Kotu ta bada belin Dr Bishir Kurfi don sauraron shari’a 13 ga Yuli

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kotun majistare a Katsina ta bada belin Dr Bishir Kurfi zuwa 13 ga watan Yuli ranar da za ta cigaba da sauraran ƙarar da gwamnatin Jihar Katsina ta shigar tana zargin sa da ƙarya da ɓata su.

A wata hira da gidan talabijin na Trust TV Dr Kurfi ya yi zargin cewa gwamnatin Jihar Katsina ta ɗauki nauyin ‘yan bindiga zuwa aikin hajji wanda gwamnatin ta ƙaryata ta kuma buƙaci Dr Kurfi ya janye ƙazafin da ya yi.

Lauyan wanda ake ƙara Barista AD umar ya bayyana wa manema labarai bayan da aka fito daga kotu cewa,kotu ta bada belin wanda ake zargin zuwa 13 ga watan Yuli ranar da za a dawo a cigaba da shari’ar.

Ya ce kotun ta gindaya sharuɗan bada beli da suka haɗa da kawo mutane biyu masu kadara na fili a Katsina.

Barista AD umar ya kuma nuna gamsuwa da zaman kotun tare da sanar da cewa za su zauna da wanda ake ƙara su duba tuhuma da kuma bayanai da ake cewa yayi sannan su san abin yi.

By ukarofi