Yanke wa ’yan ta’adda 2,512 hukunci: Babbar nasara a yaƙi da ta’addanci

Spread the love

Nasarar da Gwamnatin Tarayya ta samu na tabbatar da hukuncin laifin ta’addanci kan mutum 2,512, a matakai 11 na shari’o’in ta’addanci, abin farin ciki ne matuƙa. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin tsaro ke ƙara ƙaimi wajen gurfanar da mutanen da ƙungiyoyin da ake zargi da ɗaukar nauyin kuɗaɗe ko tallafa wa ayyukan ta’addanci.

Wannan gagarumar nasara da ba a taɓa samun irinta ba, tana nuna cikakken ƙudurin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kawo ƙarshen ta’addanci, ayyukan ’yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran nau’o’in tsattsauran ra’ayi da ke janyo zubar da jini a ƙasar nan. Muhimmancin wannan aiki mai sarƙaƙiya ya ƙara ƙarfi da gaggawa, musamman ganin yadda lokacin babban zaɓen ƙasa ke ƙaratowa, wanda aka tsara gudanarwa a ranakun 16 ga Janairu da 6 ga Fabrairu, 2027, domin zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan Majalisar Tarayya, sannan kuma zaɓen gwamnonin jihohi da na ’yan majalisun dokokin jihohi.

A cewar Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta ƙasa (NCTC), an samu hukuncin laifin ta’addanci kan mutum 791 a sabon zagayen shari’o’in da aka gudanar. Wannan na nuna ci gaba da ƙoƙarin magance matsalar ta’addanci ta hanyar tsarin shari’ar laifuffuka. Mai kula da cibiyar, Manjo-Janar Adamu Laka, ne ya bayyana adadin yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Talata, 3 ga Nuwamba, 2026.

An gudanar da wannan zagaye na shari’o’in ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, tsakanin ranakun 15 zuwa 24 ga Oktoba, 2026, inda kotuna 10 suka saurari shari’o’i sama da 1,000.

Mai kula da cibiyar ya ce sakamakon ya nuna ƙudirin gwamnati na hukunta duk wanda aka tabbatar da hannu a laifuffukan da suka shafi ta’addanci, tare da tabbatar da cewa an kiyaye ƙa’idojin shari’a. Ya jaddada cewa dole ne a gudanar da shari’o’in bisa adalci, inda kowace kotu za ta tantance hujjojin da aka gabatar mata cikin ’yanci, ba tare da tsoma baki ba.

ɗaya daga cikin fitattun sakamakon shari’o’in shi ne hukuncin kisa da aka yanke wa Suleiman Abu, bayan an same shi da laifin kasancewa mamba a ƙungiyar Boko Haram da kuma shiga cikin munanan hare-haren ta’addanci. Laifuffukan da aka danganta da shi sun haɗa da kai hare-hare kan sansanonin sojoji da fararen hula, waɗanda suka yi sanadin mutuwar mutane tare da jikkata wasu da raunuka masu tsanani. Wannan hukunci ya zama misali na irin hukuncin da mutum zai fuskanta idan kotu ta tabbatar da cewa yana da alhakin aikata laifuffukan ta’addanci.

Baya ga gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata laifuffuka, mai kula da cibiyar ya yi kira da a ƙara tallafa wa waɗanda suka tsira daga hare-haren ta’addanci da sauran waɗanda lamarin ya shafa. Ya bayyana cewa kula da lafiyar kwakwalwa da dawo da waɗanda abin ya shafa cikin rayuwa ta yau da kullum, ba su damar samun adalci da kuma farfaɗo da al’ummomin da hare-haren suka ɗaiɗaita, duk muhimman ɓangarori ne na yaƙin da ƙasar ke yi da matsalar tsaro.

Laka ya kuma jaddada muhimmancin kare shaidu da waɗanda abin ya shafa daga barazana, tsoratarwa ko ɗaukar fansa. A cewarsa, samar da ingantaccen tsarin kariya ga shaidu zai ba su damar bayar da bayanai da kuma halartar bincike da zaman kotu cikin aminci.

Mai kula da cibiyar ya yaba da haɗin gwiwar da aka samu tsakanin Babbar Kotun Tarayya, Ma’aikatar Shari’a, lauyoyin kare waɗanda ake tuhuma, hukumomin tsaro da Hukumar Taimakon Shari’a. Ya kuma amince da irin gudunmawar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, suka bayar wajen samun nasarar gudanar da shari’o’in.

A cewar Laka, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da haɗa ayyukan soji da na tsaro, gurfanar da masu laifi a kotu, matakan rigakafi da haɗin gwiwar hukumomi wajen yaƙi da ta’addanci. Ya ce babban burin wannan ƙoƙari shi ne kare rayukan al’umma, tallafa wa yankunan da hare-haren suka shafa da kuma kiyaye muhimman haƙƙoƙin bil’adama.

Yana da kyau a fahimci cewa dokokin Nijeriya kan yaƙi da ta’addanci ba su taƙaita hukunta waɗanda ke shiga hare-haren ta’addanci kai tsaye ba. Dokar Hani da Rigakafin Ta’addanci ta shekarar 2022 ta haramta nau’o’in tallafi da dama da ake bai wa ƙungiyoyin ta’addanci, ciki har da samar musu da kuɗaɗe, taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu da kuma wasu shirye-shiryen aikata laifuffuka.

Saboda haka, duk mutumin da ya san cewa yana taimaka wa ƙungiyar ta’addanci ta hanyar da doka ta haramta, zai iya fuskantar shari’a, ko da kuwa tallafin da ya bayar bai da alaƙa kai tsaye da wani hari da aka kai. Misali, laifuffukan da suka shafi samar da tallafi ko kaya ga ’yan ta’adda na iya jawo hukuncin ɗaurin shekaru masu yawa a gidan yari.

A sakamakon haka, gwamnatin tarayya ta faɗaɗa yaƙin da take yi da ta’addanci, ta hanyar mayar da hankali kan hanyoyin kuɗaɗe da dabaru da ƙungiyoyin ta’addanci ke amfani da su wajen ci gaba da gudanar da ayyukansu. Wannan ya bayyana a yadda aka saurari shari’o’in da suka shafi samar da kuɗaɗen ta’addanci guda 201 a sabon zagayen shari’o’in.

Wannan mataki yana da matuƙar muhimmanci, domin kuɗaɗen tallafi ne ke bai wa ƙungiyoyin ta’addanci damar sayen makamai, ɗaukar sabbin mambobi, jigilar mayaƙansu da kuma ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Daraktan Masu Gabatar da ƙara na Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, Rotimi Oyedepo, ya bayyana cewa gwamnati na nan daram kan manufarta ta gurfanar da mutanen da akwai isassun hujjojin da za su tabbatar da zargin da ake musu. Ya bayyana cewa an shigar da tuhume-tuhume kusan 1,047 a sabon zagayen shari’o’in.

Oyedepo ya yi bayanin cewa masu gabatar da ƙara na aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin bincike da sauran cibiyoyi domin tantance bayanan shari’a da hujjojin da ke cikin kowace takarda kafin kai ƙara gaban kotu.

Ya ce idan aka gano cewa hujjojin da ake da su ba su wadatar ba, ana sake duba shari’ar ta fuskar doka maimakon a gaggauta gurfanar da wanda ake zargi. Daraktan ya bayyana cewa idan bincike bai tabbatar da zargin da ake yi wa mutum ba, ana iya ba da shawarar a sake shi tare da samar masa da tsarin gyaran hali da dawo da shi cikin al’umma idan hakan ya dace.

Ya kuma jaddada cewa alhakin yanke hukunci kan ko masu gabatar da ƙara sun tabbatar da zarge-zargen da ake yi wa wanda ake tuhuma bisa ƙa’idar shari’a yana hannun ɓangaren shari’a ne, wato kotuna.

Jaridar Blueprint ta nuna gamsuwarta da yadda ɓangaren gurfanar da masu laifi a kotu ya zama wani ginshiƙi a tsarin yaƙi da ta’addanci na Nijeriya. Gaskiyar cewa gwamnatin tarayya ta samu ƙarfin ikon siyasa da ƙudurin da ya kai ga tabbatar da hukuncin laifin ta’addanci kan mutum 2,512, ba wai kawai tana nuna aniyar gwamnati ta kawar da ta’addanci da sauran laifuffukan tashin hankali daga Nijeriya ba ne, har ma tana wakiltar wata gagarumar nasara da ba a taɓa samun irinta ba tun bayan ɓarkewar rikicin Boko Haram a shekarar 2009.

Duk da wannan nasara, muna kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da cewa dukkan hukunce-hukuncen kotuna, musamman waɗanda suka shafi manyan laifuffuka, sun yi daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulki da kuma ingantattun ƙa’idojin shari’a.

Haka kuma, akwai buƙatar gwamnati ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin masu gudanar da bincike, masu gabatar da ƙara, hukumomin tattara bayanan sirri kan harkokin kuɗi da sauran hukumomin tsaro, domin gano hanyoyin sadarwar ƙungiyoyin ta’addanci da kuma tarwatsa su tun kafin su aikata munanan laifuffuka.

Wannan hanya za ta taimaka wajen daƙile ayyukan ta’addanci da sauran nau’o’in tsattsauran ra’ayi tun kafin su zama babbar barazana ga zaman lafiya da tsaron ƙasa.

By ukarofi

Leave a Reply