Daga UMAR GARBA a Katsina
Rundunar Operation Fansan Yamma na rundunar sojojin haɗin gwiwa ta Arewa maso yamma sun kama wasu mutane uku da ake zargi da tallafawa ’yan ta’adda da kuɗaɗe.
Rundunar ta kuma ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Faskari ta Jihar Katsina.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta bayyana cewa, a ranar 24 ga watan Satumba 2026, dakarun Sector 2 sun tare wasu mutane uku da ke kan babur, inda aka gano suna ɗauke da Naira miliyan 2.7 da ake zargin kuɗin fansa ne, da wayoyin hannu guda uku, domin miƙa su ga wani jagoran ’yan ta’adda ta hannun wasu masu shiga tsakani.
Haka kuma rundunar ta ce, a ranar 25 ga Satumba, dakarun sun yi artabu da ’yan ta’adda a Faskari, lamarin da ya tilasta musu tserewa, inda aka ƙwato bindigar AK-47 guda ɗaya, harsasai 30 da babur guda.
A wani samame da aka gudanar a ranar, dakarun sun kuma ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su, ciki har da maza 12 da mata biyu, waɗanda aka yi garkuwa da su daga ƙauyukan Anguwan Miko da Tafoki.
Rahotanni sun ce ’yan ta’addan sun bar mutanen ne bayan sun hango dakarun sojin da ke tunkararsu. Daga bisani aka miƙa waɗanda aka ceto ga hukumomin ƙaramar hukumar Faskari domin ɗaukar matakin da ya dace.
