Sojoji sun yi wa ‘yan bindiga 240 luguden wuta a hanyar zuwa Kebbi daga Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun tsaro na Bataliya ta 3 ƙarƙashin Sashe na 8 na Rundunar Sojin Nijeriya da haɗin-gwiwar jami’an Atisayen FANSAN YAMMA sun yi musayar wuta da wani dandazon ‘yan bindiga a yankin iyakar jihohin Zamfara da Kebbi.

Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan bindigar, waɗanda aka ƙiyasta adadinsu zai kai guda 240, sun ɗauko hanya ne daga yankin Sangeko Gap da ke Jihar Zamfara kana suka nufi birnin Makuku a Jihar Kebbi.

A cewar majiyoyin tsaro, ‘yan bindigar sun rabu ne kashi uku a lokacin suka tunkari yankin a wani yanayi na salon kai farmaki.

Wannan al’amari ya haifar da fargaba acikin al’umma, wanda ya sa wasu mazaunin suka fara ƙaura daga gidajensu zuwa wasu yankuna masu tsaro yayin da sojojin suke ƙoƙarin daƙile shirin nasu.

Atisayen dakarun ya haɗa da ruwan wuta daga sojojin ƙasa da jami’an ‘yan sanda da kuma ƙarin tallafi daga dakarun sama na FANSAR YAMMA.

An ruwaito cewa, jami’an tsaron sun yi ƙoƙarin hana ‘yan bindigar shiga ƙauyukan da ke kewayen yankin wajen takalar su yayin zirga-zirgarsu a yankin iyakar.

Rahotanni sun bayyana cewa, a yayin arangama da tsananin ɓangarorin biyu, dakarun tsaron sun yi nasarar halaka sama da ‘yan ta’adda 200.

Haka kuma, an shawarci mazauna da su zauna a ankare tare da yin biyayya ga umarnin jami’an tsaro.

By Babaji

Leave a Reply