A duk lokacin da aka ambaci manyan matsalolin da suke yi wa Nijeriya barazana, mutane kan fi karkata hankali ga rashin tsaro, talauci, rashin aikin yi da hauhawar farashin kayayyaki. Sai dai akwai wata annoba da ke ci gaba da kutsawa cikin al’umma cikin shiru, tana lalata rayuwar dubban matasa, tana rusa iyalai, tana haddasa aikata manyan laifuka, kuma tana kassara makomar ƙasa. Wannan annoba ita ce shan miyagun ƙwayoyi da kuma fataucin su.
A yau, shan miyagun ƙwayoyi ya zama wani babban ƙalubale da ya wuce matsalar mutum ɗaya ko iyali ɗaya. Matsala ce da ta shafi lafiyar jama’a, tsaro, tattalin arziki da ci gaban ƙasa baki ɗaya. Duk inda aka samu yawaitar masu amfani da miyagun ƙwayoyi, ba da jimawa ba za a fara ganin ƙaruwar sata, fashi da makami, garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, rikice-rikicen daba, cin zarafin mata da yara, da sauran miyagun laifuka.
Abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda wannan annoba ke ƙara shiga zukatan matasa, waɗanda su ne ginshiƙin kowace al’umma. Matasan da ya kamata su kasance injinan ci gaban Nijeriya suna zama bayi ga ƙwayoyi masu sa maye. Wasu sun rasa karatunsu, wasu sun rasa ayyukansu, wasu sun lalata dangantakarsu da iyaye, yayin da wasu kuma suka rasa rayukansu saboda shaye-shaye.
Masana kiwon lafiya da na ilimin halayyar ɗan Adam sun sha bayyana cewa mutumin da ya fara amfani da miyagun ƙwayoyi tun yana ƙarami yana cikin haɗarin lalacewar kwakwalwa, rashin iya yanke shawara mai kyau, da kamuwa da matsalolin tabin hankali. Hakan ne ya sa ake samun matasa masu ƙarfin jiki amma marasa hangen nesa, marasa buri, kuma marasa amfani ga kansu da al’umma.
A Nijeriya, Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta ci gaba da bayyana cewa mafi yawan masu aikata manyan laifuka suna da alaƙa da amfani da miyagun ƙwayoyi. Wannan ya nuna cewa idan ana son rage rashin tsaro, dole ne a fara daƙile shaye-shaye.
Abin farin ciki shi ne, gwamnatin tarayya da Hukumar NDLEA sun ƙara nuna ƙwazo wajen yaƙar wannan annoba. A cikin ‘yan shekarun nan, NDLEA ta samu manyan nasarori wajen kama dillalan ƙwayoyi, kwace tarin miyagun ƙwayoyi masu darajar biliyoyin nairori, tare da gurfanar da dubban mutane a gaban kotu. Haka kuma, hukumar ta ƙara mayar da hankali wajen wayar da kan jama’a da kuma kula da masu son daina shaye-shaye ta hanyar cibiyoyin gyaran hali.
Rahotanni daga Majalisar ɗinkin Duniya ta hanyar UNODC sun yaba da irin ci gaban da Nujeriya ke samu wajen yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi, musamman yadda NDLEA ta ƙara tsaurara matakan hana Nijeriya zama mafakar ƙungiyoyin safarar ƙwayoyi na duniya. Wannan abin a yaba ne, domin ba aikin hukuma kaɗai ba ne, aiki ne na kare rayuwar miliyoyin matasa.
Haka kuma, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ci gaba da nuna goyon baya ga NDLEA ta hanyar ƙarfafa ayyukan hukumar, samar da kayan aiki, horar da jami’ai da kuma tallafa wa shirye-shiryen wayar da kan al’umma. Wannan ya nuna cewa gwamnati ta fahimci cewa ba za a samu cikakken ci gaba ba idan aka bar matasa suna nutsewa cikin shaye-shaye.
Sai dai, duk da irin wannan ƙoƙari, gaskiya ita ce gwamnati ita kaɗai ba za ta iya cin wannan yaƙi ba. Iyaye suna da rawar da za su taka. Sau da yawa ana barin yara suna yawo ba tare da kulawa ba, suna shiga mummunar ƙawance wanda daga ƙarshe ke kai su ga shaye-shaye. Wasu iyaye kuma ba su san irin mutanen da ‘ya’yansu ke hulɗa da su ba, har sai lokacin da abin ya lalace.
Malaman makarantu ma suna da muhimmiyar rawa. Ya kamata a ƙara koyar da ɗalibai illolin shan miyagun ƙwayoyi tun suna ƙanana, domin rigakafi ya fi magani. Haka kuma shugabannin addinai su ci gaba da amfani da mimbari wajen wayar da kan jama’a, domin addini ya haramta duk wani abu da ke gusar da hankali da lalata rayuwa.
Har ila yau, shugabannin al’umma, sarakuna, masu unguwanni da ƙungiyoyin matasa su haɗa kai da hukumomin tsaro wajen gano masu safarar ƙwayoyi da masu yaɗa su a cikin al’umma. Duk wanda ya san dillalin ƙwayoyi ya yi shiru, tamkar yana taimaka masa ne wajen lalata rayuwar matasan da ke kewaye da shi.
Duk da haka, akwai buƙatar gwamnati ta ƙara faɗaɗa yaƙin da take yi da shaye-shaye ta hanyar mayar da hankali ba kawai kan kama masu safara da dillalan miyagun ƙwayoyi ba, har ma da magance tushen matsalar. Rashin aikin yi, talauci, ƙarancin ilimi da rashin kyakkyawan kulawar iyaye na daga cikin abubuwan da ke jefa matasa cikin wannan hali. Matashin da ke da sana’a, ilimi da fata a rayuwa ba ya cika karkata zuwa shaye-shaye kamar wanda ya rasa makomar rayuwarsa.
Don haka, akwai buƙatar a ci gaba da bunƙasa shirye-shiryen koyon sana’o’i, tallafa wa ƙananan sana’o’i, samar da guraben aikin yi, da ƙarfafa wasanni da sauran ayyukan raya matasa. Idan aka cike lokacin matashi da abin yi mai amfani, za a rage damar da zai samu ta faɗawa tarkon miyagun ƙwayoyi.
Haka kuma, ya kamata a ƙara yawan cibiyoyin gyaran hali (rehabilitation centres) a sassan ƙasar nan. Gaskiya ne akwai matasa da yawa da suka shiga shaye-shaye, amma a yau suna nadamar abin da suka aikata kuma suna neman hanyar dawowa cikin al’umma. Bai kamata a riƙa kallon kowane mai shaye-shaye a matsayin ɓatacce ba. Wasu marasa lafiya ne da ke buƙatar taimako, kulawa da shawara daga ƙwararru domin su dawo rayuwa ta gari.
A wannan wuri, ya dace a yaba wa Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), ƙarƙashin jagorancin Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), bisa yadda ta ƙara ƙaimi wajen yaƙar dillalan miyagun ƙwayoyi da kuma shirye-shiryen wayar da kan al’umma. A ‘yan shekarun nan, an ga yadda hukumar ke kama manyan dillalan ƙwayoyi, tana lalata gonakin wiwi, tana ƙwace tarin miyagun ƙwayoyi a filayen jiragen sama, tashoshin ruwa da kan iyakokin ƙasa. Hakan ya nuna cewa yaƙin ba ya tsaya ga masu amfani da ƙwayoyi kaɗai, har da waɗanda suke cin gajiyar lalata rayuwar matasa.
Ina kuma kira ga ‘yan siyasa da su guji amfani da matasa masu shaye-shaye a matsayin kayan aikin tayar da rikici yayin zaɓe. Tarihi ya nuna cewa mafi yawan rikice-rikicen siyasa ana amfani da matasa ne waɗanda aka raunana tunaninsu ta hanyar miyagun ƙwayoyi. Wannan ɗabi’a ba ta da amfani ga dimokuraɗiyya, kuma tana lalata makomar waɗanda ake amfani da su.
Ga matasan Nijeriya kuwa, ina roƙonsu da kada su bari matsin rayuwa ko tasirin abokai ya ruɗe su. Shaye-shaye ba mafita ba ne ga matsaloli. Duk wata daɗi da ƙwayoyi ke bayarwa na ɗan lokaci ne, amma sakamakonsu na iya kasancewa na tsawon rayuwa. Akwai matasa da dama da suka rasa ilimi, aiki, aure, mutunci har ma da rayukansu saboda kuskuren fara gwada ƙwayoyi sau ɗaya kawai.
Ya kamata mu tuna cewa matashin da ya tsare lafiyarsa, ya nemi ilimi, ya koyi sana’a kuma ya kasance mai kyawawan ɗabi’u shi ne ginshiƙin ci gaban Nijeriya. Amma idan muka bar miyagun ƙwayoyi suna ci gaba da lalata wannan ginshiƙi, to muna lalata makomar ƙasar da hannunmu.
A ƙarshe, wannan yaƙi ba na gwamnati kaɗai ba ne, ba na NDLEA kaɗai ba ne, ba na iyaye ko malamai kaɗai ba ne. Yaƙi ne da ya rataya a wuyan kowane ɗan Nujeriya. Mu haɗa hannu wajen kare matasanmu daga wannan annoba, domin idan muka ceci matasa, mun ceci iyalai; idan muka ceci iyalai, mun ceci al’umma; idan muka ceci al’umma, mun tabbatar da kyakkyawar makomar Nijeriya.
Allah Ya kare matasanmu, Ya ba su basira da ƙarfin guje wa duk wani abin da zai lalata rayuwarsu. Ilahee Ya Rabbi.
Wasiƙa daga MAHDI MUSA MUHAMMAD.07066778190.
