Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata ƙungiya mai rajin kare muhalli, Women Initiatiɓe for Sustainable Enɓironment (WISE), tare da haɗin gwiwar Energy and Enɓironmental Law Club na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, ta horas da mata da matasa kan damar kasuwanci a fannin girke-girke mai amfani da makamashi mai tsafta.
Shugabar kuma Daraktar WISE, Olanike Olugboji Daramola, ce ta bayyana hakan a yayin bikin EcoCare Campus Initiatiɓe 2026, wani shirin tsaftace muhalli da aka gudanar a harabar Kongo ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
An gudanar da bikin ne domin karrama Comrade Jerry Adams, tsohon Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS).
Daramola ta jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a game da sauyin yanayi, tana kira ga ɗaiɗaikun mutane da al’ummomi da su rungumi hanyoyin rayuwa masu kare muhalli.
Ta ce WISE na ƙoƙarin bunƙasa tunanin kare muhalli da kyawawan ɗabi’un da suka dace da shi, ta hanyar bai wa mata da matasa damar zama masu kula da muhalli, masu taka rawa wajen yaƙi da sauyin yanayi da kuma masu samar da zaman lafiya.
A cewarta, ƙungiyar na kuma jagorantar shirye-shiryen bunƙasa hanyoyin girki da samar da haske masu tsafta da kare muhalli, tare da sauya rayuwar al’ummomi ta hanyar amfani da dabarun da ba sa gurɓata muhalli da kuma samar da ingantattun hanyoyin makamashi masu sabuntawa.
Daraktar ta ƙara bayyana cewa ana bai wa mata muhimmiyar rawa wajen jagorantar sabbin dabarun sake sarrafa shara da kuma amfani da kayan da aka zubar wajen ƙirƙirar wasu kayayyaki masu amfani. Ta ce hakan na taimakawa wajen gina al’ummomi masu tsafta da kuma rage illa ga muhalli.
Ta ce WISE na amfani da tsari mai haɗaka wajen kare muhalli, inda shirye-shiryenta suka shafi tsaftar muhalli, sarrafa shara daga gidaje da kasuwanni, da kuma bunƙasa yawon buɗe ido mai ɗorewa.
Daramola ta ce an shirya gangamin tsaftace muhalli na EcoCare Campus Initiatiɓe 2026 a matsayin wata hanya ta musamman ta girmama Jerry Adams, inda mahalarta suka shiga aikin tsaftace harabar jami’a da sauran sassan al’umma, tare da gudanar da shirye-shiryen wayar da kai kan muhalli da ayyukan sa-kai.
Ta yi kira da a ƙara haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki, musamman mata, matasa, manyan makarantun ilimi da ƙungiyoyin kare muhalli, domin tinkarar matsalar sauyin yanayi da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa.
