Dalilin da ya sa na daina saka baki a siyasar Nijeriya – Rotimi Amaechi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Ministan Sufuri a Nijeriya Rotimi Amaechi ya ce an daina jin ɗuriyarsa ne a fagen siyasar Nijeriya saboda “babu wani sabon abu” da zai faɗa.

Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya riƙe muƙamin minista a gwamnatin tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2022, bayan ya mulki jihar tasa a Kudancin Nijeriya tsawon shekara takwas.

“Babu wani sabon abu kwatakwata,” inji ɗan siyasar wanda ya nemi takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC mai mulki cikin hira ta musamman da BBC.

“Abubuwan da ake so na yi magana a kan su suna nan kuma tun shekarun 1970 aka fara magana a kansu. Talauci, yunwa, rashin ingataccen ilimi, fashi, sata, cin hanci da rashawa, duka suna nan. Akwai abin da ya sauya ne?”

Haka nan, Amaechi ya riƙe muƙamin kakakin majalisar dokoki ta jihar Ribas mai arzikin man fetur daga 1999 zuwa 2007.

Yana cikin gwamnonin da suka kafa sansanin tawaye a jam’iyyar PDP mai mulkin Nijeriya a lokacin da yake gwamna, inda suka yaƙi Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, abin da ya kai ga faɗuwar gwamnatin a zaɓen shugaban ƙasa na 2015.

Ɗan siyasar mai shekara 59 na cikin mutum 23 da suka nemi tsayawa takarar shugaban ƙasa a APC, zaɓen da Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara.

Da aka tambaye shi ko don ya faɗi zaɓen fitar da gwani ne a takarar shugaban ƙasa shi ya sa yake faɗar matsaloli, Amaechi ya ce ya nemi takara ne saboda ya sha goyon bayan mutanen da suka gaza gyara Nijeriya.

“Na shiga takara ne saboda na goya wa mutane da yawa baya bayan sun yi min alƙawarin cewa za su sauya ƙasar nan amma kuma ba su yi hakan ba.

“Buhari ya yi mani alƙawarin zai gyara ƙasar nan. Jonathan ya yi mani alƙawarin gyara ƙasa. Daga baya na yi tunanin ko dai ni ne ban ga sauyin ba, ko kuma lallai akwai matsala.

“Sai na ce me ya sa ba zan jarraba ba. Ba ina cewa Buhari da Jonathan sun gaza ba ne, ni dai ina ganin lallai ya kamata a yi wani abu. Shi ya sa na nema [takarar].”

Rotimi Amaechi ya kwatanta rayuwar da yake ciki a yanzu bayan barin mulki a matsayin “nutsattsiya maras hayaniya”.

Ya ce a lokacin da yake minista sai ƙarfe “12:00 ko 2:00 na dare nake barci kuma na tashi 6:00 na safe don ganawa da jama’a”.

Ya ce: “Amma a yau mutumin da na fara haɗuwa da shi ita ce mahaifiyata. Ita kaɗai ce za ta iya sakawa na sauko daga bene idan ta zo.

“Yanzu hankalina a kwance, ba hayaniya, ba na gaggawar zuwa wani wuri, ko kuma mutanen da ke zuwa tambayoyi ko neman agaji.

“Ban ce ‘yan siyasa ba su zuwa ba, amma dai sun ragu sosai ba kamar da ba.”