Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Cibiyar Bunƙasa Kamfanoni Masu Zaman Kansu (CPPE) ta yi gargaɗin cewa matsalolin samar da wutar lantarki, tsadar harkokin sufuri da jigilar kaya, rashin tsaro da kuma yawan kuɗin ruwa na iya kawo cikas ga mataki na gaba na bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya.
Cibiyar ta buƙaci gwamnatin tarayya ta sauya salon da take bi wajen aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki, inda ta mayar da hankali daga daidaita manyan ma’aunan tattalin arziki zuwa bunƙasa samar da kayayyaki da ayyukan yi.
CPPE ta bayyana cewa, duk da cewa sauye-sauyen baya-bayan nan sun taimaka wajen inganta daidaiton tattalin arziki, kasuwar canjin kuɗaɗen waje, kuɗaɗen shiga na gwamnati da kuma amincewar masu zuba jari, har yanzu manyan sassan da ke samar da arziki na fuskantar matsin lamba sakamakon tsadar gudanar da kasuwanci da matsalolin da suka daɗe suna addabar tattalin arzikin.
Cibiyar ta bayyana hakan ne a yayin da take tsokaci kan takardar tantance nasarar sauye-sauyen tattalin arziki mai maki 11 da Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Haɗaɗɗen Tattalin Arziki, Farfesa Taiwo Oyedele, ya gabatar a Abuja ranar 19 ga Agusta, 2026.
Takardar ta yi nazari kan yadda sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu suka kasance tsakanin watan Mayun 2023 zuwa Disambar 2025, musamman kan kuɗaɗen shiga na gwamnati, hauhawar farashi, tsadar rayuwa da sauran manyan ma’aunan tattalin arziki.
A cikin wata sanarwa, Darakta-Janar na CPPE, Dakta Muda Yusuf, ya yaba wa ministan bisa gabatar da rahoton, yana mai cewa hakan na da muhimmanci wajen tabbatar da gaskiya da kuma ƙara amincewa da tsarin sauye-sauyen.
Yusuf ya ce kuɗaɗen shiga na gwamnati sun inganta, kasuwar canjin kuɗaɗen waje ta samu daidaito, ajiyar kuɗaɗen waje ta ƙaru, yayin da amincewar masu zuba jari ita ma ta farfaɗo.
Ya kuma bayyana cewa haƙiƙanin bunƙasar GDP, wato Jimillar Abubuwan da Tattalin Arziki ke Samarwa, ta kai kashi 3.89 cikin 100 a zangon farko na shekarar 2026, idan aka kwatanta da kashi 3.13 cikin 100 a makamancin zangon shekarar 2025.
Sai dai Darakta-Janar na CPPE ya yi gargaɗin cewa wannan ci gaba da aka samu a manyan ma’aunan tattalin arziki bai riga ya sauya zuwa sauƙi mai ma’ana ga kamfanoni da sauran masu gudanar da harkokin samar da arziki ba.
Ya ce, duk da ci gaban da aka samu, ɓangaren samar da kayayyaki da ayyuka na tattalin arzikin ƙasar na ci gaba da fuskantar matsin lamba.
A cewarsa, ɓangaren wutar lantarki ya samu koma baya da kashi 15.3 cikin 100 a zangon farko na 2026, yayin da masana’antu suka samu ƙaruwa da kashi 3.29 cikin 100, sannan aikin noma ya ƙaru da kashi 3.15 cikin 100.
Yusuf ya lissafa wutar lantarki, sufuri da jigilar kaya, rashin tsaro, ƙarancin aikin noma, rashin isassun ababen more rayuwa, kuɗaɗen bin ƙa’idoji da kuma tsadar jari a matsayin manyan matsalolin da ke hana tattalin arzikin ƙasar yin cikakken tasiri.
Ya ce: “Manyan matsalolin Nijeriya a yanzu suna ƙara zama matsaloli na tsarin tattalin arziki, musamman wutar lantarki, sufuri, rashin tsaro, aikin noma, ababen more rayuwa, kuɗaɗen bin ƙa’idoji da kuma tsadar jari.”
Ya jaddada cewa magance waɗannan matsaloli na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da ɗorewar bunƙasar tattalin arziki, saboda tsadar gudanar da kasuwanci na ci gaba da rage wa kamfanonin Nijeriya damar yin gogayya da takwarorinsu.
