Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Allah ya yi wa Hakimin Sabuwa kuma Kogon Katsina Injiniya Bello Ibrahim Kogo rasuwa.
Wata majiyar ta nuna cewa marigayi Bello Kogo ya rasu a wata asibiti da ke Kano bayan ya yi fama da rashi lafiya.
Babu wani ƙarin bayani sai ana sa ran gobe Talata za ayi jana’izar hakimin a gidan sa da ke garin Sabuwa a ƙaramar hukumar Sabuwa.
