Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta cire rajistar masu zaɓe marasa inganci guda 1,608,660 daga cikin kundin rajistar masu zaɓe na wucin gadi, bayan gudanar da bincike a faɗin ƙasar kan bayanan rajistar da aka tattara yayin aikin ci gaba da rajistar masu zaɓe na shekarar 2025/2026.
Rahoton News Point Nigeria ya ce hukumar ta kuma cire bayanan mutane 876 da aka tabbatar sun rasu, sannan ta gano wasu bayanan mutane 873 da suka rasu, waɗanda aka kuma goge daga rajistar. Hakan ya sa adadin waɗanda aka cire saboda sun rasu ya kai 1,749.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan (SAN), ne ya bayyana waɗannan alkaluma ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai kan sakamakon binciken rajistar masu zaɓe ta wucin gadi.
Ya ce hukumar ta karɓi bayanan rajistar mutane 11,088,238 daga matakai uku na aikin rajistar masu zaɓe na shekarar 2025/2026.
A cewarsa, tsarin tantance bayanan masu zaɓe ta hanyar na’ura mai suna Automated Biometric Identification System ya fara gano bayanan mutane 1,545,052 da ke buƙatar ƙarin bincike.
Sai dai Amupitan ya bayyana cewa gano bayanan mutum ta wannan na’ura ba yana nufin an tabbatar da cewa rajistarsa ba ta inganta ba. Ya ce kowane bayani ya bi ƙarin bincike da tantancewa kafin yanke hukunci a kansa.
An gudanar da aikin gyaran rajistar ne bayan koke-koke da ƙalubale da ’yan Nijeriya suka gabatar, sakamakon baje kolin kundin rajistar masu zaɓe na wucin gadi a faɗin ƙasar daga ranar 9 zuwa 15 ga Oktoban 2026.
Rajistar ta jawo suka bayan da wasu ’yan Nijeriya da ƙungiyoyin farar hula suka ce sun gano kura-kurai, ciki har da hotunan da ake zargin an ƙirƙira da fasahar AI, rajistocin da aka maimaita, sunayen da ba a saba gani ba da kuma bayanan mutanen da suka rasu.
Wasu daga cikin hotunan da ake zargi sun yaɗu a kafafen sada zumunta, lamarin da ya jawo damuwa kan sahihancin rajistar masu zaɓe da kuma yadda INEC ke tantance bayanan.
Bayan koke-koken, hukumar ta gudanar da bincike domin tantance waɗannan kura-kurai tare da cire bayanan da aka tabbatar ba su da inganci.
Amupitan ya kuma bayyana cewa an gano jami’an rajista 54 a jihohi 10 da ake iya ɗaukar matakin ladabtarwa a kansu, ciki har da gurfanar da su a gaban kotu, bisa zargin hannu a kura-kuran da aka gano yayin aikin.
INEC ta ce za ta wallafa ingantacciyar rajistar masu zaɓe a ranar 16 ga Disamban 2026, bisa tanadin dokar zaɓe.
