
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ƙoƙarinta na tallafa wa ayyukan hukumomin tsaro wajen yaƙi da ayyukan ‘yan bindiga da wasu miyagun laifuka, Gwamnatin Jihar Sakkwato ta amince da ƙudirin neman kafa Dokar Haramta Ayyukan ‘Yan bindiga a Jihar Sakkwato ta 2026.
Haka kuma, gwamnatin jihar ta bayar da kwangilolin siyo ƙarin wasu motoci guda 30 ƙirar Toyota Hilux akan jimillar kuɗi Naira 1,592,250,000.
An ɗauki wannan mataki ne a zaman majalisar zartarwar jihar karo na 8 da ta saba, wanda Gwamna Ahmed Aliyu ya jagoranta, a cewar wata sanarwa da Daraktan yaɗa labaran gwamnan, Abubakar Bawa ya fitar a ranar Asabar. Ya ce, motocin ƙari ne akan sama da irinsu guda 200 da motocin yaƙi 62 da aka siyo da fari tare da raba su ga hukumomin tsaro a jihar domin ƙarfafa ayyukansu akan yaƙi da ta’addanci.
Ya bayyana cewa, gwamnatin Sakkwato ta kuma amince da ƙudirin kafa Sokoto State Banditry Special Prohibition Law, 2026 a matsayin matakin hukunci ga ayyukan ‘yan bindiga a jihar. Bawa ya ƙara da cewa majalisar ta kuma amince da siyan motocin Mitsubishi Canter guda 10 akan Naira miliyan 776.3 da kuma Toyota Hilux vans biyu akan miliyan N122.
Kazalika, majalisar ta amince da Naira miliyan 118.1 a matsayin kuɗin kammala gina shaguna 30 a tashar mota ta hukumar sufuri jihar. Sauran da aka amince da su a zaman sun haɗa da gyaran wasu wurare da suka lalace a Makarantar Sakandare ta Kimiyya da ke Gwadabawa, wanda zai lanƙwame Naira miliyan 844.6. Har ila yau, ta amince da miliyan 182.2 a matsayin kuɗin gyaran rukunin gidajen ɗakunan kwanan ɗalibai na Koko Technical College, Farfaru.
Akwai kuma gyaran ajujuwan, sashe, hanyoyin zuwa da wasu gine-gine na makarantar Ahmadu Bello Academy, Farfaru, wanda aka ware wa miliyan N123.9. Sannan, gwamnatin ta ce ta ware Naira 168.6m domin gina rukunin gidaje takwas a Shehu Shagari College of Education, kuma miliyan 132.4 don siya kayan ɗakin karatu ga Shehu Shagari University of Education.
Bugu da ƙari, majalisar ta amince da miliyan N550.4 don gina sashen hukumar gudanarwar Aliyu Magatarda College of Technology and Advanced Studies. Sai kuma N234,674,481 ga gina babbar katanga a asibitin dabbobi ta Veterinary Specialist Hospital.
