
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babban Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa labarai da Hulɗa da Jama’a, Temitope Ajayi, ya bayyana iƙirarin tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai shekara 90 a duniya a matsayin “harin ƙarshe na doki mai shure-shuren mutuwa”.
Ajayi ya bayyana haka ne yayin mayar da martani ga kalaman ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar ADC da ya yi su a wata hira da BBC, inda ya yi zargin cewa Shugaba Tinubu “ɗan shekara 90” ne. Mashawarcin shugaban ƙasar ya bayyana hakan a matsayin zumuɗin son zama shugaban ƙasa ga Atiku. A yayin hirar, Atiku ya ce yana hujjar da zai gabatar a kotu wadda ke goyon bayan iƙirarin nasa.
Saidai, a wata hira a yammacin ranar Asabar, Ajayi ya ce Atiku ya faɗi haka ne bisa zumuɗinsa na son zama shugaban Nijeriya a madadin mayar da hankali akan ababen da suka dami ‘yan Nijeriya, ya koma yin tsokaci akan rayuwar Tinubu ta kai-da-kai.
Ya kuma zargi Atiku da amfani da sukar Tinubu a karan kansa da nufin janyo hankalin jama’a kan yaƙin neman zaɓensa bayan gaza gamsar da ‘yan Nijeriya kan matsayarsa game da tallafin fetur.
A cewarsa, Atiku ya rikice kan bayyana matsalolin tsare-tsare yayin da ya bayar da mabambantan bayanai kan dawo da tallafin fetur, yana mai cewa hanya guda da ta rage masa ita ce cin fuskar shugaban ƙasar.
