Zan kawo wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20 a 2027 — Matawalle

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya ce yana da burin tara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ƙuri’u miliyan 20 a zaɓen Shugaban ƙasa na 2027.

Matawalle ya bayyana hakan ne ranar Talata a Abuja, yayin da dubban magoya bayansa da ’yan jam’iyyar APC suka tarbe shi bayan dawowarsa Nijeriya.

Ya ce zai fara tattara bayanai da neman ƙuri’u a faɗin jihohin Nijeriya 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja.

“Kamar yadda kuka sani, an fara kamfen, kuma burina shi ne in kawo wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ƙuri’u miliyan 20 a zaɓen shugaban ƙasa na 2027… Kuma a shirye nake in yi duk abin da zan iya domin tabbatar da mun cimma wannan buri,” in ji shi.

Matawalle ya ce akwai dalilai da dama da suka sa yake ganin ya kamata a sake zaɓar Tinubu a 2027, yana mai cewa shugaban ya yi ƙoƙari wajen inganta ayyukan yi ga matasa, tsaro da tattalin arzikin ƙasa a cikin shekaru ukun da ya yi yana mulki.

Rahotannin baya-bayan nan sun nuna cewa Matawalle na daga cikin jami’an da aka bai wa muƙami a kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na 2027.

By ukarofi