Masu burin kassara PDP ke adawa da shugabancin Umar Damagun – Biniya Gabari

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An zargi wasu ‘yan majalisar wakilai 60 na PDP da wasu ƙungiyoyin da ke nuna adawa da shugabancin Ambasador Umar Iliyasu Damagun a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar na ƙasa, da kasancewa karnukan farauta ne da ake amfani da su wajen yin zagon ƙasa ga ci gaban jam’iyyar.

Shugaban haɗakar matasa na jam’iyyar na ƙasa PDP Youths Collation Movement Hon. Biniya Yahuza Gabari ya bayyana haka.

Ya ƙara da cewa ‘ya’yan  jam’iyyar su ke ƙalubalantar shugaban riƙo na jam’iyyar PDP na da   ɓoyayyen manufa na ruguza jam’iyyar ne, ganin yanda yanzu take samun ƙarin goyon baya a ƙarƙashin jagorancin Damagun.

Kodinetan haɗakar ƙungiyoyin matasan jam’iyyar PDP na ƙasa Hon. Biniya Yahuza  ya ce babu wani zargi na ƙarya ko cin zarafi da zai hana shugaban riƙo na jam’iyyar PDP na ƙasa. Ambasador Umar Damagun cigaba  ƙoƙarinsa na Gina  ci gaban jam’iyyar da haɗa kan ‘ya’yanta.

Ya ce bai dace ‘ya’yan da suka ci zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP  a yi amfani da su wajen yi wa Shugabancin Jam’iyyar zagon ƙasa a yanzu ba.

Shugaban riko na ƙasa Damagun ba shi ne Shugaban Jam’iyyar ba a zaɓen Shugaban ƙasa na 2023, amma a lokacin PDP ta yi nasara a   zaɓen shugaban qasa a jihar sa ta Yobe, yayin da waɗanda ke adawa da shi a yanzu  basu iya  kawo jihohinsu ba.

Hon. Biniya Yahuza Gabari ya nuni da  cewa shi a jiharsu ta Jigawa duk da makudan kuɗaɗe  N800,000,000 da aka bayar a lokacin zaɓen shugaban ƙasa, PDP ba ta iya nassra ba.

Haka zalika a Jihar Kano an baiwa PDP N900,000,000 amma jam’iyyar ta gaza nasarar kujerar shugaban ƙasa ƙarƙashin jagorancin waɗanda yanzu sune  ke adawa da shugabancin  ƙasa na yanzu.

Gamayyar ƙungiyoyin matasa na PDP na  ƙasa sun yi kira ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a 2023.

Atiku Abubakar ya yi watsi da waɗanda suka  kewaye shi  suna  ba shi bayanan da ba  na daidai ba.Sune mutanen da   suka gaza   kai  jam’iyyar PDP  ga nasara a zaɓen 2023.

Ya ce a matsayinsu na ƙungiyar matasa a jam’iyyar PDP ba za su goyi bayan duk wani zagon ƙasa da wasu da suke fakewa da sunan yan  jam’iyyar ne, suna kitsa zagon qasa ga irin ƙoƙari da shugaban riƙo na jam’iyyar na ƙasa Ambasador Umar Iliyasu Damagun yake na haɗa Kai da bunƙasa cigaban jam’iyyar ba.

Hon. Biniya Yahuza Gabari ya buƙaci ‘yan jam’iyyar PDP masu kishi su ci gaba da bai wa shugaban jam’iyyar na riqo na ƙasa Hon. Amb. Umar Iliyasu Damagun goyon baya da haɗin kai domin cimma nasarar  jagorantar babbar jam’iyyarsu  ta  lPDP zuwa ga nasara.