20
Apr
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa, ƙiris ya rage madugun jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya dawo jam’iyyarsu ta APC, saboda ruwa ya kusa ƙare wa ɗan kada. Ganduje ya bayyana hakan ne yana mai cewa jam’iyyar NNPP ta mutu murus, kuma jana’izarta kaɗai suke jira a gudanar a nan kusa. Dakta Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin ziyarar da wata ƙungiya mai goyon bayan Shugaba Bola Tinubu (TSG) ta kai sakatariyar APC ta ƙasa da ke Abuja. Ganduje ya ce, APC a kodayaushe…