Daga AISHA ASAS
A lokacin da ake magana kan jaruman da suka taimaka wajen gina masana’antar fina-finan Najeriya, musamman ɓangaren fina-finan Yarbawa, sunan Alhaji Taiwo Babatunde Hassan, wanda aka fi sani da Ogogo, ba ya cikin waɗanda za a iya tsallakewa.
Ogogo ya shafe sama da shekaru arba’in yana haskawa a gaban kyamara, yana taka rawar da ta sa mutane suka saba ganinsa a matsayin mutum mai mutunci, dattijo mai natsuwa, jagora ko kuma mai tsayawa kan gaskiya. Amma kafin ya zama ɗaya daga cikin fitattun fuskokin Nollywood, rayuwarsa ta fara ne da sana’ar da ba ta da alaƙa da fim.
Shin wane ne Taiwo Hassan?
An haife shi a ranar 31 ga Oktoba, 1959, a Ilaro da ke Jihar Ogun. Ya fito daga zuriyar da tagwaye suka yawaita a cikinta, domin mahaifinsa da kakansa duk tagwaye ne. Sunan Taiwo da aka ba shi ma yana da alaƙa da wannan al’adar, kasancewar Taiwo shi ne ɗan fari a cikin tagwaye.
Abin da ya fi ɗaukar hankali a labarin rayuwarsa shi ne yadda ya bi wata hanya kafin daga bisani fasahar wasan kwaikwayo ta mayar da shi ɗaya daga cikin fitattun jaruman Najeriya.
Kafin shahara, Ogogo ya samu horon fasaha kuma ya yi aiki a matsayin makanikin mota a Hukumar Ruwa ta Jihar Legas. Ya shafe kusan shekaru 13 yana wannan aiki, kafin ya bar aikin a shekarar 1994 domin ya mayar da hankali gaba ɗaya kan wasan kwaikwayo.
A shekarar 1981 ya fara shiga harkar wasan kwaikwayo ƙarƙashin koyarwar fitaccen ɗan wasan kwaikwayo kuma masani kan wasan kwaikwayo, Chief Afeez Oyetoro, sannan ya shiga ƙungiyar wasan kwaikwayo ta Ademola Group.
Wannan shi ne farkon tafiyar wadda daga baya ta kai shi ga babbar shuhura da ta sa aka san shi kuma ya tara masoya a koina a faɗin ƙasar Najeriya har ma da ƙetare.
Me ya sa ake kiransa Ogogo?
Sunan da ya fi shahara da shi ba sunan haihuwarsa ba ne. Ogogo ya samo asali ne daga sunan yabo na gargajiya, wato Oriki, da ke da alaƙa da zuriyar danginsa. Daga baya ya mayar da sunan wani ɓangare na rayuwarsa ta sana’a, har ya kai ga mutane da dama sun fi saninsa da Ogogo fiye da Taiwo Hassan.
Tsayin wane lokaci ne ya ɗauka a duniyar fina-finai kafin ya yi fice?
Ko da yake Ogogo ya riga ya samu suna a wasan kwaikwayo na dandali da fina-finan Yarbawa, sai dai fim ɗin ‘Owo Blow’ na Tade Ogidan, wanda aka saki a shekarar 1996, ya taimaka matuƙa wajen ɗaga darajarsa zuwa matsayin babban jarumi.
Daga nan ne ya ƙara zama sanannen fuska a Nollywood, musamman wajen taka rawar da ke buƙatar mutum mai iko, dattako da natsuwa.
Ba wai kawai yadda yake furta magana ko motsinsa a gaban kyamara ne ya bambanta shi ba. A tsawon shekarun da ya yi yana aiki, Ogogo ya gina wani irin tambari da ya zama nasa kaɗai.
Sau da yawa ana ganinsa a matsayin mutum mai ƙa’ida, mai tsayawa kan gaskiya, ko kuma jagoran da ba ya gaggawar yanke hukunci.
Wannan irin rawar ce ta sa Ogogo ya kasance cikin jaruman da mutum kan gane su tun kafin a ambaci sunansu.
Wacce irin gudunmawa ce Ogogo ya bayar wurin gina masana’antar Nollywood?
Ogogo bai tsaya ga yin wasan kwaikwayo kawai ba. Ya kuma kasance cikin mutanen da suka taimaka wajen gina tsarin da masana’antar fina-finan Yarbawa ta dogara da shi.
Tare da abokinsa kuma fitaccen jarumi Yinka ƙuadri, ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa Odunfa Caucus, wata ƙungiya da ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da fina-finai da horar da masu tasowa a masana’antar.
Ta haka, gadonsa bai tsaya kan fina-finan da ya fito a cikinsu kaɗai ba. Ya kuma shafi mutanen da suka taso bayansa da kuma yadda aka ci gaba da yaɗa al’adun Yarbawa ta hanyar fim.
A shekarar 2022 ya fito a fim ɗin ‘Aníkúlápó’ na Kunle Afolayan, inda ya taka rawar Alaafin Ademuyiwa. Daga baya ya sake fitowa a jerin shirye-shiryen fim ɗin, Aníkúlápó: Rise of the Spectre, da aka fitar a shekarar 2024.
Wannan ya nuna cewa har zuwa shekarun ƙarshe na rayuwarsa, yana da abin da zai bayar ga masana’antar da ya shafe kusan rabin ƙarni yana cikinta.
Ta yaya ya sanya al’ada ta zama hanyar bi a masana’antar?
Ga Ogogo, fim ba kawai hanyar samun suna ko kuɗi ba ne. A matsayinsa na Musulmi mai kishin al’ada, ya kasance mai jaddada muhimmancin amfani da fina-finan cikin gida wajen kare harshen Yarbanci, al’adunsu da ɗabi’un da suke gina zamantakewa.
A wannan lokaci da fina-finan duniya ke ƙara tasiri kan abubuwan da ake kallo da kuma yadda ake kallon rayuwa, irin wannan matsayi ya sanya shi cikin jaruman da suka ɗauki fim a matsayin wata hanya ta adana abin da al’umma za ta iya rasawa idan ba a kula da shi ba.
Manyan mutane da masana’antar sun shiga makokin Ogogo
Rasuwar Ogogo ta haifar da alhini daga gwamnati, ƙungiyoyin masana’antar nishaɗi da kuma abokan aikinsa na tsawon shekaru.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga masana’antar ƙirƙira ta Najeriya, yana miƙa ta’aziyyarsa ga iyalansa, abokansa, abokan aikinsa da miliyoyin masu kallonsa.
Gwamnatocin Ogun da Lagos, jihohin da rayuwarsa da aikinsa suka yi tasiri a kansu, su ma sun shiga cikin waɗanda suka yi alhinin rasuwar jarumin. Gwamnatin Ogun ta bayyana shi a matsayin “fitaccen haske” wanda bai tsaya ga nishaɗantar da mutane ba, har ma ya taimaka wajen ɗaukaka al’adun Yarbawa da nuna su ga duniya.
A ɓangaren masana’antar, abokan aikinsa sun bayyana irin girman gibin da ya bari. Fitaccen jarumi Jide Kosoko ne ya sanar da rasuwarsa, yayin da Femi Adebayo Salami ya bayyana shi a matsayin ginshiƙin fina-finan Yarbawa wanda tasirinsa zai ci gaba da rayuwa a cikin tsararraki.
Shugaban TAMPAN, Bolaji Amusan, wanda aka fi sani da Mr Latin, ya bayyana Ogogo a matsayin babban jigo, fitaccen mutum kuma uba ga mutane da dama a masana’antar.
Haka kuma, yadda wasu daga cikin abokan sana’arsa suka karɓi labarin rasuwarsa ya nuna cewa abin da ya bari bai tsaya kan kyamara ba. Yinka ƙuadri, wanda ya yi tafiya mai tsawo tare da shi a masana’antar, ya nuna tsananin damuwarsa, yayin da mawakan Fuji irin su Wasiu Ayinde da Sule Alao Malaika su ma suka bayyana alhininsu.
Audio Visual Rights Society of Nigeria (AVRS), ƙungiyar da ke kare haƙƙin masu ayyukan sauti da hotuna, ita ma ta shiga cikin jerin waɗanda suka nuna alhinin rasuwar Ogogo, wanda ta kira ɗaya daga cikin membobinta.
A cikin saƙon ta’aziyyar da ta fitar, AVRS ta bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan masana’antar fina-finan Najeriya, tare da cewa ya kasance ƙwararren ɗan wasan kwaikwayo wanda gudunmawarsa wajen ci gaban masana’antar ta shafe shekaru da dama.
ƙungiyar ta ce ta hanyar basirarsa, jajircewarsa da rawar da ya taka a fina-finai, Ogogo ya nishaɗantar da tsararraki tare da taimakawa wajen gina tarihin fina-finan Najeriya.
AVRS ta kuma bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga iyalansa, abokan aikinsa da kuma al’ummar masu fasahar ƙirƙira baki ɗaya, musamman saboda irin gudumlnmawar da ya bayar wajen bunƙasa wannan fanni.
A madadin kwamitin gudanarwa da dukkan mambobinta, ƙungiyar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan Ogogo, abokansa, abokan aikinsa da ɗaukacin masana’antar fina-finan Najeriya, tare da addu’ar Allah Ya ba iyalansa ƙarfin jure wannan rashi, Ya kuma jiƙan marigayin.
Taiwo Hassan Ogogo ya rasu a ranar 23 ga Agusta, 2026, yana da shekaru 66, bayan fama da cutar kansa mai mataki na huɗu. Rasuwarsa ta zo ne jim kaɗan bayan iyalansa sun bayyana halin da yake ciki, lamarin da ya sa abokan aiki da masu fatan alheri suka shiga ƙoƙarin neman masa taimakon jinya.
Mutuwarsa ta rufe wani babi na rayuwar ɗaya daga cikin jaruman da suka shafe shekaru suna gina masana’antar fina-finan Najeriya. Saidai kamar yadda yake faruwa da masu fasahar da suka bar tarihi, rasuwa ba ta nufin gushewar abin da suka bari.
Ogogo ya fara ne a matsayin makanikin mota, ya shiga wasan kwaikwayo tun yana saurayi, ya shafe shekaru yana aiki a dandali da fina-finai, sannan ya zama ɗaya daga cikin fitattun jaruman da aka san su da mutunci da natsuwa a Nollywood. Ya kuma kasance cikin waɗanda suka taimaka wajen ba fina-finan Yarbawa wata murya da za a iya gane ta.
Saboda haka, idan aka sake buɗe tsofaffin fina-finan Nollywood a shekaru masu zuwa, za a ga wata fuska da ta daɗe tana kallon mai kallo cikin natsuwa, tana magana da ƙarfi ba tare da hayaniya ba.
Wannan fuskar ita ce ta Taiwo Hassan Ogogo, jarumin da ya bar kyamara, amma ya kasa ficewa daga tarihin Nollywood.
