Ɓarkewar cutar mashaƙo: An rasa gado a sashen yara na Asibitin Koyarwa a Katsina

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Yayin da cutar mashaƙo take cigaba da yaɗuwa a Jihar Katsina, an samu cinkoson marasa lafiya a Asibitin Koyarwa da ke Katsina (FTH Katsina) yayin da aka rasa gado a sashen kuka da ƙananan yara.

Hukumar gudanarwar asibitin ce ta sanar da haka ga wakilinmu labarai a ranar Asabar, inda ta ce ana samu adadi mai yawa na irin masu cutar da ake turo su daga wasu asibitoci, wanda hakan ya sa suka kere adadin gadaje asibitin.

A cewarta, cigaba da yaɗuwar cutar da samun ƙarin marasa lafiya sun yi sanadiyyar cikar jama’a a sashen ƙananan yaran yayin da ake ƙara tabbatar da kamuwa da cutar mashaƙo.

Ta bayyana cewa, duk da wannan hali, asibitin na iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya bayar da kulawa ga kowane mara lafiya da aka kai masa daga cikin yaran ta hanyar ƙara matakan shirye-shiryen don amsa buƙatun cigaba da yawaitar masu ɗauke da cutar.

Kazalika, hukumar ta jinjina wa ma’aikatan lafiya bisa sadaukarwa da jajircewarsu musamman bisa la’akari da yadda suke ƙoƙarin bai wa mara lafiyan da cutar ta yi tsanani a jikinsu magani, tana mai kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su ƙara ƙaimi wajen shirye-shirye don sauke nauyin da ya rataya a kansu.

By Babaji

Leave a Reply