Talakawa na amfana da sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu, inji Idris

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, ya ce dukkan ’yan Nijeriya na amfana da sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa, ba tare da la’akari da matsayinsu na zamantakewa ko siyasa ba.

Idris ya musanta ra’ayin da ke cewa wasu tsiraru ne kawai ke amfana da sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa, inda ya jaddada cewa talakawa ma na cin moriyar waɗannan sauye-sauye.

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin wani taron wayar da kan kafafen yaɗa labarai kafin ƙaddamar da kundin manufofin jam’iyyar APC a hukumance gabanin zaɓen 2027. Ya ƙara da cewa ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da hukumomin tantance ƙimar tattalin arziki sun yi tsokaci mai kyau kan tattalin arzikin Nijeriya.

Ya ce: “Sau da yawa mutane na cewa, ‘Eh, kuna cewa ana aiwatar da duk waɗannan sauye-sauye, amma mutane kaɗan ne kawai ke amfana da su.’ Sai na yi tambaya: Yayin da ake gyara hanyar Abuja zuwa Kano, ban san cewa akwai wanda ake buƙatar ya nuna katin shaidarsa domin tabbatar da cewa shi ɗan APC ne, ko attajiri ne, ko kuma yana cikin wani rukuni na musamman kafin ya bi hanyar ba.”

Idris ya kuma tunatar da masu shakkar nasarorin da Shugaba Tinubu ya samu a ɓangaren tsaro halin rashin tsaron da a baya ya addabi babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Ya ce: “Muna ganin kamar mun manta cewa idan ana shakkar ko Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana yin wani abu a kan matsalar tsaro, a baya tsakanin Abuja da Kaduna, inda nake zaune, an kai wani lokaci da mutum ba ya iya ɗaukar motarsa da makullinta ya kama hanya kawai.

“Mutum sai ya fara tambayar kansa: ‘Shin suna nan yau?’ Wato ina ’yan bindigar ko waɗanda ke tare mutane a kan hanya suke? Shin har yanzu suna nan?

“A yau, babu wanda yake yin irin wannan tambayar. Mutum zai ɗauki motarsa daga nan ya tafi Kano ba tare da tambayar ko ’yan ta’adda, ’yan bindiga ko masu garkuwa da mutane suna nan ba. Amma a baya ba haka abin yake ba,” inji shi.

Ministan ya ƙara da cewa sama da ’yan Nijeriya miliyan 1.6 da ke amfana da Asusun Tallafin Lamunin Karatu na Nijeriya (NELFUND) shaida ce da ke nuna cewa talakawa na amfana da sauye-sauyen gwamnatin Tinubu.

Ya ce: “Idan kuna neman misalin yadda waɗannan sauye-sauye ke shafar rayuwar talakawa, ku duba ’yan Nijeriya miliyan 1.6 da ke amfana da NELFUND. Ba daga wata duniya suka zo ba, ’yan Nijeriya ne da ke zaune a cikin ƙasar nan.

“Abin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu yake son tabbatarwa shi ne, babu dalilin da zai sa matashi ko budurwa da suka cancanci shiga makaranta, kuma suka samu gurbin karatu a babbar makaranta, su kasa yin karatun saboda iyayensu ko masu kula da su ba su da kuɗin biyan kuɗin makaranta da na gudanar da rayuwarsu.

“Saboda haka, idan ana neman misalin ’yan Nijeriya da ke amfana da wannan shiri, matasa miliyan 1.6 da iyayensu suna nan a matsayin misali,” inji shi.

Bagudu ya yi tsokaci

A nasa jawabin, Ministan Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi da Tattalin Arziki, Atiku Bagudu, ya ce manufofin sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ke aiwatarwa sun samo asali ne daga hangen nesa na dogon lokaci ga Nijeriya, da kuma ƙudurin magance matsalolin da gwamnatocin baya suka kasa warwarewa.

Ya ce ɓangaren kamfanoni masu zaman kansu ya amince da ci gaban da aka samu a ƙarƙashin wannan gwamnati, yana mai cewa gwamnati na ci gaba da mayar da hankali wajen tabbatar da cewa amfanin bunƙasar tattalin arziki ya isa ga talakawa.

Bagudu ya ce: “Shugaba Tinubu ya yi imanin cewa Nijeriya za ta iya zama ƙasa mai tattalin arzikin da ya kai dala tiriliyan biyu. Ya ɗauki matakai masu wahala domin samar wa ƙasar tushe mai ƙarfi. Sai dai kuma ya fahimci cewa akwai sauran ayyukan da ya kamata a yi domin tabbatar da cewa kowane ɗan Nijeriya, musamman iyalai masu ƙoƙarin neman abinci da sauran masu rauni, sun amfana da ci gaban tattalin arzikin.”

By ukarofi

Leave a Reply