Tsadar haya da lamunin gida na ƙara jefa mazauna Legas cikin matsin rayuwa – Rahoto

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Matsalar samun gidaje masu sauƙin biya a Legas na ƙara ta’azzara, sakamakon aarancin kuɗin shiga, tsadar ribar lamunin gidaje, hauhawar farashin filaye da kuɗin gina gidaje, ƙarancin ababen more rayuwa da kuma matsalolin tsarin mallakar fili.

Wani sabon rahoto mai shafuka 86 mai taken “Bayan Hayar Gida: Nazarin Faɗaɗa Jari Ta Hanyar Gidaje a Legas” ne ya bayyana hakan.

An ƙaddamar da rahoton ne a wani taron haɗaka mai taken “Bayan Hayar Gida: Taron Gidaje da Jari na Legas”, wanda GTI Inɓestment Group ta shirya a Legas.

Taken taron shi ne “Gidaje, Jari da Makomar Legas”, inda masu ruwa da tsaki suka tattauna dangantakar da ke tsakanin gidaje, harkar kuɗi da kuma ci gaban tattalin arzikin jihar na dogon lokaci.

Shugaban Sashen Bincike da Dabarun Ci gaba na GTI Inɓestment Group, Abiodun Ogunniyi, ne ya gabatar da taƙaitaccen bayanin rahoton. Rahoton ya ce, ba za a iya magance matsalar gidaje masu tsadar gaske ta hanyar rage farashin siminti kawai ba, domin kayan gini wani ɓangare ne kawai na manyan abubuwan da ke haddasa tsadar gidaje.

Binciken ya nuna cewa ko da an samu ragin kashi 82 cikin 100 na farashin siminti, hakan zai iya rage farashin gidaje da kusan kashi 14 zuwa 15 cikin 100 ne kawai. Rahoton ya gano cewa ƙarancin kuɗin shiga na iyalai, tsadar ribar lamunin gidaje, ƙarancin samun lamunin jinginar gida, rashin wadatattun ababen more rayuwa, matsalolin mallakar ƙasa da kuma tsadar gine-gine baki ɗaya su ne manyan abubuwan da ke hana mutane mallakar gida.

Rahoton ya ce amfani da lamunin jinginar gida a Nijeriya har yanzu yana da ƙarancin gaske, inda kusan kashi 0.6 cikin 100 na iyalai ne kawai ke dogaro da irin wannan tsarin wajen samun gidaje. Haka kuma, rahoton ya nuna cewa farashin haya a Legas na ƙaruwa fiye da hauhawar farashin kayayyaki. A wasu yankunan babban birnin jihar, haya ta ƙaru da sama da kashi 40 cikin 100 a shekara, yayin da a wasu fitattun yankunan tsibirin Legas ta kai kusan kashi 51 cikin 100.

Rahoton ya kwatanta hakan da hauhawar farashin kayayyaki na ƙasa baki ɗaya, wanda ya kai kashi 15.9 cikin 100 a watan Yuni. Matsalar, a cewar binciken, ta fi tsanani ga masu ƙarami da matsakaicin kuɗin shiga.

Kashi 80 cikin 100 na waɗanda aka tambaya sun bayyana Legas a matsayin wurin da samun gida ya yi matuƙar tsada, abin da ke nuna girman nauyin gidaje da mazauna birnin ke fuskanta.

Rahoton ya ƙara da cewa ko iyalan da ke samun kusan Naira 500,000 a wata na iya kashe tsakanin kashi 40 zuwa 60 cikin 100 na kuɗin shigarsu wajen biyan haya a wasu sassan yankunan babban birnin.

Masu binciken sun yi gargaɗin cewa ƙaura zuwa ƙauyukan da ke bayan birnin domin neman haya mai rahusa ba lallai ne ta kawo sauƙin kuɗi ba, saboda tsadar sufuri na iya cinye mafi yawan kuɗin da aka samu daga rage kuɗin haya.

Ta amfani da Marina a matsayin wurin misali, masu binciken sun nazarci tallace-tallacen gidaje 3,200 a kasuwannin gidaje guda 15. Sun gano cewa kuɗin zirga-zirga daga wuraren da ke nesa da birni zuwa wuraren aiki na iya cinye wani babban kaso na kucin da mutum ya tanada sakamakon yin haya mai rahusa.

Baya ga sufuri, rahoton ya ce ababen more rayuwa na ƙara zama muhimmin abin da ke ƙayyade darajar gidaje da kuma buƙatarsu a kasuwa. Binciken ya nuna cewa gidajen da ke tsakanin nisan kilomita ɗaya zuwa biyu daga tashoshin jirgin ƙasa na iya samun ƙarin daraja mai yawa, lamarin da ke nuna yadda ingantaccen sufuri ke ƙara tasiri kan darajar gidaje.

By ukarofi

Leave a Reply