Yadda tuhume-tuhume suka kaure tsakanin Abba da Ganduje

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Tataɓurza, musayar yawu da kuma tayar da ƙura irin na siyasa sun kunno kai a Jihar Kano tsakanin  zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-gida) da kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Shugaban Jam’iyyar APC ta Ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Gumurzun ya fara ne daidai lokacin da Jam’iyyar APC reshen mazavlɓar Ganduje da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano ta dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje. 

Mai bai wa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a a mazaɓar Ganduje, Haladu Gwanjo, ne ya sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar a wani taron manema labarai da a ka yi a Kano ranar Litinin.

Gwanjo ya bayyana cewa matakin dakatar da Ganduje daga jam’iyyar ya faru ne saboda zargin da gwamnatin Kano take masa na aikata rashawa da wadaƙa da kuɗaɗe.

Sai dai kuma Shugaban Jam’iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas ya ce waɗanda suka dakatar da tsohon Gwamnan Ganduje ba ‘yan APC ba ne, inda ya ce za su ɗauki mataki kan ɓangaren da ya sanar da dakatar da tsohon gwamnan na  Kano kuma shugaban jam’iyyar APC ta ƙasa na riƙo, Abdullahi Umar Ganduje.

Shugaban na APC ya yi zargin cewa waɗanda suka dakatar da Ganduje makusanta ne ga wasu masu riƙe da muƙamai a gwamnatin jihar da NNPP ke mulki.

Ya shaida cewa sun duba jerin sunayen ‘yan jam’iyyar na mazaɓar Ganduje, “mutum 27 ne kowace mazaɓa, mun duba a cikin su gaba ɗaya babu ko ɗaya da yake a cikin shugabanni.”

A cewarsa, jami’in da aka ce ya sanar da dakatar da Gandujen, Haladu Gwanjo, ya ce zai je kotu ya nemi haƙƙinsa saboda an zalunce shi.

Abdullahi Abbas ya bayyana cewa “wannan ba abin da ya haɗa shi da jam’iyyarmu, wannan tsari ne na gwamnatin jihar Kano da jam’iyyarsu ta kayan gwari suka shirya, ina tunanin wannan ita ce hanyar da za su ci mutuncin dak,ta Ganduje,” a cewar shugaban APC na Kano.

Ana tsaka da wannan danbarwa ne dai a ranar Larabar da ta gabata sai ga babbar Kotun Jihar Kano mai Lamba 4 dake zaman ta akan titin Mila, ta tabbatar da dakatarwar da wasu shugabannin Jam’iyyar APC a Mazaɓar Ganduje suka yi wa Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa Abdullahi Umar Ganduje daga jam’iyyar.

Alƙalin kotun Justice Usman Malam Na’abba ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata takardar da masu ƙara suka nema, ba tare da sanarwa ɓangaren waɗanda suke ƙara ba wato (Motion Ex parte).

Haladu Gwanjo da Laminu Sani ne suka shigar da ƙarar, inda suka yi ƙarar ɓangarori huɗu waɗanda suka haɗar da Jam’iyyar APC, Kwamitin ayyukan jam’iyyar na qasa, Kwamitin Zartarwa na Jam’iyyar APC na Jihar Kano da kuma Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Masu ƙarar dai sun shigar da roƙon su ta cikin wata takardar mai sakin layi 12 tare da adireshin mai ƙara na biyu a ranar 16 ga watan nan da muke ciki, bisa jagorancin Lauyansu Barista I. A. Sa’ad.

Takardar umarnin ta amince waɗanda ake ƙara na farko da na biyu da kuma na huɗu, su maida martani ta wajen hurumin kotun, wato a ofis mai Lamba 40 dake kan titin Biantyre Crescent a Babban birnin Tarayya Abuja.

Kazalika a ranar ta Laraba an zauna domin gudanar da shari’a tsakanin gwamnatin Kano da tsohon gwamnan na Kano Dr Abdullah Umar Ganduje da zuri’arsa inda ake zarginsu da cin hanci da rashawa, to dai ba su halaccin zaman kotun ba, wanda rashin bayyanar Ganduje a gaban kotun ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin waɗanda suke je sauraren ƙarar, yayin da suke ƙoƙarin tantance ko rashin bayyanar Ganduje rashin girmama kotu ne ko kuma a’a, 

Sauran waɗanda ba su halarci kotun ba sun haɗa da matarsa, Farfesa Hafsat Ganduje da danta, Umar Ganduje, da wasu mutane 5 da ake zargi .

Sai dai ba a bayyana dalilin da ya sa tsohon gwamnan wanda kuma shi ne shugaban jam’iyya mai mulki na ƙasa ya kasa bayyana a gaban kotu, amma wasu makusancinsa da ba a bayyana sunansa ba ya bayyana cewa “Dr. Ganduje ba ya ƙasar.”

Tun a ranar 9 ga Afrilu, 2023 babbar kotun jihar Kano ta bayar da sammaci ga shugaban jam’iyyar APC na ƙasa da ya gurfana a gaban kotu a ranar 17 ga watan Afrilu kan zargin almundahana na biliyoyin naira da aka tafka a lokacin da yake kan mulki.

Har ya  zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, ba a bayyana ko ya aike da wakilci kotun ko a’a ba .

Sai dai Hedikwatar Jam’iyyar APC ta Ƙasa ta ce ba ta da masaniyar umarnin kotu da ke dakatar da shugaban jam’iyyar, Abdullahi Ganduje.

Mai ba jam’iyyar shawara ta fuskar shari’a, Farfesa Abdulkarim Kana, ya ce ba su samu umarnin Babbar Kotun Jihar Kano kan shugaban jam’iyyar, wanda shugabannin mazaɓarsa suka dakatar ba.

Ya ce, “Shugabancin jam’iyyarmu ya riga ya rubuta wa shugaban ’yan sanda takardar ƙorafi kan lamarin.”

Hukumar Yaƙi da Rashawa da Sauraren ƙorafe-ƙorafe ta Jihar Kano, ta shigar da sabuwar ƙara kan tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Shugaban Jam’iyyar APC na qasa, Abdullahi Ganduje, inda take zarginsa da karkatar da maƙuden kuɗi Naira biliyan 51.3 mallakar ƙananan hukumomin jihar.

Shugaban Hukumar, Muhuyi Magaji ne ya bayyana haka a cikin wani shirin da tashar Channels Television ta yi da shi a ranar Talata da ta gabata.

A cewar Magaji, bincike ya gano wasu kuɗaɗe mallakar ƙananan hukumomi har biliyan N51.3 wanda aka karkatar da su zuwa asusun ajiyar wasu ɗaiɗaikun mutane ba a bisa ƙa’ida ba a zamanin gwamnatin Ganduje.

Haka nan, ya yi zargin cewa, gwamnatin Ganduje ta ciri kuɗi Naira biliyan 1 duk wata daga asusun jihar kafin qarewar wa’adin shugabancinsa a watan Mayun 2023 da sunan gyara hanya, maimakon haka sai aka karkatar da kuɗin zuwa ga kamfanonin canji.

Kazalika, ya tavo batun wani biliyan N4 da aka tura cikin asusun wani kamfanin harkokin noma a Kano.

Ya ƙara da cewa, “Abin da ke faruwa yanzu somin-taɓi ne kawai. A yanzu da nake wannan zancen, muna bincike kan kuɗaɗen ƙananan hukumomi biliyan N51.3 wanda aka cire daga asusun gwamnati sannan aka tura cikin asusun wasu ɗaiɗaikin mutane.

“Mun shigar da ƙararraki da dama ciki har da batun Naira biliyan 1 da aka cire daga asusun gwamnati a watan Afrilun bara da sunan gyaran hanyoyi guda 30 a birane, amma sai aka tura kuɗin ga kamfanin canji,” in ji shi.

Ana tsaka da wannan, sai wani tsagi na Jam’iyyar NNPP, ƙarƙashin jagorancin Manjo Agbo ya sanar da dakatar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano daga cikin jam’iyyar.

A cikin sanarwar da Ogini Olaposi, sakataren jam’iyyar, ya fitar a yayin taron ‘yan jarida na wannan Talata a Abuja, tsagin jam’iyyar ta NNPP, ya ce rashin bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi shi ne ya sanya su ɗaukar wannan mataki.  

Jaridar The Punch ta ce tsagin na NNPP ya fusata da halartar babban taron jam’iyyar da wani ɓangare ƙarƙashin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya jagoranta da gwamnan na Kano ya yi a ranar 6 ga Afrilu, 2024. 

A jawabin Mr. Olaposi, ya ce ba su ga dalilin da gwamnan Kano zai halarci taron na Kwankwasiyya da a ganinsu haramtacce ne ba.

Sai dai tuni wasu ‘yan Kwankwasiyya suka yi watsi da wannan dakatarwa daga jam’iyyar ta NNPP wacce a ƙarƙashinta ne aka zaɓi gwamnan na Kano da ƙuri’u sama da miliyan ɗaya.