Akwai masu zuga ni na binciki Gwamna Abba – Muhuyi Magaji

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), Malam Muhuyi Magaji, ya ce wasu mutane na bincikensa domin ƙoƙarin tunzura shi ya binciki Gwamna Abba Kabir.

Magaji ya bayyana haka ne yayin da ya halarci shirin Sunrise Daily na gidan talabijin Channels ranar Talata, 16 ga watan Afrilu, 2024.

Jami’in ya ce, ya fara binciken shugaban jam’iyyar APC na qasa, Dr. Abdullahi Ganduje, a lokacin da yake kan kujerar gwamnan Jihar Kano.

Shugaban hukumar yaƙi da rashawar, wanda ya jaddada cewa ya zama tilas jami’an gwamnati su kiyaye bin doka da oda, ya ce ba su matsu dole sai sun maka Ganduje a kotu ba.

Da aka tambaye shi ko zai kuma binciki gwamna mai ci, Abba Kabir Yusuf, Magaji ya ce, “Abin da mutane ke ƙoƙarin ingiza ni a kai kenan.”

Magaji ya bayyana cewa ya sani sarai wasu mutane a ɓangarori daban-daban suna masa kallon mutum mai taurin kai.

Amma a cewarsa, duk da kotu ta yanke cewa laifin satar kuɗin baitul-mali laifi ne na ƙasa amma hukumar yaƙi da rashawa ta Kano tana da haƙƙin bincikar gwamnatin Ganduje. 

A halin da ake ciki kuma, za a gurfanar da Ganduje a babbar kotun Kano ranar Laraba 17 ga Afrilu, 2024, bisa tuhumar da ake masa na cin hanci da rashawa da karkatar da wasu kuɗaɗe.

Daga cikin laifukan da ake zargin Ganduje har da tuhumar karɓar cin hancin Dala Amurka 413,000 da kuma Naira Biliyan 1.38.

Ganduje, wanda ya yi gwamnan Kano tsakanin watan Mayun 2015 zuwa Mayu 2023, yana fuskantar matsin lamba ya yi murabus daga muƙamin shugaban APC na ƙasa.