Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
ƙungiyar Kare Haƙƙin Tattalin Arziki da Walwala da Yaƙi da Rashawa (SERAP) ta buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana ko ta yi amfani da ikon da doka ta ba ta wajen sanya iyakar kuɗin da mutum zai iya bayarwa ga jam’iyyar siyasa ko ɗan takara a zaɓen 2027.
ƙungiyar ta kuma nemi Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana wa ’yan Nijeriya iyakar kuɗin tallafin siyasa da hukumar ta amince da su, tare da tabbatar da cewa an sanar da jam’iyyun siyasa, ’yan takara, masu bayar da tallafi da sauran jama’a yadda ya kamata.
SERAP ta yi wannan buƙata ne cikin wata wasiƙar neman bayanai ƙarƙashin Dokar ’Yancin Samun Bayanai (Freedom of Information) mai kwanan wata 22 ga Agusta, 2026, wadda Mataimakin Daraktan ƙungiyar, Kolawole Oluwadare, ya sanya wa hannu.
ƙungiyar ta kuma nemi INEC ta bayyana tsarin, ma’aikata da hanyoyin da ta tanada domin sa ido, bincike da ɗaukar mataki kan duk wani take iyakar kuɗin tallafin siyasa da kuma kuɗin yaƙin neman zaɓe a yayin shirye-shiryen babban zaɓen 2027.
SERAP ta ce ya kamata INEC ta bayyana yadda take sa ido kan harkokin kuɗin siyasa, ciki har da hanyoyin gano kuɗin da ake bayarwa tsabar kuɗi, kadarori ko wasu kayayyaki, kuɗin tallan dijital da kafofin sada zumunta, kuɗin da wasu ɓangarori ke kashewa a madadin ’yan takara, da kuma tallafin da ake bayarwa ta hannun wasu mutane domin kauce wa iyakar da doka ta tanada.
A cewar ƙungiyar, ƙarin bayyana gaskiya kan yadda ake tafiyar da kuɗin siyasa na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da cewa zaɓen 2027 ya gudana cikin adalci da daidaiton dama, domin ’yan Nijeriya su iya yanke shawarar siyasa cikin ’yanci da cikakken sani.
SERAP ta ce aikin INEC bai tsaya kawai ga karɓar bayanan kuɗin jam’iyyun siyasa ba. A cewarta, Kundin Tsarin Mulki ya wajabta wa hukumar binciken harkokin kuɗin jam’iyyun, gudanar da binciken da ya dace da kuma miƙa rahotonta ga Majalisar Dokokin Tarayya.
Ta ce wallafa irin waɗannan rahotanni zai bai wa ’yan Nijeriya damar tantance ko INEC na sauke nauyin da Kundin Tsarin Mulki da dokokin zaɓe suka ɗora mata.
ƙungiyar ta ce masu zaɓe, ’yan jarida da ƙungiyoyin fararen hula ba za su iya sa ido yadda ya kamata kan harkokin kucin siyasa ba idan ba a bayyana iyakokin tallafin da aka tanada ba, ko kuma babu wani tsari bayyananne da jama’a za su iya amfani da shi wajen bibiyar yadda ake bin dokokin.
SERAP ta bayyana damuwa kan yadda kuɗi ke ƙara mamaye siyasar Nijeriya, tana mai cewa hakan, tare da yiwuwar amfani da hukumomin gwamnati ba bisa ƙa’ida ba, na iya zama babbar barazana ga tsarin dimokuraɗiyya da gasa tsakanin jam’iyyun siyasa.
A cewar ƙungiyar, bayanan da ta nema za su taimaka wa ’yan Nijeriya wajen gano yawan kuɗin da aka kashe fiye da kima, kuɗin da ba a bayyana asalinsa ba ko kuma kuɗaɗen siyasa da ake zargin ba su da tushe na doka tun kafin su gurɓata tsarin zaɓe, maimakon a jira sai an kammala zaɓe.
SERAP ta ce dokokin da ke kula da harkokin kuɗin siyasa na da muhimmiyar rawa wajen kare dimokuraɗiyya, daidaiton damar siyasa, ’yancin faɗar albarkacin baki da haɗuwa, amincin zaɓe da kuma damar jama’a ta shiga harkokin mulkin ƙasa.
Sai dai ƙungiyar ta ce Nijeriya na fama da matsalar da jam’iyyun siyasa ke kasa bayyana cikakkun bayanan kuɗin da suke samu a matsayin tallafin yaƙin neman zaɓe.
Ta ce rashin bayyana waɗannan bayanai ya zama matsala mai ɗorewa, yayin da rashin tsauraran matakan hukunta masu karya doka ya rage wa INEC ƙarfi wajen tabbatar da bin ƙa’idojin.
SERAP ta ƙara da cewa Nijeriya ta daɗe tana fuskantar ƙalubale wajen kula da harkokin kuɗin siyasa, musamman game da yawan kuɗin da ake kashewa a yaƙin neman zaɓe, ɓoye tushen kuɗaɗen siyasa, ƙarancin bayyana bayanan kuɗi da kuma raunin aiwatar da dokokin da suka shafi kashe kuɗi da karɓar tallafi.
SERAP ta yi nuni da Sashe na 91(1) na Dokar Zaɓe ta 2026, wanda ya bai wa INEC ikon sanya iyaka kan adadin kuɗi ko kadarorin da mutum zai iya bai wa jam’iyyar siyasa ko ɗan takara.
ƙungiyar ta ce, wannan sashe ya kuma bai wa hukumar damar neman bayanai kan adadin kuɗin da aka bayar da kuma tushen kuɗin.
A cewar SERAP, Sashe na 91(2) ya tanadi hukunci ga mutum, ɗan takara ko jam’iyyar siyasa da ta wuce iyakar da INEC ta sanya.
Saboda haka, ƙungiyar ta ce ikon da doka ta bai wa INEC na sanya iyakar tallafin siyasa wata muhimmiyar kariya ce daga yadda masu hannu da shuni za su yi amfani da kuɗaɗensu wajen mamaye jam’iyyun siyasa ko ’yan takara.
Ta ce idan INEC ta yi amfani da wannan ikon, ’yan Nijeriya na da haƙƙin sanin iyakar kuɗin da aka amince a bayar da kuma yadda hukumar ke shirin tabbatar da bin wannan iyaka.
SERAP ta nemi INEC ta fayyace ko ta riga ta sanya iyakar. Idan ta yi hakan, ta ce ya kamata hukumar ta wallafa iyakokin nan take a wurin da jama’a za su iya ganinsu cikin sauƙi, musamman a shafin intanet na hukumar.
Ta kuma nemi INEC ta bayyana ƙa’idojin da ta bi wajen tantance wannan iyaka, ciki har da matakan da aka ɗauka domin hana tasirin kuɗi fiye da kima, tabbatar da daidaiton gasa da yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran hanyoyin samun kuɗin siyasa ba bisa ƙa’ida ba.
