11
Mar
"Iyaye sun yi farin ciki da muka koyar da 'ya'yansu sana'a a lokacin karatu" Daga UMAR AKILU MAJERE A makon da ya gabata, mun ɗauko tattaunawa da jajirtacciyar mace da ya cancanta a kira da Gimbiya, sakamakon irin gwagwarmayar da take yi wurin ganin ta inganta harkar ilimi musamman ma a karkara, duk da cewa ba mazauniyar karkara ba ce, amma tana tafiyayya har zuwa ƙauyukan nesa, waɗanda da yawa ba su da hanyar da mota za ta iya bi. A cikin tattaunawar, mai karatu da ke bibiyar mu ya ji irin ƙalubalen da Hajiya Nafisa ta fuskanta ciki har…