Zama da kishiya

Daga SA’ADATU SAMINU KANKIA

MANHAJA: Wacce shawara za ki ba wa matan da mazajensu ke shirin ƙara aure?

Shawarata ga mata da mazansu ke shirin ƙara aure shi ne, su yi haƙuri, kuma su sanya a ransu ba don mijinsu baya sonsu ba ne za ya ƙara aure, kowa da irin ƙaddarar rayuwarshi.

Abu na gaba da mace zata yi shi ne ta dage da addu’a, akan samun zaman lafiya a gidansu, ta natsu ta fahimci mijinta, sannan ta kauce ma sauraren maganganun mutane, saboda wani lokaci su ne ke hana zaman lafiya. Haka nan ta kame kanta kada ta biye ma zuciya ta yi abinda za ya zubar mata ƙima a idon miji da kuma wadda za a auro. kada ta saki kanta har ta bada kafar kawo mata raini.

Sannan ta riƙe gaskiya da amana, ta ɗauki girma, kada ta yarda ta rinƙa aikata abubuwan da za su sanya tun daga waje amarya ta raina ta, ko kuma ya zanto ta fita ran mijin.

Akwai ciwo sosai, amma da zaran anyi haƙuri sai kaga komi ya wuce kuma an zauna lafiya.

Wane kira za ki yi ga maza da ke da sha’awar ajiye mace fiye da ɗaya?

Ina so su sani cewa, wannan damar da Allah ya ba su ya ba su ne, saboda yasan za su iya, don haka su kasance masu adalci a tsakanin iyalinsu, su guji kwasar maganar ɗaya suna gaya ma ɗaya, su guji nuna bambanci ko fifiko, sannan su yi adalci akan komi.

Hakanan su sani mace shu’umace, kowacce da irin halinta, don haka su karanci yadda za su zauna da kowacce lafiya, ba tare da nuna fifiko ko ƙaasƙanci ga wata ba, akwai mazan da da kansu suke hana zaman lafiya a tsakanin iyalinsu wai saboda ba su so su haɗa kai. Wannan sakarci ne da jahilci saboda babu abinda ya fi zaman lafiya daɗi.

Namiji ya zama namiji a gidanshi ba wai hoto ba, sannan ya rinƙa sanya ido akan zamantakewar gidan don kada ya zamto ana kwarar ɗaya. Sannan ya dage da addu’a, Allah ya ba shi iko da ƙarfin riƙe iyalinshi.

Wacce shawara ki ke da ita ga mata bakiɗaya?

Shawarata ga mata ita ce su sani, ƙarin aure ba laifi ba ne, ba kuma gazawarsu ke sanyawa a ƙara aure ba, su sani halittar maza haka take Allah bai halicce su su so mace ɗaya ba, ko namiji bai ƙara aure ba, tabbas akwai wata da yake so ko take burge shi, don haka su cire tunanin zasu zauna su kaɗai, sai dai idan Allah ya ƙaddara hakan.

Da zaran suka fahimci haka za su zauna lafiya, sannan su kyautata ma mazajensu zato a cikin ko wane yanayi, su zamo masu haƙuri da juriya da kame kai.