
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jaruman Masana’antar Hollywood ta ƙasar Amurka, Susan Sarandon da Hannah Einbinder suna cikin masu zanga-zangar da ‘yan sanda suka tsare a ranar Alhamis, yayin nuna adawarsu ga Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu gabanin jawabinsa a taron Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD).
Ƙungiyar Jewish Voice for Peace ce ta shirya gangamin, inda aka samu halartar ɗaruruwan mutane a wajen hedikwatar MƊD. An ga yadda jama’a suka riƙa nuna adawarsu da zuwan Netanyahu taron da kuma nuna rashin goyon bayansu ga ayyukan sojojin Isra’ila a Gaza.
Haka kuma, an hangi Sarandon, wadda ta taɓa lashe kyautar Oscar kan finafinanta na Thelma & Louis da Dead Man Walking, ɗauke da sarƙar ɗaure mai laifi da ‘yan sanda New York suka maƙala mata, yayin da suke ƙoƙarin dakatar da masu zanga-zangar.
Sannan, an kama Einbinder, tauraruwar fim ɗin talabijin mai dogon zango na Hacks. Wata ɗauka ta nuna yadda jami’an tsaro suke mata rakiyar ficewa daga dandazon masu zanga-zangar bayan ta shiga sahun ‘yan waje da zauren majalisar.
Sauran jaruman da aka gani acikin gangamin sun haɗa da Cynthia Nixon, Elliot Page da Indya Moore, da kuma ‘yan barƙwanci kamar su Caleb Hearon da Sarah Sherman, sai kuma mawaƙa Lucy Dacus da Julien Baker.
