
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Juma’a Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta yanke hukuncin cewa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ba ta da ikon soke takarar wani ɗan takara da ke neman zaɓe, inda ta umarce ta da ta gaggauta dawo da sunan ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Ogun, Ladi Adebutu cikin jaddawalin ‘yan takara a cikin kwana guda.
Haka kuma kotun ta ce INEC ta taka dokar da ta ba wa Adebutu damar jin ba’asinsa ta hanyar cire sunansa a jaddawalin ‘yan takara, inda ta bayyana hakan a matsayin abin da aka yi ta haramtacciyar hanya da ya saɓa wa doka.
Mai Shari’a Peter Lifu, wanda ya gabatar da hukuncin, ya ce ikon soke sunan ɗan takara bayan an aike wa hukumar zaɓe ya raja’a ne a hannun Babbar Kotun Tarayya ko kuma Babbar Kotun Jiha. Wannan hukunci ya biyo bayan watsi da ƙorafin INEC ga kotun na neman korar ƙorafin da PDP ta shigar mata kan al’amarin.
Yayin watsi da ƙorafin na INEC, alƙalin ya ce bayan nazari kan ƙorafe-ƙorafen da PDP ta shigar, ya gano cewa babu wata matsala da za ta sanya su tabbatar da matakin cire Adebutu da hukumar ta yi sakamakon cewa an bi hanyoyin da suka dace wajen gabatar da shi. Adebutu acikin ƙorafin nasu, ya bayyana cewa ya nemi takarar gwamnan Ogun a 2019 kuma shi ne ɗan takarar PDP a zaɓen 2023. Sannan, mai shari’ar ya ce, an gwabza da Adebutu a zaɓen fidda gwanin ɗan takarar gwamna na 2027, kuma PDP ta wallafa sunansa a ranar 29 ga Agusta, 2026 ba tare da wani ƙalubale ba a game da ayyana shi a matsayin ɗan takara.
Adebutu ya shigar da ƙara ne bayan INEC ta wallafa sunayen ‘yan takarar gwamna a watan Oktoba, inda aka ga babu shi a ciki duk da cewa bai ayyana janyewa ba daga takara. A nata ɓangaren, INEC ta ƙalubalanci PDP kan rashin sahihancin Adebutu na zama mamban PDP duk da cewa wani mai suna Bature ya kare hakan da cewa shi ne Sakataren Shirye-shiryen PDP a lokacin da suka miƙa INEC jaddawalin mambobinsu, wanda a ciki akwai sunan ɗan takarar gwamnan.
