Matatar Ɗangote ta ƙara farashin fetur karo na uku cikin kwana takwas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kamfanin Matatar Ɗangote ya sake ɗaga farashin lita fetur inda ya yi ƙarin Naira 65, kwana uku da ƙarin baya.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙarin na yanzu ya ɗage farashin matatar daga N1,200 zuwa N1265 ga kowacce lita, wanda zai fara aiki daga yau Lahadi, 30 ga Agusta.

Wannan shi ne karo na uku da matatar take ƙara farashi cikin kwana takwas, wato hakan ya nuna cewa an samu karin N100, wanda ke wakiltar kaso 8.6. An bayyana wannan mataki ne a wata sanarwa da matatar ta fitar, wadda jaridar PUNCH ta samo a ranar Lahadi.

Haka kuma, ta ƙara farashin defo daga N1,582,380 zuwa N1,669,545 ga kowace ganga. Akan haka ne ta umarci dukkan kwastomominta da su mayar da dukkan izini domin karɓar sabon farashi kafin yin lodi. Ƙarin ya wakilci kaso 5.4 na farashin defon.

A ranar 21 ga Agusta ne ta ƙara daga N1,165 zuwa N1,185 kafin ta sake ƙara N15 a kai a ranar 26 ga watan.

By Babaji

Leave a Reply