
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), ta ce ta ƙwato sama da Naira biliyan 5.3 daga asusun ƙananan hukumomi a jihohi guda bakwai da Babbar Birnin Tarayya Abuja, biyo bayan nazari da ta yi kan rahoton kuɗaɗensu.
ICPC tana kuma aiki tare da Hukumar Kula da Ci-gaban Fasahar Sadarwa (NITDA) domin tabbatar da cewa baki ɗaya ƙananan hukumomi 774 na Nijeriya sun wallafa rahotannin kuɗaɗensu da wasu muhimman bayanai a yanar gizo.
A wata sanarwa da Kakakin ICPC, John Odey ya fitar, ya ce shugaban hukumar, Dakta Musa Aliyu ya bayyana haka ne a Jihar Nasarawa yayin ƙaddamar da shafin ƙananan hukumomi na yanar gizo na ICPC-NITDA. Dakta Aliyu ya ce, shirin, wanda aka fara a Nasarawa, an shirya shi ne da nufin ƙarfafa tsare gaskiya da adalci a matakin tushe ta tsarin bayyana wa al’umma dukkan bayanan da haƙƙi ne a sanar da su ta digital.
Ya bayyana cewa, ƙwato sama da biliyan 5.3bn ya nuna girman haɗarin kuɗi a matakin ƙananan hukumomi da muhimmancin kariya ga aikata rashawa. “ICPC ta ƙwato sama da biliyan N5.3bn daga nazarin asusun ƙananan hukumomin jihohi bakwai da Babban Birnin Tarayya, kuma a yanzu tana ƙoƙarin samar da tsarin da za a riƙa sanya ƙananan hukumomi a sassan ƙasar halin wallafa kuɗaɗensu a intanet,” inji shi.
A cewarsa, hukuncin Kotun Ƙoli na bai wa ƙananan hukumomi ‘yancin cin gashin kai da ba su kuɗaɗen da aka ware musu kai-tsaye, ya ƙara nuna buƙatar tabbatar da gaskiya da adalci wajen gudanar da dukiyar al’ummar ƙasa. Ya kuma ce, za a tsara shafukan ne ta yadda za su riƙa wallafa kasafinsu, kuɗaɗen da aka ware, kuɗaɗen shiga, rahoton kuɗi, basusuka, ababen da aka siya, albarkatun ɗan-adam da hanyoyin damawa da al’umma da kuma tsarin fallasa.
Ya ce, fagagen za su bai wa mazauna, ‘yan jarida da cibiyoyin sanya ido damar kula da halin kuɗaɗe da gano wasu kurakuran kuɗi da ka iya faruwa, yana mai ƙarawa da cewa NITDA za ta samar da kayan fasahar da ake buƙata domin tabbatar da aiwatar da tsarin bisa inganci.
Kazalika, ya yi kira ga ciyamomin ƙananan hukumomi da su naɗa jajirtattun jami’an da za su riƙa kula da shafukan da tabbatar da an wallafa dukkan bayanan da ake buƙata daidai kuma a kan kari. A cewarsa, wannan salo ne na daƙile rashawa da aka samar a madadin zargin mutane ba tare da hujja ba.
