“Rubutu ba ruwansa da girman ka ko ƙanƙantarka”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Akwai masu ganin cewa ba a gadon basira ko wata baiwa ta ƙirƙira, domin kuwa wannan kyauta ce ta Allah. Amma fa duk da haka da akwai waɗanda za a iya cewa ƴan na gada ne da sun wuce ƴan na koya. Ummulkhairi Sani Panisau da aka fi sani da Khairat UP na daga cikin marubutan da suka taso cikin gidan rubutu, domin kuwa ƴa ce a wajen fitacciyar marubuciyar nan Sadiya Garba Yakasai, wacce ta rubuta littattafai fiye da 80, kuma har yanzu tana jan zarenta a fagen rubutu. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, Khairat wacce ita ma ta rubuta littattafai fiye da 30 ta bayyana cewa bayan rubutu da ta gada daga wajen mahaifiyarta, ta kuma koyi wasu abubuwa da dama da suka taimaka mata wajen zaman rayuwa da gidan aure.
MANHAJA: Mu fara da gabatar da kanki.
KHAIRAT UP: Assalamu Alaikum. Asalin sunana Ummulkhairi Sani Panisau, wacce aka fi sani da Khairat UP. Ni marubuciya ce kuma malamar makaranta. Ina aikin koyarwa a makarantar firamare ta maza da mata. Ina kuma sana’ar mata ta cikin gida, irinsu Zoɓo (Hibiscus Mix), wanda har aikawa nake yi gari gari. Har wa yau, ina yin sana’ar kwalliya a gida. Ina sayar da kayan qƙwalama na yara irinsu alawar madara, da fara. Ina kuma sayar da mayafai, da haɗa kayan anko. Ni uwa ce, ina da aure da yara.
Ko za mu san wani abu daga tarihin rayuwarki?
Iyayena haifaffun garin Kano ne, sai dai mahaifina sauyin wurin aiki ya mayar da shi garin Legas a can ma aka haife ni, sai daga baya muka dawo Kano. Na fara karatuna tun daga matakin makarantar rainon yara ta nursery zuwa firamare a Seat of Wisdom da ke Unguwar Hotoro, a Tsamiyar Boka. Na yi sakandire a FAAN, sannan na yi NCE a Kwalejin Nazarin Ilimin Larabci ta CAS da ke Kano, inda na karanci Turanci da Hausa. In sha Allahu, nan gaba kaɗan ina da niyyar komawa makaranta. Ina da ƙannai shida. Na yi aure a shekarar 2018, ina da yara biyu, Ummulkhairi da Halima.
Menene ya ja ra’ayinki ki ka fara rubutun adabi?
Abinda ya jawo ra’ayina game da rubutu gaskiya mahaifiyata ce. Abinda ya sa na ce haka kuwa shi ne, na taso na ga tana rubutu, kuma na ga irin ɗaukaka da girmamawar da take samu a wajen mutane daban-daban. Sai ni ma na taso da sha’awar son yin rubutun, sai dai ban fara yin rubutu ba sai da na kammala makarantar sakandire. Shi ma a vɓoye nake yi, saboda ban san yadda iyayena za su karɓi abin ba.
Menene dangantakarki da marubuciya Sadiya Garba Yakasai?
Sadiya Garba Yakasai mahaifiyata ce, wadda ta kawo ni duniya.
Shin za mu iya cewa kin gaji baiwar rubutu ne daga wajen mahaifiyarki?
E, ƙwarai na gaji rubutu daga wajen mahaifiyata! Kuma ina alfahari da wannan a ko’ina. Na koyi girki, tsaftar gida, kwalliya da kuma sana’ar cikin gida a wajen mahaifiyata. Saboda ita mace ce da bata son ka zauna haka kawai ba ka wata sana’a. Babban abin da nake fahari da shi daga gareta shi ne, yadda take nusar da ni da ‘yan’uwana muhimmancin zumunci da qaunar junanmu, da ma sauran ‘yan’uwanmu. A danginmu ma tsabar son zumuncinta “Uwar Marayu” suke kiranta da shi. Wannan ma nasara ce kuma abin alfahari a gare ni. Sannan ta koya min yadda zan zauna da mutane faram-faram ba tare da na ɓatawa wani ko wata ba, sai dai in Allah ne ya kawo.
Wanne tasiri mahaifiyarki ta yi wajen zaɓin salon rubutunki? Akwai wani abu da ku ke kamanceceniya da ita wajen salo ko zubi?
Gaskiya na fara rubutu a voye ba tare da mahaifiyata ta sani ba, a lokacin ina tsoron yadda za a karɓi abin a gidanmu don mahaifina ya fi son mu mayar da hankali a kan karatunmu. Amma ina yin amfani da wasu daga cikin salon rubutunta. Muna da kamanceceniya a fannin salon labari irin na gidan gandu da ƙalubalen da ake samu a cikinsa. Akwai kuma na matsalolin da mata ke fuskanta a gidajensu na aure.
Wanne labari ki ka fara rubutawa, kuma kawo yanzu kin rubuta littattafai nawa?
Littafin da na fara rubutawa shi ne, ‘Nana Firdausi’. Kuma kawo yanzu na rubuta littattafai a onlayin guda 30 ko ma fiye da haka.
Kawo mana sunayen littattafan da ki ka rubuta, da taƙaitaccen bayani kan uku daga cikinsu?
Kamar yadda na ce, na rubuta littattafai guda 30, da suka haɗa da ‘Nana Firdausi’, ‘Takaicin Ɗa Namiji’, ‘Meye Laifina?’ ‘Rayuwata’, ‘Nana Fatima’, ‘Kukan So’, ‘So’, ‘Kuskure’, ‘Mugun Miji’, ‘Tun Ran Gini Tun Ran Zane’, ‘Ahlam’, ‘Sarkakiyar Soyayya’, ‘Ruxɗin Duniya’, ‘Kai Nake So’, ‘Sanadi Ne’, ‘Hilal Da Ilham’, ‘Ummusalma’, ‘Amini Na Ne’, ‘Sila’, ‘Tsaka Mai Wuya’, ‘Ban Yi Zato Ba’, ‘Aisha Humaira’, ‘Rashin Sani’, ‘Da Bambamci’, ‘Rukkaya’, ‘Waye Nawa?’ ‘Ƙanin Ajali’, ‘Son Ma So Wani’, ‘Sakamakon Ƙauna’.
Shi littafin ‘Meye Laifina?’ littafi ne da ya kawo labarin wata matashiya da bata da kowa sai mijinta. Marainiya ce babu wanda ta sani sai mijinta, wanda shi kuma ya kasance azalumin mutum ne mai saurin fushi da fusata, sannan kuma gashi ɗan shaye-shaye ne. Ba ya ganin darajarta, bai ɗauke ta a matsayin komai ba, sai mai mishi tsaron gida kawai. Ya aurota ne don ya kawar da idon mutane daga kansa. In ya dawo a buge ya daketa, ya zage ta, ya yi mata mugayen raunika. Sai dai in ya tashi ya gani ya yi mata barazana da wani dukan akan idan sun je asibiti kar ta ce shi ne ya dake ta.
Rayuwar da ta yi ba mai dadi ba ce, wani zubin ma da matan banza ko abokanansa zai zo ya yi abin da zai yi kuma ta gyara. Ɗansu ɗaya ne, kuma mafi soyuwa a wajen mahaifinshi. A cikin wannan zaman nasu ne har ta shiga cikin lalurar damuwa ta soma manta wace ce ita. Ana haka ta gaji ta kashe shi, kuma ta kira ‘yan sanda kan ta yi kisan kai. Aka kama ta aka yi zaman shari’a, amma sai ta bayyana wa kotu cewa ta kashe shi ne wajen kare kanta saboda irin dukan da yake yi mata har da yankan kwalba da tabon wuta a jikinta. Sakamakon hujjojin da suka bayyana gaban kotu, aka sallameta tare da ba da umarnin kaita asibitin ƙwaƙwalwa don yi mata magani. Yaron kuma lauyanta ta riƙe shi har zuwa lokacin da za ta warke.
Littafin ‘Sarƙaƙiyar Soyayya’ kuwa labarin wasu masoya ne guda hudu da suke son junansu. Ma’isha da Ruqƙayya sun kasance yan’uwan juna ubansu ɗaya mahaifiyar Ma’isha ta rasu, amma mahaifinsu bai raba kan yaransa ba. Sai dai Ruqƙayya na kishi da kulawar da ake nunawa yar’uwarta fiye da ita, saboda bata da cikakkiyar lafiya, amma bata tava nunawa ba. Akwai Muhammad da yake ɗa ne a gidan amma riƙon shi ake yi mahaifinsa yayan mahaifinsu ne.
Soyayya ce mai ƙarfi, tsakanin Ma’isha da Muhammad, yayin da Ruƙayya take son Muhammad kuma ta ci alwashin sai ta aure shi, ba zata bar wa Ma’isha ba. A gefe kuma akwai wanda ke son Ma’isha da shi suka ƙulla suka ruguza soyayyar Ma’isha da Muhammad aka yi musu aure. Haka suka haƙura da junansu, amma zuciyoyinsu na mabambamta wurare.
Ma’isha na fama da halin kishin mijinta saboda Muhammad, yayin da Muhammad ya danne zuciyarsa ya daina kula da Ruƙayya. Mahaifinsu ya rasu. Ruƙayya ta haihu sai dai mutuwa take yi. A kan jaririyar Ma’isha da mijin suka yi faɗa har ya fusata cikin fushi ya saketa. Daga ƙarshe ta auri Muhammad bayan shan gwagwarmayar soyayya da suka yi. A ƙarshe dai Allah Ya yi za su zauna da juna.
A littafin Tun Ran Gini Tun Ran Zane, an nuna yadda wata muguwar ƙiyayya tsakanin ƙawaye biyu. Aliyu da Rauda sun kasance ‘yan’uwan juna, kakaninsu ɗaya da mahaifiyar Rauda da mahaifin Aliyu ‘ya’yan ya da ƙanwa ne. Sai dai mahaifin Aliyu da mahaifin Rauda ba sa ga maciji kamar yadda mahaifiyar Aliyu da mahaifiyar Rauda basa ga maciji saboda sun taso ƙawayen juna sai mahaifiyar Aliyu ta shiga ta fita ta raba soyayyar Mami da Abba Ibrahim.
Ta yi asirin da ya aureta, ita kuma ya karya nata alƙawarin ita kuma aka aura mata Baban Rauda, wanda shi yake sonta amma bata son shi, kuma har suka hayayyafa. Iyayensu maza suka mutu bata tava son shi ba, abin na damun shi matuƙa. Cikin ikon Allah ‘ya’yansu suka faɗa soyayya da junansu, sai dai rashin shirin iyayensu ya sa ba a yi magana ba, duk da mahaifin Aliyu bashi da matsala da hakan. Daga ƙarshe dai Mami Abban Rauda ya sake ta, kuma ta auri Ibrahim din suka dinga tafka kishi a cikin gidan kamar ba sanayya ko alaƙar auren ‘ya’yansu a tsakaninsu.
Wanne littafin ne bakandamiyarki? Kuma ta wacce hanya ki ke gane karɓuwar labarinki a wajen masu karatu?
A cikin dukkan littattafan da na yi guda biyu ne bakandamiyata, ‘Meye Laifina?’ Da kuma ‘Sarƙaƙiyar Soyayya’. Ba zan taɓa manta irin mabiyan da na samu a littattafan nan biyu ba. Har sai da wani ya kira ni a littafin ‘Meye Laifina?’ ya ce na burge shi yadda na tafiyar da jigon labarin ya yi masa daɗi sosai. ‘Sarƙaƙiyar Soyayya’ ko har yau ina samun masu yin yabo da sharhi a manhajar wattpad saboda littafin na soyayya ne, soyayyar ma irin wadda aka sha gwagwarmaya kafin a samu nasara. Waɗanda suka shiga irin wannan halin sun fi kira na sosai. Sannan ina gane karvuwar labaraina ne ta kafafen sadarwa irinsu WhatsApp da wattpad.
A WhatsApp ina ganin saƙonni daga masoyan da ban taɓa gani ba sai ta hanyar waya, ina kuma samun masu kira na kawai don su yi min godiya kan darasin da suka tsinta a labarin. Ta hanyar wattpad ma ina samun yabo da sharhi.
Wanne darasi ki ka fi mayar da hankali a kai wajen zaɓar jigon da za ki yi rubutu a kai?
Na fi karkata ga jigon gidan aure saboda irin ƙalubalen da mata ke fuskanta a gidajensu da haƙurin da suke yi da maza, da ma dangin mazajensu. Haka su ma a ɓangaren mazan, yadda suke haɗuwa da makiran mata.
Wanne ƙalubale ki ka fuskanta a farkon littafinki? Wa ya taimaka miki ki ka gano hakin zaren?
Ban fuskanci wani ƙalubale a lokacin da na fara rubutu ba. Babu wanda ya taɓa taimaka min saboda dama a lokacin bana shiga cikin harkar mutane sosai. Ni kaɗai na yi kasada ta, kuma Alhamdulilahi kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
Yanzu da mahaifiyarki, Sadiya Garba Yakasai, ta dawo cigaba da rubutu, yaya ki ke kallon hakan a matsayinta ta uwa a tsakanin sa’o’in ƴaƴanta?
(murmushi). Wato abin da na lura shi ne tana son ta gayawa masoyanta cewa fa tana nan bata durƙusa ba, hutawa ta yi, kuma har yau tana nan da son rubutunta. Na san tana nan da niyyar buga wasu littattafan nan ba da jimawa ba, in sha Allah.
Sannan kuma ai shi rubutu babu ruwansa da girman ka ko ƙanƙantarka, don kuwa da akwai marubuta da dama da suke ƙoƙarin tasowa, akwai ma tsofaffin marubutan da suka cigaba da yin rubutun onlayin ɗin cikin ‘ya’yan nasu. Kawai dai shi marubuci duk inda yake marubuci ne, sai dai in rubutun bai motsa masa ba, kuma in ya motsa masan sai ya rubuta.
Wacce gudunmawa ki ke ganin za ta iya bayarwa wajen tarbiyya da fahimtar da sauran matasa mata masu tasowa cikin duniyar marubutan Hausa?
Na san har cikin ranta abin da take so a samu rashinsa a harkar rubutu ko in ce a daina ma kwata-kwata, shi ne rubutun batsa. kamar yadda take nuna musu, shi ne tsaftar rubutu abu ne mai kyau, saboda duk abin da ka rubuta to, fa shi zai yi ta bin ka har kabarinka. Marubuci zai iya mutuwa amma rubutunsa ba zai taɓa goguwa ba. Sannan abu ne mai kyau su riƙa jin maganar manyansu don su ma a bi nasu a gaba. Koyawar tarbiyya abu ne mai wuya amma mai daɗi ga wanda ya bin ta. Ita kuma mahaifiyarmu abin da ta fi bai wa muhimmanci sosai kenan.
Shin mahaifiyarki tana karanta littattafan da ki ke rubutawa? Yaya ki ke ji a ranki idan ta duba labarinki?
Tana karantawa sosai, amma ba dukka littattafaina ta karanta ba. Sannan wani lokacin idan zan yi rubutu nakan yi mata bayanin labarin da nake son yi, sai ita kuma ta ɗora ni a hanya tare da bani shawarwari a kai. Ina matuƙar jin daɗi idan ta yaba labarina a yayin da ta duba.
Wanne abu ne ya taɓa faruwa da ke a harkar rubutu na alheri ko akasin haka, wanda ba za ki manta da shi ba?
Gaskiya babban alherin da rubutu ya bani shi ne girmamawa da mutunci a tsakanina da masoyana. Lokuta da dama idan wani ko wata ya ganka sai ka ga murna da girmamawar da yake ko take baka ba ta iya ɓoyuwa. Wannan ma nasara ce kuma babban alheri ne sosai, saboda ka yi rubutu mai tsafta, kuma dalilin tsaftace alƙalaminka mutane da dama maza da mata suka san ka, kuma suke ganin girman ka.
A dalilin rubutu wata mata ta tura min katin waya don na yi rubutu a kan kari. A dalilin rubutu wata baiwar Allah za ta yi sa’ar mahaifiyata ta yi min ciniki tun daga Adamawa ba tare da ta sanni ko na san ta ba, ta yarda dani nima na yarda da ita ina ganin wannan ma abin alkahairi ne a gareni. Ban tava cin karo da wani abu da zan kasa mantawa da shi ba.
Me ya fi baki sha’awa a rayuwa cikin marubuta?
Gaskiya abin da yake burge ni da marubuta na farko haɗin kansu, zumuncinsu ga juna, da kuma kyakkyawar alaƙa a tsakaninmu, daga mazan har matan. Sannan muna ilimantuwa da junanmu daga wasu daga cikinmu da suka yi zurfi cikin ilimin harshen Hausa da yadda ake kiyaye ƙa’idojin rubutu, da sauransu.
Wanne bambanci ki ke ganin aka samu tsakanin marubuta mata na baya da matasa na yanzu, duba ga irin salon rubutu da darussa da suke rubutu a kai?
(Hmm) To! Bambamci na farko marubuta mata na baya haƙiƙa ba su da girman kai, ba sa kuma nuna wani jin kai don sun kasance sanannu, ko masu ɗaukaka. A tsakaninsu babu wanda ya fi wani, a cikinsu kuma babu bambancin ban san waccan ba, ban san wannan ba. Kowa nasu ne, kuma har yau zumuncinsu ya ɗore bai rushe ba.
Na biyu kuma gaskiya zan iya cewa kowa da irin darasi da salon da yake amfani da shi wajen isar da saqonsa. Kuma Alhamdulillahi, kowa da irin darasin da yake isarwa, akwai waɗanda suke gyara alƙalaminsu akwai waɗanda suke ɓatawa. A marubutan baya akwai marubutan da duniya bata mance da su ba har yanzu. Ko a marubutan onlayin ɗin ma akwai waɗanda suka yi fice saboda tsafta da kyan alƙalumansu masu ɗauke da ma’ana da darrusa masu yawa.
Wacce ƙungiyar marubuta ki ke? Kuma yaya ki ke kallon tasirin ƙungiyoyi wajen inganta rubutun mambobinsu?
Ina cikin Ƙungiyar Karamci Writers Association ne. Kuma abin da na sani shi ne kowacce ƙungiya akwai tsarin da take amfani da shi wajen tafiyar da harkokinta. Dama amfanin ƙungiya ga mambobinta shi ne su ƙara wayar da kan marubuta a kan ƙa’idojin rubutu. Musamman mu a Karamci Writers Association, ana koyar da ƙa’idojin rubutu, yadda marubuci zai zaɓi jigo, yadda zai kiyaye salon labarinsa. Kuma wajibi ne kafin marubuci ya fitar da littafinsa ko nata, sai shugabanin ƙungiya sun gani sun yarda da tsaftarsa, za a tura cikin zaurukan da ƙungiya ke da su. Sannan akwai ƙungiyoyin da suke da rijista da CAC, akwai kuma waɗanda ba su da shi.
Shin da gaske ana yawan samun gutsiri tsoma a zamantakewar marubuta? Ta yaya za a riƙa ƙarfafa zumunci a tsakaninsu?
Da dai a baya an samu amma a yanzu kam Alhamdulilahi, an samu sauƙin hakan sosai. Zan iya cewa ma yanzu daga mazan har matan suna zumunci da juna sosai. Ta hanyar gaisawa akai-akai, da kuma ta hanyar qarfafawa juna. Sannan kuma waɗanda suke mabambamta garuruwa suna ƙoƙarin halartar abinda ya danganci wani marubucin ko wata, in ya tashi wata hidima kamar aure. Maza kan halarci ɗaurin aure a madadin wasu daga cikinmu, hada gudunmawa ga waɗanda suka haihu ko aure ko rashin lafiya ko taimakawa juna in wani abu ya samu wani ko wata.
Su wanene makusantanki a cikin marubuta da ku ke hulɗar zumunci tare?
Gaskiya ina zumunci da marubuta sosai, kusan kowa nawa ne. Amma muhimmai daga cikinsu akwai irinsu Sadiya Adam (Sanah) Firdausi Sodangi, Futhatulkhair, Suwaiba Muhammad, Fatima (Mrs. Omar) Zara BB, Hajja Ce, Jamila Muhammad (Maman Bobo) da dai sauran su.
Wane ne madubinki a cikin marubuta?
Yayana Ayuba Muhammad Danzaki.
Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?
Da taron yuyuyu gwara ɗa ɗaya ƙwaƙƙwara.
Na gode
Ni ma na gode ƙwarai da gaske.