Kotu ta bada belin Nnaji akan miliyan N20 da ƙwace fasfonsa bayan musanta zarge-zargen da ake masa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta bayar da belin tsohon Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji akan Naira miliyan 20 bayan ya musanta tuhume-tuhume guda shida da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta shigar akansa kan zargin amfani da takardar shaidar karatu ta bogi da kuma sauya akalar kuɗaɗen al’umma.

A yayin Shari’ar, Alƙali Joyce Abdulmalik ta umarci Nnaji da ya gabatar da mai tsaya masa guda ɗaya wanda wajibi me ya zama ma’aikacin Gwamnatin Tarayya mai matsayi daga mataki na 15 zuwa sama, tare da wasu sharuɗɗan kotu.

Baya ga haka ne aka ɗage shari’ar zuwa ranar 21 ga Satumba, 2026 domin sake zama akan al’amarin.

ICPC ta ce an kama Nnaji ne bayan ya ƙi amsa gayyatar hukumar, yayin da ake zarginsa da gabatar da takardun karatu na bogi a lokacin da ake tantance shi domin naɗa shi minista a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

By Babaji

Leave a Reply