An tsinci gawar jami’in ɗan sanda a gidansa a Maiduguri

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Al’ummar Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, sun samu kansu a cikin wani yanayi yayin da aka tsinci gawar wani sifeton ’yan sandan a gidansa.

Marigayi jami’in (da aka sakaya sunansa) da ke aiki a sashin Gwange na rundunar ’yan sandan jihar Borno an gansa ne kwanaki uku da suka wuce kafin a gano gawarsa a gidansa da safiyar Asabar.

Maqwabtansa a Layin Bayan, unguwar Wulari Jerusalem a Maiduguri, sun ɗaga murya wajen kiransa a lokacin da suka lura ya kulle ƙofarsa ta baya, amma wani ɗoyi na fitowa daga gidan.

Nan take aka kai rahoton lamarin ga rundunar ’yan sandan jihar Borno, inda aka tura wasu jami’ai zuwa wurin.

Wata majiya ta ce; “A safiyar yau ne mutanen da ke harabar gidan suka ga wani ɗoyi na fitowa daga gidansa; ƙofarsa a rufe daga baya.

“Mutanen ’yan sanda daga Metro da Gwange Dibision sun zo ne don karya ƙofa kuma an tsinci gawar sa a tsakar ɗakin kwanansa.”

Hukumomin ’yan sanda a jihar dai ba su fitar da wata sanarwa ba game da lamarin har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Wannan lamari dai ya zo ne kwanaki 10 bayan da aka tsinci gawar wani mataimakin kwamishinan ’yan sanda da ke aiki a sashin binciken manyan laifuka da bincike na rundunar ’yan sandan Jihar Legas, Gbolahan Oyedemi a ranar Litinin a gidansa da ke unguwar Ogbomoso a Jihar Oyo, wanda labarin hakan shima ya ɗaga hankulan al’umma.

Oyedemi ya kasance mai taimaka wa marigayi tsohon gwamnan jihar, Adebayo Alao-Akala, a tsawon watanni 11 da ya yi yana gwamna a shekara ta 2006

By Editor