Tinubu ya taya Idris murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya taya Ministan Labarai da Wayar da Kan ‘Yan Ƙasa, Mohammed Idris, murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce, Ministan hadimin gwamnati ne wanda ya zo a daidai lokacin da ake buƙatarsa.

Ta ƙara da cewa, Ministan wanda mawallafi ne kuma ɗan siyasa, yana aiki da ƙwarewa a matsayinsa na Ministan Labarai da Wayar da Kan ‘Yan Ƙasa.

Haka nan, ta ce Idris na daga cikin ‘yan sahun gaba a fagen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a kasancewarsa mawallafi na Jaridun Blueprint, kuma Shugaban Bifocal Group da kuma Kamfanin Kings Broadcasting Limited wanda ke da tashar WE 106.5 FM a Abuja.

Ngelale ya ce, “Shugaban Ƙasa na yi wa Alhaji Idris fatan ganin shekaru masu yawa kuma cikin ƙoshin lafiya, da kuma samun nasara a hidimar da yake yi wa ƙasa.”