
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙasar Birtaniya ta umarci Nijeriya da wasu ƙasashen Afirka guda 32 da su mallaki takardar tantancewa ta shiga gabanin zuwa ko wucewa ta ƙasar.
Birtaniya ta sanar da haka ne ta ofishin hukumar shige da ficenta a ranar Litinin.
Sabon jaddawalin sharuɗɗan ya ƙunshi matafiya su tabbatar da cika ƙa’idojin biyan ƙudin jirgin zuwa ƙasar, inda ta yi gargaɗin cewa waɗanda ba su da takardun da ake buƙata ka iya fuskantar jinkiri ko soke tafiyarsu.
Haka kuma, ‘yan ƙasashe sama da 100 da yankunan ake buƙatar su mallaki biza gabanin shiga Ingila da nufin ziyara na tsawon watanni shida, saidai idan akwai wani dalili mai ƙarfi da zai sa a ware wasu.
Dokar ta kuma shafi fasinjoji da ke amfani da tashoshin jiragen saman Birtaniya.
Kazalika, gwamnatin ƙasar ta ce mutanen da ba su da ƙasa da matafiya masu amfani da wasu takardu a madadin waɗanda aka amince da su a hukumance wajibi ne su mallaki takardar tantancewar shiga gabanin zuwa ƙasar.
A cewarta, ta ɗauki matakin ne a matsayin wani ɓangare na inganta lamuran kula da iyakokin ƙasa da tabbatar da bin dokokin shige da fice.
Ƙasashen da aka fitar da sabuwar dokar akansu sune “Algeria, Angola, Botswana, Burundi, Cameroon, Republic of the Congo, Democratic Republic of the Congo, Egypt, Eritrea, Eswatini, Ethiopia, The Gambia, Ghana, Guinea, Guinea-Bissau, Côte d’Ivoire, Kenya, Lesotho, Liberia, Libya, Malawi, Namibia, Nigeria, Rwanda, Senegal, Sierra Leone, Somalia, South Africa, South Sudan, Sudan, Tanzania, Uganda” da kuma Zimbabwe.
