Yawan waɗanda ake zargin sun kamu da kwalara ya haura 65,000 a 2026 – NCDC

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar kula da cututtuka masu yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) ta bayyana cewa adadin waɗanda ake zargin sun kamu da cutar kwalara a ƙasar ya haura 65,000 a bana. Darakta-Janar na NCDC, Jide Idris, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, inda ya ce an samu rahotannin cutar daga jihohi 35 da ƙananan hukumomi kusan 195. Ya ce duk da cewa adadin masu kamuwa da cutar a kowane mako yana raguwa sosai idan aka kwatanta da ƙololuwar da aka samu a farkon shekarar, har yanzu ba a kawo ƙarshen ɓarkewar cutar ba.

Idris ya ce ana ci gaba da fuskantar daminar ruwa, lokacin da haɗarin yaɗuwar kwalara ke ƙaruwa saboda ambaliyar ruwa na iya gurɓata hanyoyin samun ruwa tare da lalata tsarin tsaftar muhalli. Ya bayyana cewa ɗaya daga cikin muhimman darussan da aka koya daga ɓarkewar cutar shi ne muhimmancin samun magani cikin gaggawa. Ya ce a Jihar Borno, inda aka fi samun yawan masu kamuwa da kwalara a bana, sakamakon jinya ya fi kyau a wuraren da aka kusantar da cibiyoyin kula da marasa lafiya ga al’ummomin da abin ya shafa.

Sai dai darakta-janar ɗin ya jaddada cewa magani kaɗai ba zai kawo ƙarshen kwalara ba, saboda rashin tsaftataccen ruwan sha, yin bayan gida a fili, lalacewar hanyoyin rarraba ruwa, rashin ingantaccen tsarin tsafta da kuma matsalolin tsaftar muhalli a makarantu da kasuwanni na daga cikin abubuwan da ke ƙara yaɗuwar cutar. Ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi da su ƙara samar da ruwa mai tsafta, inganta sa ido kan ingancin ruwa, gyara muhimman kayayyakin samar da ruwa tare da ɗaukar matakan kawo ƙarshen yin bayan gida a fili.

A gefe guda kuma, NCDC ta bayyana cewa Najeriya ta samu sama da mutane 10,000 da aka tabbatar sun kamu da cutar mashaƙo a bana. Jide Idris ya ce duk da cewa cutar na ci gaba da zama babban ƙalubale, adadin waɗanda ke mutuwa daga cikin waɗanda aka tabbatar sun kamu ya ragu sosai idan aka kwatanta da makamancin lokaci na bara. Jihohin Kano, Borno da Bauchi na daga cikin jihohin da aka fi samun adadin masu ɗauke da cutar. Ya ce rashin yi wa yara allurar rigakafi ko rashin kammala allurar na daga cikin manyan matsalolin da ke haddasa yaɗuwar cutar, yayin da rashin yarda da allurar rigakafi, rashin tsaro, ƙauracewar al’umma da kuma matsalar isa ga yankunan da ke da wahalar shiga ke ƙara dagula lamarin.

NCDC ta ce tana haɗa kai da gwamnatocin jihohi da abokan hulɗa wajen daƙile kwalara da mashaƙo, ta hanyar ƙarfafa tsarin sa ido, ɗakunan gwaje-gwaje, tallafa wa ma’aikatan lafiya da tura tawagar gaggawa zuwa jihohin da abin ya shafa. A ɓangaren kwalara, matakan sun haɗa da allurar rigakafin kwalara ta baki, sanya sinadarin chlorine a ruwa, gyaran hanyoyin samun ruwa da wayar da kan jama’a kan tsafta. NCDC ta kuma shawarci jama’a da su garzaya asibiti idan sun fara fama da yawan gudawa mai ruwa, tare da fara amfani da ruwan ORS nan take, ba tare da jiran ciwon ya tsananta ba. Haka kuma, ta bukaci iyaye da masu kula da yara su tabbatar cewa yaran da ba su kammala allurar mashaƙo ba sun samu dukkan alluran da ake buƙata.

By ukarofi

Leave a Reply