Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Jihar Taraba, tare da haɗin gwiwar Shirin Tallafa wa Haɓaka Samar da Dabbobi (L-PRES), ta ƙaddamar da wani shirin haɗa maniyyin ingantattun bijimai ga shanu a faɗin jihar, da nufin inganta nau’in shanu da ƙara yawan samar da madara da nama.
An aaddamar da shirin ne a ranar Asabar a Jalingo, babban birnin jihar, inda ake sa ran zai taimaka wajen ƙara yawan amfanin garken shanu da kuma bunƙasa darajar kiwon dabbobi a fannin tattalin arzikin jihar.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da shirin, Manajan Daraktan Kamfanin Liɓestock Genetics Africa Ltd, Emmanuel Nnoku, ya ce amfani da fasahar zamani wajen hayayyafa dabbobi zai taimaka matuƙa wajen sauya tsarin kiwon dabbobi da inganta samar da nama da madara.
Nnoku, wanda kamfaninsa ke aiwatar da shirin a Taraba, ya ce an tura ƙwararrun ma’aikatan fasaha zuwa sassa daban-daban na jihar domin gudanar da aikin. Ya ƙara da cewa ana aiwatar da makamantan shirye-shirye a wasu jihohi, inda ya buƙaci manoma da sauran masu ruwa da tsaki su ba ƙungiyar ƙwararrun da ke gudanar da aikin cikakken haɗin kai domin tabbatar da nasarar shirin.
A cewarsa, an tsara shirin ne domin inganta ƙwayoyin halittar shanu, musamman ta fuskar ƙara yawan madara da nama, haɓaka ingancin garke da kuma bunƙasa ribar da masu kiwon dabbobi ke samu.
Shi ma Jami’in Gudanar da Ayyukan L-PRES a Jihar Taraba, Hananiah Albert, ya ce tsarin haɗa maniyyin shanu zai bai wa manoma damar samun kwayoyin halittar bijimai masu inganci ba tare da ɗaukar nauyin kuɗi da wahalar kiwon bijimai na musamman domin hayayyafa ba. Ya ce za a aiwatar da shirin a cibiyoyin kiwon dabbobi da sauran wuraren da aka ware a faɗin jihar, tare da tallafin ma’aikatan kula da lafiyar dabbobi da ƙwararrun masu kula da kiwo.
Albert ya buƙaci masu kiwon shanu su samar da dabbobinsu domin a yi musu aikin, tare da bin shawarwarin ƙwararru yadda ya kamata. Ya bayyana cewa amfani da maniyyin ingantattun bijimai zai taimaka a hankali wajen inganta wasu muhimman siffofin shanu, ciki har da yawan madara, saurin girma, haihuwa, jure cututtuka, iya dacewa da yanayi da kuma ƙara ingancin garken gaba ɗaya.
Shugaban Hukumar Bunƙasa Kiwo ta Jihar Taraba (TALDEC), Dakta Dauda Abubakar, ya bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki na sauya kiwon dabbobi daga tsohuwar hanya zuwa tsarin zamani.
Abubakar ya yaba wa Sashen Aiwatar da Ayyukan L-PRES da abokan hulɗarsa na fasaha bisa ƙaddamar da shirin, inda ya buƙaci masu kiwon dabbobi su rungumi wannan dama domin ƙara yawan amfanin garkensu. Ya kuma jaddada cewa TALDEC za ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen da ke inganta kiwon dabbobi da kuma ƙarfafa tattalin arzikin al’ummomin da suka dogara da kiwo a jihar.
A nasa ɓangaren, Alhaji Arma Yau, wani manomin kiwo kuma tsohon mataimakin gwamnan Jihar Taraba, ya yaba wa gwamnatin jihar da L-PRES bisa ƙaddamar da shirin haɗa nau’o’in shanu. Yau ya ce shirin zai taimaka sosai wajen inganta nau’in shanu tare da ƙara yawan amfanin da manoman kiwo ke samu a Jihar Taraba.
