Ranar Ma’aikata: Gwamnati ta ayyana 1 ga Mayu, ranar hutu ga ma’aikata

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Laraba, 1 ga watan Mayu, a matsayin ranar hutun gama-gari albarkacin Bikin Ranar Ma’aikata na bana.

Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Babban Sakataren Ma’aikatar Cikin Gida, Dr Aishetu Ndayako, ta fitar ranar Talata a Abuja.

Aishetu ta ce, Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr Olubunmi Tunji-Ojo ne ya ayyana ranar hutun a madadin Gwamnatin Tarayya.

Tunji-Ojo ya jaddada buƙatar aiki da ƙwazo a ɗaukacin ɓangarorin ƙwadago, kana ya ƙara haskaka ƙudurin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ƙoƙarin samar da walwala ha ma’aika da kuma son ganin ma’aikata sun zamo masu ƙirƙirar a wajen aiki.

A ƙarshe, Ministan ya yi kira ga ‘yan Nijeriya ta su zamanto masu mara wa gwamnatin Tinubu baya domin cimma nasara a manufofinta na ciyar da ƙasa gaba.