Tompolo da Dauda Lawal sun ƙaddamar da gangamin tallafa wa Tinubu a 2027

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU

Babban mai ɗaukar nauyin ƙungiyar ‘PBAT Door-to-Dooru ?Movement’, Cif Oweizide Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo, tare da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, sun yi kira ga masu kaɗa ƙuri’a a jihar da su zaɓi Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 domin ba shi damar ci gaba da ayyukan da ya fara.

An yi wannan kiran ne yayin ƙaddamar da reshen ƙungiyar a Jihar Zamfara, ranar Alhamis a Gusau, inda aka kuma gabatar da motoci 25 da za a yi amfani da su wajen wayar da kan al’umma da neman goyon baya ga sake zaɓen Shugaba Tinubu.

Motocin, waɗanda aka sanya wa na’urorin lasifika da allunan tallan yaƙin neman zaɓe, an tanade su ne domin taimaka wa mambobin ƙungiyar wajen isar da saƙonta ga al’ummomi daban-daban a faɗin jihar.

Kestin Pondi, Manajan Daraktan kamfanin Tantita Security Services, ne ya wakilci Tompolo a wajen taron ƙaddamarwar.

Da yake magana a madadin Tompolo, Pondi ya bayyana cewa ƙungiyar ta zo Jihar Zamfara ne domin tallafa wa ƙoƙarin gwamnatin jihar da kuma tara goyon bayan jama’a ga Shugaba Tinubu ta hanyar ziyartar gidaje da tattaunawa kai tsaye da al’umma.

Ya ce: “Za a miƙa motocin ga Gwamna Dauda Lawal domin ya kula da su, kuma za a yi amfani da su wajen yaɗa saƙon ƙungiyar a faɗin jihar.”

Ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da su yi haƙuri dangane da sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa, yana mai cewa zai ɗauki lokaci kafin amfanin waɗannan sauye-sauye ya kai ga gidajen jama’a.

A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya nuna godiyarsa ga Tompolo da ƙungiyar bisa goyon bayan da suke bayarwa ga yaƙin neman sake zaɓen shugaban ƙasar, tare da tabbatar da cewa Jihar Zamfara za ta ci gaba da goyon bayan Shugaba Tinubu.

Tun da farko, babban mai gudanar da ayyukan ƙungiyar a matakin ƙasa, Sunday Adekanbi Asuku, ya yaba wa shugabannin reshen ƙungiyar na Jihar Zamfara bisa ƙoƙarin da suke yi.

Asuku ya bayyana cewa: “Nijeriya tana da mutanen da suka dace a muƙaman shugabanci, a matakin, tarayya da na jihohi,” inda ya bayyana halin da ake ciki a matsayin wani yanayi na musamman da ba a taɓa ganin irinsa ba tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya.

By ukarofi

Leave a Reply