yake magana kan matsalar garkuwa da mutane, Obi ya yi gargaɗin cewa ba zai amince masu garkuwa da yara ko wasu mutane su shiga daji su ɓuya ba tare da jami’an tsaro sun bi sahunsu ba. Ya kuma ambaci wasu yankunan Jihar Filato, ciki har da Bokkos, Barkin Ladi da Mangu, a matsayin wuraren da matsalar rashin tsaro ke ci gaba da shafar rayuwar jama’a.

A nan ne bambancin manufofin ukun ya fi bayyana: Tinubu ya fi gabatar da ƙididdigar yawan jami’an tsaro da kayan aikin da zai samar, Obi ya fi jaddada kare rayuka da dawo da mutanen da rikici ya raba da muhallansu, yayin da Atiku ya yi alƙawarin tunkarar matsalar tsaron ba tare da gabatar da cikakken tsarin aiwatarwa a bayanan da aka bayyana ba.

Tattalin arziki da tsadar rayuwa: Wa zai sauƙaƙa wa ’yan Nijeriya?

Matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa na daga cikin batutuwan da suka fi damun al’ummar Nijeriya, musamman sakamakon hauhawar farashin abinci, sufuri, man fetur da sauran muhimman kayayyakin masarufi.

Tinubu ya gabatar da burin bunƙasa tattalin arzikin ƙasar da kashi shida cikin ɗari a duk shekara nan da 2031, tare da rage rashin aikin yi tsakanin matasa. Ya kuma yi alƙawarin faɗaɗa damar samun lamuni cikin sauƙi, rage asarar amfanin gona bayan girbi da inganta hanyoyin sufuri domin rage kuɗin da ake kashewa wajen jigilar kayayyaki tsakanin jihohi. A cewarsa, inganta wuraren ajiya da sarrafa amfanin gona zai taimaka wajen rage ɓarnar kayan abinci, wanda hakan zai iya ƙara yawan kayayyakin da ake samu a kasuwanni.

Haka kuma, ya sanya burin ƙara yawan abincin da ake nomawa a cikin gida domin ƙarfafa wadatar abinci da rage dogaro da kayayyakin da ake shigo da su daga ƙasashen waje.

Atiku Abubakar kuwa ya gabatar da wata hanya daban ta magance matsin tattalin arziki, inda ya yi alƙawarin sake duba batun tallafin man fetur tare da dawo da shi domin rage nauyin da tsadar man fetur ta ɗora wa ’yan Nijeriya. Wannan na daga cikin manyan alƙawuran da ya yi, musamman ganin cewa cire tallafin man fetur na daga cikin muhimman manufofin gwamnatin Tinubu da suka haifar da muhawara mai yawa a ƙasar.

Atiku ya kuma yi alƙawarin sake buɗe iyakokin Nijeriya na ƙasa domin bunƙasa kasuwanci da ƙasashen Afirka maƙwabta. A cewarsa, wannan mataki zai samar da damarmakin tattalin arziki ga manoma, ’yan kasuwa, masu sufuri da sauran masu sana’o’i, tare da ƙarfafa hulɗar kasuwanci tsakanin Nijeriya da ƙasashen da ke maƙwabtaka da ita. Ya kuma bayyana cewa manufofinsa za su mayar da hankali wajen inganta walwalar jama’a, bunƙasa harkokin kasuwanci, samar da ayyukan yi da ƙara kuɗaɗen shiga ga iyalai.

Peter Obi kuwa, a cikin bayanan da ya gabatar, ya fi jaddada buƙatar samar da tattalin arzikin da zai bai wa ’yan Nijeriya damar gudanar da sana’o’insu da samun abin dogaro da kai cikin yanayi mai kyau. Sai dai bai gabatar da takamaiman ƙididdigar bunƙasar tattalin arziki, tsarin tallafin man fetur ko shirin buɗe iyakoki irin wanda Atiku ya bayyana ba.

A wannan fanni, Tinubu ya gabatar da manufofin bunƙasa tattalin arziki ta hanyar samar da ababen more rayuwa da ƙarfafa samarwa, Atiku ya mayar da hankali kan rage nauyin tsadar rayuwa ta hanyar sake duba tallafin man fetur da buɗe iyakoki, yayin da Obi ya jaddada muhimmancin haɗa kan ƙasa da samar da shugabanci da zai saurari buƙatun jama’a.

Ayyukan yi da walwalar jama’a:

Rashin aikin yi, musamman tsakanin matasa, na daga cikin matsalolin da ke hana ci gaban Nijeriya. Saboda haka, yadda kowace gwamnati za ta samar da ayyukan yi na daga cikin abubuwan da za su iya jan hankalin masu zaɓe.

Tinubu ya yi alƙawarin rage rashin aikin yi tsakanin matasa da rabi nan da shekarar 2031, tare da faɗaɗa damar samun lamuni domin bunƙasa ƙananan sana’o’i da kasuwanci. Haka kuma, shirin samar da gidaje 200,000 masu sauƙin kuɗi ga ma’aikata na daga cikin manufofin da ya gabatar domin inganta rayuwar iyalai. Za a aiwatar da wannan shiri ne ta hanyar shirin samar da gidaje ga al’umma, tsarin lamunin sayen gidaje da haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu.

Atiku kuwa ya ce, shirin da yake son aiwatarwa zai mayar da hankali kan samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arzikin iyalai, tare da rage matsin da hauhawar farashin kayayyaki ke jawo musu. Ya kuma yi alƙawarin cewa sake buɗe iyakokin ƙasa zai samar da sababbin damarmakin sana’o’i ga manoma, ’yan kasuwa da masu harkokin sufuri.

Peter Obi kuwa, ya fi jaddada buƙatar samar da shugabanci mai sauraron jama’a, wanda zai fahimci matsalolinsu tare da samar da mafita bisa buƙatunsu. A ganinsa, ba zai yiwu a samu ci gaban ƙasa na gaskiya ba idan shugabanni ba sa sauraron waɗanda suka zaɓe su.

Wutar lantarki: Muhimmin ginshiƙin ci gaban ƙasa

Matsalar wutar lantarki na ci gaba da zama babban cikas ga ci gaban masana’antu da ƙananan sana’o’i a Nijeriya.

Tinubu ya yi alƙawarin ƙara ƙarfin wutar lantarkin da ake iya samarwa a ƙasar zuwa megawatt 10,000, tare da inganta hanyoyin isar da wutar da rarraba ta. Ya kuma yi alƙawarin faɗaɗa tsarin auna amfani da wutar lantarki da kuma samar da makamashi mai tsafta ga al’ummomin da ba su da isasshen wutar lantarki.

Atiku kuwa, ya bayyana cewa zai sake nazarin harkokin samar da wutar lantarki da kuma tsarin rarraba masu amfani da wuta zuwa rukuni-rukuni domin ƙayyade kuɗin da za su biya. Ya ce zai yi gyara ga tsarin cajin kuɗin wuta na yanzu domin kawo ƙarshen abin da ya bayyana a matsayin nuna bambanci wajen cajin masu amfani da wutar lantarki, tare da tabbatar da cewa farashin wutar ya kasance mai sauƙin biya ga jama’a.

Haka kuwa, bayanan Peter Obi da aka gabatar a taron masu goyon bayansa a Jos ba su ƙunshi takamaiman ƙididdigar samar da wutar lantarki ba.

Wannan ya nuna cewa Tinubu da Atiku sun ɗora ɗamarar cimma burin inganta fannin wutar lantarki.

Ilimi da kiwon lafiya: Makomar al’umma

Ilimi da kiwon lafiya na daga cikin muhimman ginshiƙan ci gaban kowace ƙasa, musamman wajen inganta rayuwar jama’a da samar da al’umma mai ƙwarewa.

A fannin ilimi, Tinubu ya yi alƙawarin ɗaukar ƙarin malamai 20,000 tare da horas da su, inda za a ba da fifiko ga mata malamai da yankunan karkara da ke fama da ƙarancin ma’aikatan koyarwa. Ya kuma yi alƙawarin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da rabi, tare da inganta rajistar shiga makaranta da yawan ɗaliban da ke kammala karatunsu.

A ɓangaren kiwon lafiya kuwa, ya sanya burin tabbatar da cewa kashi 90 cikin ɗari na cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a Nijeriya suna aiki yadda ya kamata nan da 2031. Haka kuma, yana son faɗaɗa inshorar lafiya domin ta shafi kashi 40 cikin ɗari na al’ummar ƙasar, tare da rage kuɗaɗen da marasa lafiya ke biya kai tsaye daga aljihunsu.

Daga cikin sauran manufofinsa akwai farfaɗo da kusan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 1,000, samar da kulawar gaggawa kyauta ga mata masu juna biyu a ƙananan hukumomi 774, da kuma kafa cibiyoyin kula da masu fama da cutar kansa a yankuna shida na siyasar Nijeriya.

Atiku kuwa, ya yi alƙawarin sake fasalin hukumomi da tsarin gudanar da kiwon lafiya domin inganta damar samun ingantaccen magani cikin sauƙi. Ya kuma ce zai magance ƙarancin ma’aikatan lafiya, inganta albashinsu da walwalarsu, tare da samar da yanayin aiki da zai ƙarfafa ƙwararrun ma’aikatan lafiya su ci gaba da yi wa ƙasar hidima.

Peter Obi kuwa, ya gabatar da haɗin kan ƙasa da kare rayukan jama’a a matsayin manyan ginshiƙan gwamnatinsa, inda ya jaddada cewa gwamnati dole ta kula da waɗanda suka rasa ’yan uwansu, gidajensu da muhallansu sakamakon rikice-rikice.

Duk da cewa batutuwan ilimi da kiwon lafiya suna da matuƙar muhimmanci a ƙasar, jawabin Obi da aka bayyana a Jos bai ƙunshi takamaiman ƙididdigar ayyukan da zai yi a waɗannan fannoni ba.

Ilimi: Tallafin ɗalibai da rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta

A fannin ilimi, Atiku ya yi alƙawarin sake duba tsarin asusun lamunin ɗalibai na Nijeriya (NELFUND), tare da duba yiwuwar yafe basussukan ɗaliban da suka ci gajiyar lamunin. A cewarsa, ɗaliban Nijeriya sun cancanci samun tallafin karatu da damar samun ilimi cikin sauƙi, maimakon zora musu nauyin basussukan da za su iya zama cikas ga rayuwarsu bayan kammala karatu.

Tinubu kuwa, ya yi alƙawarin ɗaukar ƙarin malamai 20,000 da horas da su, tare da ba da fifiko ga mata malamai da yankunan karkara. Ya kuma yi niyyar rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da rabi nan da shekarar 2031.

Peter Obi bai gabatar da takamaiman adadin malamai ko shirin yafe basussukan ɗalibai a jawabin da ya yi a Jos ba, amma ya sanya inganta rayuwar al’umma da shugabanci mai sauraron jama’a a cikin manyan manufofinsa.

Kammalawa

Bayan nazarin manufofin ’yan takarar ukun, a bayyane yake cewa kowannensu ya gabatar da wata alƙibla da yake son bi wajen tafiyar da Nijeriya.

Tinubu ya gabatar da cikakken kundin manufofi mai ɗauke da ƙididdigar ayyukan da yake son cimmawa a fannoni daban-daban, ciki har da tsaro, wutar lantarki, gidaje, ilimi da kiwon lafiya.

Atiku ya gabatar da manufofi guda 12 da suka haɗa da dawo da tallafin man fetur, sake fasalin tsarin gwamnati, farfaɗo da tashoshin jiragen ruwa, tallafa wa matasa da mata da dala biliyan 10, da kuma sake fasalin tsarin ilimi da wutar lantarki.

Peter Obi kuwa ya fi jaddada haɗin kan ƙasa, tsaro, dawo da ’yan gudun hijira muhallansu da samar da shugabanci mai sauraron jama’a.

Sai dai babban abin da ya kamata ’yan Nijeriya su lura da shi shi ne cewa alƙawuran yaƙin neman zaɓe ba su zama nasarori kai tsaye ba. Akwai buƙatar kowanne ɗan takara ya bayyana yadda zai samar da kuɗaɗen aiwatar da manufofinsa, lokacin da zai fara su da kuma hanyoyin da zai bi wajen tabbatar da cewa an cimma burin. Musamman ma, shirin dala biliyan 10 na Atiku, alƙawarin gina gidaje 200,000 na Tinubu da shirin dawo da ’yan gudun hijira gidajensu na Obi, duk suna buƙatar ƙarin bayani kan hanyoyin aiwatarwa da tsarin sa ido.

A ƙarshe, abin da zai fi muhimmanci ga al’ummar Nijeriya shi ne yadda waɗannan tsare-tsare za su shafi rayuwarsu ta yau da kullum: ko za su samu tsaro, abinci cikin sauƙi, wutar lantarki mai ɗorewa, ayyukan yi, ilimi da kiwon lafiya mai inganci. Zaɓen 2027 zai ba ’yan Nijeriya damar nazarin waɗannan manufofi da tambayar kowanne ɗan takara muhimman tambayoyi: daga ina za a samo kuɗaɗen aiwatar da alƙawuran? Yaushe za a fara? Wa zai kula da aiwatarwa? Kuma ta yaya za a tabbatar da cewa jama’a sun amfana?

Domin makomar Nijeriya ba ta ta’allaƙa ga yawan alƙawuran da aka yi ba, sai dai ga yadda za a mayar da su ayyukan da za su kawo sauyi a rayuwar al’umma.

By ukarofi

Leave a Reply