MOPPAN ta kafa muhimman kwamitoci biyu

A ƙoƙarin da take yi na ci gaba da ingata harkokinta, Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), ta kafa muhimman kwamitoci guda biyu.

Ƙungiyar ta kafa Kwamitin Ladabtarwa da ayyuka na MOPPAN/Kannywood mai mabobin 14 domin ci gaba da tsaftace ayyukan masana’atar finafinai.

Sai kuma kwamitin tara kuɗi da kai ziyara, shi ma mai mambobi 14.

Ƙungiyar ta bayyana haka ne a cikin sanarwar manema labarai da ta fitar mai ɗauke da sa hannun Sakatare na Ƙasa, Al-Amin Ciroma.

Sanar ta ce an ƙalubalanci ‘yan kwamitin da su yi aiki daidai da tanadin dokokin MOPPAN.

Shugabam MOPPAN na ƙasa, Alhaji Habibu Barde, ya ce kafa kwamitocin na da matuƙar kuma muhimmanci, kuma an kafa su a lokqcin da ya dace.

Ga jerin sunayen mambobin kwamitocin kamar yadda Sakatare Janar na MOPPAN, Salisu Mu’azu, ya miƙa su kamar haka:

Kwamitin Ladabtarwa da Ayyuka:

Mohammed Kabiru Maikaba – Shugaba
Ahmad Alkanawy – Mamba
Shuaibu Yawale – Mamba
Hajiya Balaraba Ramat – Mamba
Magaji Mijinyawa – Mamba
Hajiya Rashida Adamu (Mai Sa’a) – Mamba
Hauwa Editor – Mamba
Dr. A. S. Bello – Member
Bala Muazu Kufaina – Mamba
Hajiya Fatima Lamaj – Mamba
Muhammed Gumel – Mamba
Salisu Officer – Mamba
Maikudi Cashman – Mamba

Kwamitin Tara Kuɗi da Kai Ziyara:

Alh. Ado Ahmad Gidan Dabino MON – Shugaba
Bello Achida – Mamba
Asma’u Sani – Member
Haladu Muhammed – Mamba
Al-Amin Ciroma – Mamba
Ibrahim L Ibrahim – Mamba
Umar Gombe – Mamba
Ahmad Hashim – Mamba
Tijjani Faraga – Mamba
Jamila Nagudu – Mamba
Maijidda Abbas – Mamba
Falalu Dorayi – Mamba
Nasiru Gwangwazo – Mamba
Ibrahim Amarawa – Sakatare.