An gudanar da taron zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a Augie

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

An gudanar da wani muhimmin taron zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a ƙaramar hukumar Augie da ke jihar Kebbi, domin ƙarfafa zaman lafiya da warware matsalolin da suka shafi rikice-rikicen noma da kiwo a yankin.

Taron ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da manoma suka gabatar, inda suka zargi wasu makiyaya da yin ɓarna ga amfanin gonakinsu da ke tudu da kuma fadamomi.

Da yake jawabi a wajen taron da aka gudanar a sakatariyar ƙaramar hukumar Augie, Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) reshen Augie, Alhaji Shehu Rugga, ya yi alƙawarin ci gaba da inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin manoma da makiyaya domin rage rikice-rikice da bunƙasa harkokin noma da kiwo.

Ya yi kira ga shugabannin Fulani da dattawa da su ci gaba da wayar da kan matasa masu kiwo kan muhimmancin bin dokokin ƙasa da kuma mutunta haƙƙoƙin jama’a kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

“Ba wanda ke son hasara, saboda haka bai dace a bar dabbobi suna shiga gonaki suna lalata amfanin manoma ba,” inji shi.

Alhaji Shehu Rugga ya kuma roƙi manoma da su guji ɗaukar doka a hannunsu ta hanyar cin zarafi ko dukan makiyaya, yana mai jaddada cewa hanya mafi dacewa ita ce kai ƙorafi ga hukumomin da suka dace domin a sasanta matsalar cikin lumana kamar yadda aka gada tun daga kaka da kakanni.

Ya ƙara da cewa mahalarta taron sun amince cewa tattaunawa da fahimtar juna su ne hanyoyin da suka fi dacewa wajen warware sabani da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.

A nasa jawabin, wakilin jami’an tsaro ya tabbatar wa al’umma cewa hukumomin tsaro za su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi tare da aiwatar da doka ba tare da nuna son kai ba. Ya kuma yi gargadin cewa duk wanda aka samu yana aikata laifi ko tayar da zaune tsaye zai fuskanci hukunci bisa doka.

Hakazalika, Sakataren ƙungiyar Miyetti Allah reshen Augie, Alhaji Ummaru Rugga, ya yi kira ga makiyaya da su ci gaba da rayuwa cikin lumana da manoma tare da guje wa duk wani abu da zai haddasa rikici domin tabbatar da ci gaban al’umma.

Shi ma da yake jawabi, Sarkin Sudan na Tiggi, Alhaji Musa Yusuf Alkali, ya buƙaci al’umma su mara wa wannan yunƙurin na zaman lafiya baya ta hanyar nuna haƙuri, fahimtar juna da mutunta juna.

Ya jaddada cewa zaman lafiya mai ɗorewa ba zai samu ba sai an ci gaba da haɗin kai da tattaunawa tsakanin dukkan ɓangarori.

Sarkin Sudan na Tiggi ya kuma yi kira ga makiyaya da su kasance masu adalci da kulawa wajen bai wa yara ƙanana alhakin kiwon manyan garken shanu, yana mai cewa hakan na iya haifar da matsaloli.

Haka kuma ya nuna damuwa kan yadda wasu matasan Fulani ke faɗawa cikin shaye-shaye, inda ya buƙaci iyaye su ƙara sa ido da kula da tarbiyyar ‘ya’yansu.

Taron ya samu halartar sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma, jami’an tsaro, wakilan matasa da kuma jami’an gwamnati.

By ukarofi

Leave a Reply