Daga GAMBO ISA a Abuja
Mai Martaba Sarkin Jama’are, Alhaji Ahmad Nuhu Wabi, MNI, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da shugabannin ƙasashen Arewa maso Gabas da ke riƙe da makamai da su mayar da hankali wajen samar da muhimman abubuwan more rayuwa da za su amfani al’ummar yankin.
Sarkin ya bayyana cewa al’ummar Arewa maso Gabas na buƙatar tallafi daga Gwamnatin Tarayya, musamman a ɓangaren kiwon lafiya, inda ya ce asibitoci da dama ba su da isassun magunguna, kayan aikin jinya da kuma likitocin da za su kula da marasa lafiya.
Ya bayyana damuwarsa kan yadda mata da yara ƙanana ke rasa rayukansu yayin haihuwa da kuma matsalolin rashin ingantaccen tsarin kula da lafiya. Saboda haka, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta kawo ɗaukin gaggawa ga ɓangaren kiwon lafiya a yankin.
Mai Martaba Sarkin Jama’are ya kuma bayyana cewa hanyoyin sufuri da dama a Arewa maso Gabas ba su da inganci, lamarin da ke jefa al’umma cikin wahala yayin tafiye-tafiye.
Ya kawo misalin hanyar Maiduguri zuwa Dikwa zuwa Ngala, da kuma hanyar Gombe zuwa Funakaye, da Gombe zuwa ƙaramar hukumar Biu ta Jihar Borno, daga Miringa a Biu zuwa Yadin Buni a Gujba ta Jihar Yobe.
Haka kuma, ya ambaci hanyoyin da suka haɗa Jihar Taraba da Gombe, da kuma hanyar Mubi a Jihar Adamawa zuwa Biu a Jihar Borno, inda ya ce rashin ingancin waɗannan hanyoyi na jefa matafiya cikin wahala, har wasu lokuta su shafe sa’o’i masu yawa ko ma kwana guda suna tafiya.
Sarkin ya kuma nuna damuwa kan rashin wadataccen abinci mai kyau da gina jiki da al’ummar yankin ke fuskanta, yana mai cewa ya kamata a ɗauki matakai domin tabbatar da cewa jama’a sun samu abincin da zai taimaka wajen inganta lafiyarsu.
Mai Martaba Sarkin Jama’are ya yi kira ga shugabannin yankin Arewa maso Gabas da masu riƙe da makamai da su ba da fifiko ga ayyukan da za su amfani al’umma, tare da nuna kishin jama’a da tausayawa wajen magance matsalolin da suke fuskanta.
A ƙarshe, Sarkin ya miƙa godiyarsa ga Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, bisa gudunmawar da yake bayarwa.
